← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Sashe 1

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒 GARWASHI🍒🍒
Page
1
Hadiza Bara'u gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Ubangiji Allah kayi musu Rahama kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH don girman shaffakin manzon Allah kasa ADDU AR da sukayi garemu karbabbiya ce

Har kullum Ina godewa masoyan Rubutun Gidan iko bani da Bakin godewa sai dai nace Ubangiji yafi Ni yabawa son so nake muku Yan uwa Allah ya hada mu a ALJANNAH🥰

Godiya ga Ubangiji da ya yarda har na sake dawowa da wata firar Mai take GARWASHI Allah yadda kake taimako na a ko yaushe ka ci gaba da taimako na har karshen numfashi nayi ta yin nasara a komai na Fara lafiya na Gama lafiya

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

........"Kaddara sunanta guda Daya ne Amma ma anarta da harsunan ta sunfi gaban a kidaya bare a iyakance. A yadda na fahimci kaddara da Kuma sunanta sai na kalli Duniya da abinda ke cikinta duk a matsayin kaddara. Idan nace kaddara to Ina nufin kaddara. Sai dai yadda Ni na fahimci kaddara akaran kaina ba Haka sauran mutane suke kallon kaddarar ba. Domin ko mun samu banbanci kwarai da gaske. A gareni kaddara itace komai ya samu bawa kaddara ne Dadi da wuya. Samu da Rashi Rayuwa da mutuwa ita kanta DUNIYA da abinda ke cikin ta kaddara ne . Zuwan bawa Duniya ma kaddara ne Amma sai na fahimci mutane Abu guda Daya Tak suke Kira sa kaddara shine wani Abu da ya samesu marar Dadi shine kawai kaddara ban sani ba Ni fahimtar da nayiwa kaddarar ko don ya kasance gaba Daya Rayuwa ta kaddarorin ne sukayi Mata zobe ne yasa na fahimceta Haka? Koko nawa zaton ne dai Haka ? Oho.

A wannan labarin ma da Zan baku ma babu komai a cikin sa sai tarin kaddarorin da suka faru akaina da iyayena da ma Yan uwana kwara biyu da muka Rayu a wannan kuntatacciyar Duniyar marar tagogin da zasu bamu iskan da zamu Shaka bare mugane Yan cin dake cikin Duniya Wanda har na kirawa kanmu GARWASHI domin ko gara zama a cikin GARWASHIN WUTA da irin kaddarar da kaddarar ta Miko Mana dolen mu kuma muka Mika hannu muka karba har ma muka bita da godiya duk da babu murmushi yayin godiyar sai ma tarin HAWAYE Mai radadi a garemu musamman ma Ni yarinya Fatima Zahra da duka duka shekaruna Sha biyar ne kacal Amma kaddara Bata tausayawa kuruciya ta ba kamar yadda bata tausayawa mahaifiyata ba Akan Rashin dangi da Yan uwa tayi aikin ta Akan mu😭

Ku shirya ku Kuma gyara Zama kuji yadda kaddara tayi sukuwa ta kumayi zamiya Akan mu Wanda karfin imani ne ya Hana mu hadiyar zuciya mu kauce daga cikin Duniya da Rayuwa...........

*** *** **** **** ****

GARWASHI

Karfe 12:09 am ta buga Mana muna tsakiyar filin jirgin marigayi malam Umar Musa yar Adua a garin katsina motar da mahaifiya ta ke ja kirar marcendy ce 3400 muka SHIGA filin jirgin Wanda yayi daidai da Jin Rigugin jirgin AZAMAN Yana Shirin sauka Alamar dai ba wani dogon jira zamuyi ba Daddyn zai iso nayi murmushi Mai sauti yayin da ammi ta tayani wurin fadin

"Munzo a daidai ga abin Sona Nan Zuwa
Ta fada itama tana Kara fadada murmushin ta Wanda yayi daidai da parking din motar da tayi a daidai parking space da sauri na balle murfin motar na fito ina daga kaina sama Ina kallon jirgin da Yake shawagin sauka kasa cikin wani salo Wanda ya dauki hankali na
Na daga tafin hannun na Ina Kare Ranar dake kashe min ido don na kalli jirgin da Wai buwar da yakeyi idan zai sauka da kyau har ma in bawa Yan uwana labarin da nagani

Ammi tana Raba Mana kallo Ni da jirgin da ya dauko abin sonta cikin murna da farin ciki har zuwa lokacin da jirgin ya Soma saukowa kasa Yana tsillawa aguje kamar ba sauka zaiyi ba kafin ya zuro tayoyin shi da nagan su ya mitsimitsi kafin ya diresu a kasa fankokin shi na wulwulawa inda kuma wata mota Mai dauke tsani wato kwarangar da matafiyan zasu tako zuwa kasa

Na finciki hannun Ammi Wai ta taho itama da sauri ta biyo Ni inda Kuma Naga kamar bata sauri don Haka na saki hannun ta na sheka aguje da nufin idan Daddyn ya fito in fada jikin shi na Rungume shi nayi mishi oyoyo shi Kuma ya sureni yayi sama Dani Yana cillawa sama. don gaskiya Ina son Daddy na fiye da ammi don shi Kam biye min Yake Kuma duk abinda nake so shima shi Yake so yayi wasa Dani yayi dariya in fada mishi damuwa ta yayi min magani akasin ammi da ta Fi bawa Yan uwa na maza kulawa musamman Yaya Abdullahi da kanena sulaiman muhimmanci fiye Dani Ni Kuma Daddy yafi bani muhimmanci abinda ban sani ba shine kaddarar farko kenan da Zan Soma dandan Akan harshena da idanuna da Kuma zuciya ta Akan Daddy na Mai bani kulawa

