← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganganun da Yake fada ne ya tabbatar min da lallai baya cikin hayyacin shi domin ko sambatu yake tayi Kuma Ni da ammi an kasa samun Wanda zai Mika mishi wata kalmar da ta danganci hakuri ko Rarrashi
Duk juriyar sulaiman sai da ya Rungume Yaya Abdullahi Yana Taya shi kuka Koko tausayin shi ne ya Kama shi oho

Bai tsinke ba sai da yaji abinda Alh Mustafa da Yan uwan mahaifin mu sukayi na karbe duk kaddarorin Daddyn. Ya kasa tankawa ammi akan wannan Rashin mutuncin kamar yadda ya kasa tsayar da hawayen shi.

Tun daga wannan Rana sai Rayuwa tayi Mana wani irin sauyi me yawa sauyin da yazo da kaddarori kala kala domin ko Yaya Abdullahi Bai samu zarafin komawa Egypt ba Domin ko kudin da ake biya mishi ba kadan bane Dole ma karatun ya tsaya ya dawo gida ya zauna muke Rungume da hannuwa in da muka tsira da gidan da muke ciki da Kuma motocin da Daddy Yake Hawa har guda uku sai ta ammi guda Daya don haka ammi ta taramu nida Yaya Abdullahi take fada Mana cewa zata siyar da Tata motar ta nemi wani kasuwanci ta Rika yi saboda mu samu na cin abinci inda Kuma yaya Abdullahi ya kawo shawarar a siyar da duka motocin sai a siyi babbar mota wadda zata Rika yin sufuri ana bamu kudin muna yin lalurar mu.

Ammi tace A a Kar a siyar da na Daddyn Wai hakkin mune Kar suzo su shige a banza Amma Tata ko ta shige a wurin hidimta Mana batajin komai Akasin ace gadon da mahaifin mu ya bar Mana ya salwance bamu Mori komai ba don ta San cewa abinda su kawu madu suka karbe da sunan Adana Mana sun dai fada ne kawai Amma ba adanawar zasuyi ba

Abdullahi ya tambayi Ammi har da kudin Daddyn na account din banki duk sun kwace?

Tace har fa abincin dake store Basu Bari ba sun Jude Kai sururun shi ma da komai na dakin shi Basu Bari ba sun kwashe Wanda Bai bar wannan ba yaushe zai iya Rike Amanar maraya? Ni dai Nagode wa Allah na Kuma godewa uban ku da yayi silar kawo Ni cikin hasken musulunci ba Kuma Zan butulcewa Ubangiji ba don wasu daga cikin bayin shi suna goranta min Ni din tuba nayi . Na yarda na Kuma Amince da musulunci shine karbabben addini wurin Allah na Kuma gode da ya Azurta Ni da samun ku a cikin musulunci sai dai Yan uwan uban ku da suke zagina da aibata Ni Akan tuba na Kuma ko su zanyi musu uzurin jahilci don aganina irin karbar da Dan uwan su yayi min irin ta ya kamata ace sunyi min kasancewar shi musulmi Dan uwan musulmi ne sai suka nuna min har abada shi Wanda ba musulmi ba in ya shigo cikin musulmi bashi da muhalli sai gori sai kyara da hantara. To babu komai in ma sunce ba zasu karbe ku a matsayin Ya'yan Dan uwan su ba Ni ina son ku tunda Kuma na hakura da Yan uwana da iyayena da gatana na baiwa komai da kowa baya Suma Zan iya Barin su tunda nayi Ruko da igiyar Ubangiji nasan ba zata tsinke ba sai mu Riki Allah Ni da ku nasan ya ishemu a ko ina Kuma ko yaushe

Mun Sha kuka da Jin wannan magana ta ammi Domin ko Bata taba fada Mana wani Abu da ya girgiza zukatan mu kwatankwacin irin wannan ba inda Kuma muka hakikance lalli Wanda yayi Rashi irin namu shine ya San dacin da ke akwai cikin Duniya Kuma Wanda Bai Rasa Uwa ko Uba ba hakika Bai San wani bakin ciki Mai yawa ba

Rayuwa tayi Mana sauyi hatta da irin cimar da muka Saba da ita ta sauya sabulun wanka ma ya sauya daga porrin zuwa Dan gida Nigeria. Makwanci ya sauya sutura ta sauya a komai mun samu sauyi kamar yadda sauyin Rashin Daddyn ya same mu Haka sauyin komai ya nuna kanshi a garemu

Tuni aka siyar da motar ammi aka siyi karamar motar gwalp wadda kuma ta Rasa Wanda zata dankawa Amanar ta don ba kowa ta sani ba inda ta tuntubi mama ko za a cigita Wanda zai karba yayi Mata sufuri ita Kuma mama tace zatayiwa mijin ta magana ya samo Mai Amana. Yaya Abdullahi yacewa ammi shi zai Rika Jan motar Yana zuwa Kano kaduna da sauran Yan garuruwan da ke kusa Wanda zai iya Amma Ammi tace Bata yarda ba don ba sabawa yayi ba Kuma ma Bata yarda ba wahala ce tukin mota . Duk nacin da yayi ya Kuma nuna Mata duk Wanda za a samo ba zai Kai ya shi ba Amma Ammi tace Bata yarda ba gara ta bude mishi shago ta zuba mishi Yan kayan treda ya zauna anan seet room din Daddy Wanda kofar shi ke kofar gidan