Muna tsaye muna jiran a bude kofar jirgin don inyi ido Hudu da Daddy na koma in fada jikin shi muji dumin ya da mahaifi da nafi kowa muradin hakan

Kofar jirgin ta bude inda na Fara ganin aminin Daddyn ya Fara fitowa fuskar shi Babu sassauci kafin wani mutum ya biyo bayan shi sai Kuma wasu fuskoki da ban San su ba ban taba ganin su ba suka fito suka dauke da wani Abu Mai kamar gadon tura marasa lafiya wani Abu Wanda aka nade cikin farin yanki kwance Akan gadon kamar gawa........

Gabana naji yayi wata irin sarawa har naji kaina na neman daukar ciwo na juyo Ina kallon Amma wadda ta taho aguje tana bude fuskar Wanda ke kwance Akan gadon Nan fuskar was Zan gani? Daddy na ne babu Alamar motsi ko numfashi a tare dashi

Kafin na tambayi aminin Daddyn wato Alh Mustafa abinda ke faruwa Akan Daddy na sai Jin kukan mahaifiyata ammi naji cikin wata murya da ban zaci Tata bace...........

Littafin GARWASHI na kudine ga me son Jin cikakken labarin zai biya dari uku ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Labarin GARWASHI daban yake da sauran labaran gidan iko kasance da shi don Jin yadda kaddara tayi Aikin ta Akan wadan Nan bayin Allah💃🏿

Kar ku Bari abar ku baya

Gidan iko shine sunanan ke cewa saduwar ALHERI🥰

🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
3//4

Hadiza Bara'u gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Godiya ga Ubangiji madaukakin sarki Mai iko Kan komai da kowa da yake aminta har komai ya zamo cikin falalar shi ta kasance kun fayakun Allah ka saka mu a cikin kun fayakun Dinka Duniya da lahira

Gaisshe da haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria tare da girmamawa

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

..........Kukan da Naga Ammi nayi ne ya fahimtar Dani wani Al amari Mai girma ya faru ko Kuma Yana Shirin faruwa Wanda ban shirya ji ko gani ba bare daukar shi a zuciya ta.

Har ga Allah ban kawo mutuwa Akan Daddy ba abinda kawai Rai na ya bani bashi da lafiya tuna hakan da nayi ma ya kara jefani a cikin Rudani da tashin hankali don ban bawa Daddy mutuwa a wannan lokacin ba sai yayi min Aure har Ya'ya na sai ya dauka Amma fa a yadda na tsara kenan ban San nayi daban da tsari na da tsarin Ubangiji ba. Wannan kaddarar itace ta zamo masomi ko nace mafari duk da Akwai wata dadaddiyar kaddarar da na baro muku ita a baya Akan Daddyn da ammi wadda itama zakuji sanadin kaddarar da ta hadasu Wanda haduwar ce kuma ta sake bada wata kalar kaddarar duk shi Ubangiji babu Ruwan shi idan zaiyi Abu ba don aso ko aki ba a mutu ko ayi Rayuwa shiyasa ma akace alkalamin kaddara zanen shi baya gogewa to hakan take Akan mu shiyasa muke ta biya kaddarar mu da Bakin mu muna kuka ko muna dariya......

Kukan da Ammi ke Rerawa cikin fita hayyaci da kalaman dake nuna mutum yaji dukan da mutuwa ke barwa Wanda tayiwa ta adi wato sambatun radadi na Soma jiyo abinda take fadawa Daddy......

"Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un yau Ni Ina Zan saka kaina faruk me yasa kayi min Haka? Ina Alkawarin da kayi min na zaka zamo min Uwa Kuma Uba?
Ga wa ka barni bayan kasan bani da kowa sai Allah sai Kuma Kai ba don na Rasa Ahali da dangi da Yan Uwa ba? Don Allah ka tashi Kar kace min ka tafi ka barni da yaran ka da Basu da gata sai Kai. Don Allah Umar ka tashi ka ci gaba da kasance wa farin ciki na kamar yadda kayi min alkawari kafi kowa sanin bani kowa sai Kai Yan uwan ka zasu samu damar keta Ni . Iyayena zasu kasheni in suka tabbatar babu Kai a Duniya kayi min Rai kayi min gata Kar a tarwatsa min farin ciki don Allah ka tashi faruk kace min baka mutu ba kana Raye

Yadda take jijjiga gawar mijin nata ne ya sake fahimtar Dani lallai munzo gabar da wasu mutanen suke so muzo don su wulakanta mu musamman Ammi da Yan uwan Daddy basu kaunar ta don kawai ta kasance ahalul kitabi kafin Auren Daddyn shikenan suka Dora Mata kahon zuka sai gashi yanzu Daddyn da ya zamo Mata garkuwa yau Babu shi duk da ban San komai Akan abinda zuciyar ammi ta kunsa ba Zan iya cewa zafi biyu takeji a yanzu

Zafin Rasa mijin da yayi Mata gata da Kuma zullumin abinda zai biyo bayan mutuwar mijin nata daga bangaren Yan uwan shi

Tunda na tsinci kalmar mutuwar Daddyn a harshen ammi nake Taya ta kukan Rashi ko nace nake Taya ta tausayawa kanmu don nice nayi Rashi tayani kawai takeyi
Chapter 1 · 0% Book details