Haka Kuma akayi Yan sauran kudin da ta Rage na ragowar kudin motar ta su ta zubawa Yaya Abdullahi kayan treda Kuma cikin ikon Allah Asirin mu ya Rufu a ciki muke samun na hidimar gida har ma ayi Mana hidimar karatun mu Ni da sulaiman dake makarantar kayalwa dake kofar durbi Ni Kuma Ina makarantar scondry ta government college Yar kutungu

Muna ta Rayuwa a Haka cikin ikon Ubangiji da kallon komai Akan idanun mu da zukatan mu da Kuma godewa Allah a ko yaushe Kuma kowane irin hali da Kuma Mika hannu mu karbi ko wace irin kaddara kaddarar ta Miko Mana zamu karba mu Kuma godewa Allah tare da neman sauki acikin kaddarar da kaddara ta Miko Mana

Wata hudu da kwana goma da Rasuwar Daddyn mu ta fita takaba inda lissafin hakan da Kuma kwanakin mahaifina a kasa Bai taba kubce min ba a kullum dai nayi alkawarin Raka shi da ADDU A zuwa makwancin sa wadda na tabbatar ita kadai ce gatan da zanyi mishi shigen Wanda yayi min

Na dawo makaranta kenan na Tara's da ammi tayi wanka tayi Yar kwalliyar ta kadaran kadahan cikin wata atamfa me saukin farashi wadda mama ce ta siya Mata ita ta kumayi lalle abinda ta Dade batayi ba tunda Daddyn mu ya kwanta Dama tayi sallama da ko Mai Mai kamshi bare lalle sai dai Kuma duk da wannan Yar kwalliya da tayi maimakon Naga tana murna sai na Tara's tana kuka abinda ba sai an fada min ba tuno Daddy ne yasa ta kuka

Ta tusa aya da gyadar da ta soya zata Rabawa makota Amma sai Kuma take inda ta karya zuciya ta Nima sai na soke kaina cikin cinyoyi na Ina tuno Daddy da Kuma kalubalen da Rashin sa ya bar Mana wanda shi Allah baya barin wani don wani yaji Dadi. Lallai da Ubangiji na barin wani don wani yaji Dadi to da lallai muna daga cikin wadan da ba zasu taba zubar da HAWAYE don bakin ciki ba sai dai kukan Dadi irin na Ya'yan gata Domin kuwa na tabbatar Daddy zaiyi iyakar kokarin shi don ganin bamuyi kuka don Bakin ciki ba sai dai kukan Dadi

Haka Ammi ta bawa zuciyar ta hakuri Nima na bawa tawa muka share hawayen mu ta kulla ayar da gyadar ta bani na Rabawa makota gida gida har wasun su sukan Aiko Mata da Yan kudi Wai sadaka ce wasu Kuma abinci danye sai gashi ta samu kudi masu yawa da abinci

.washe gari sai ga Yan uwan Daddy su kawu gide da yagana da kawu madu sun diro gidan suna zare idanu Alamar dai Rashin mutunci ne ya kawo su.............

Labarin GARWASHI na kudine ga Mai son cikakken labarin zai biya 300 ne ta wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Salon labarin daban yake da sauran Kar ku sake ayi Babu ku bare abaku labari

Gidan iko ne sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
9//10
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Har kullum Godiyar ta tuke ga Ubangiji Mai ikon kowa da komai da Yake nufar bayi da abinda Yake so su zamo ko su kasance aciki ne ya nufeni da alkalami Wanda Ni kaina ban San yadda akayi hakan ba salati da Aminci ga shugaban halitta S A W Allah ka Kara wasila da fadila agareshi da Ahalin gidan sa da masu biye dasu da kyautatawa

ADDU OIN fatan ALHERI ga mahaifina da mahaifiya ta fatan Rahama fatan Dacewa fatan samun babban Rabo a Nan Duniya da can lahira

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

...........Na zube Agaban su kawu gide da kawu madu da Kuma ya kumbo yagana Ina gaishe su yayin da ammi ke kokarin shimfida musu tabarma tare da kawo musu Ruwan sanyi ta Kuma ce na kirawo Yaya Abdullahi yazo ya gaishe da su kawu madu

Duk wannan abin da ammi ke musu cikin kallon banza suke binta Haka Kuma Babu Wanda ya amsa gaisuwar ta bare ya kalli Ruwan da ta aje musu

Muka shigo Ni da Yaya Abdullahi ya zube Yana gaishe su suka amsa mishi cikin sakin fuska da Fara a har suna mishi gaisuwar Daddyn abinda ya bani mamaki sosai ko da Yake shi Yaya Abdullahi yayi sa a su kawu gide suna son shi kamar ba Dan ammi bane da suke saukewa kwandon tijara Kuma bayan Haka ma sunfi tsana ta fiye da sulaiman Wanda Bai tako sa ar da Yaya Abdullahi ya tako ba
Chapter 4 · 0% Book details