Sashe 6
Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsokaci Akan masu siyen labaran mu su Kuma fiddoshi waje suna yadawa to ku sani kudin da kuka biya ba na copyright bane bare kuce kun siya Kuna da damar yada shi yadda kuke so kudin karatu kuka biya idan son yadawa kike to kicewa marubuciyar copyright zata siyar Miki kigani idan cinikin ku zai tsaya a 300 ko 500 don Allah mu Rika kiyaye hakkin juna
Kyautar wa ga Anty fauza Yar Amana ba Zan taba mantaki ba Koda lokaci yazo da Zan aje alkalami don kinyi min Amanar da Zan Dade Ina tuna ki Allah yakara sutura
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
..........Gaba Daya naji Duniya da Rayuwa sun fice min Arai. Banda ALLAHU Babu Mai tsara hakan . Na tuno Ammi da labarin da ta bani na yadda ta hadu Daddyn mu har zuwa auren su Wanda ya Tara kaddarori masu yawa inda Daddyn mu yayi Mata gata yayi mata sutura ya kawota cikin Ahalin shi Wanda basuyi Mata maraba ba Amma yace tayi hakuri shi din zai zame Mata uwa Kuma Uba har da dangi.
Kuma hakan ya kasance har ma fiye sai gashi tana tsaka da bukatar shi Ubangijin da yayi Mata baiwa da samun shi ya Kuma yi Mata wata baiwar ta Rasa shi in ba Allah ba wa ya Isa yayi hakan?
Na dago kaina na kalli Yaya Abdullahi dake Rike da hannuwan ammi Yana goge Mata HAWAYE Yana kuma Bata hakuri ita Kuma sai Albarka take ta saka mishi Akan abinda yayi na tuburewa da kin bin su kawu gide. Shima Kuma hakuri Yake ta Bata Yana son kwantar Mata da hankali
"Kiyi hakuri Ammi kaddarar mu ce Haka da yardar Ubangiji ba zamu taba tozarta ba don Allah kiyi hakuri Akan batun gidan Nan zamu tashi mu bar musu duk yadda aka Dade a gidan Duniya wata Rana za a tako gidan lahira
"Wannan Haka yake Kar ka damu Abdullahi tunda na Rasa mahaifin ku nayi hakuri babu abinda ba Zan iya Rasawa na jure ba fatana Ubangiji ya SHIGA lamarin ku ko da bana Raye Kuma kada Ubangiji ya sa nayi nadamar kasancewa cikin musulmi da musulunci . Tunda na yarda Allah Daya ne ai nagama yin Dace . A ko Ina Kuma ko yaushe Banda abinda Rikewa face Allah iyayena ma na barsu na zabi Allah na Kuma tabbatar ba zai wulakanta Ni ba Kuma kuyi hakuri da duk irin Rayuwar da kuka samu kanku aciki Allah shine Mai zanawa bawa kaddara idan aka zano maka ita baka isa ka goge ta ba Allah ya kaimu Nan da wata gudan in Sha Allah zamu samu wani matsugunnin
Haka na SHIGA zaga gidan mu Ina Rayawa a zuciya ta Wai Nan da kwana talatin zamu tashi mu barshi tuni HAWAYE na suka kafe Akan in na tuno yadda Rayuwa ta ta faro da yanzu da irin juyin da tayi min sai dai nace "ALLAH na gode maka Allah ka Kara min imani kasa Kuma na cinye dukkan kaddarori na ba tare da na Rasa imani na ba
Na Gama zagaye gidan kafin na koma Kan motocin Daddyn Suma Ina shafasu zuciya ta na tuno min abubuwa masu yawa akan mahaifina da irin tanadin da yayi Mana a Rayuwa Ashe kana taka NE Ubangiji Yana tashi tashin Kuma itace tabbatacciya.
Na tuno irin motar da na taba nunawa Daddyn nace Ina son ya siya min ita ya Kuma ce inayin candy zai gwangwanje Ni da ita Ashe kafin nayi candyn kaddarori sun zagaye Rayuwa ta
Naci gaba da shafa motocin Daddyn inaji a Raina tamkar jikin shi ne nake shafawa sai Kuma zuciya ta take kissima min kudin motar Nan tashi wadda ya siyo daga karshe wato homa Jeep
Sai kawai naji zuciya ta na fada min to me zai Hana mu siyar da homar mu fanshi gidan mu da ake bamu notice?
Ban tunkari ammi da maganar ba sai na fita wurin Yaya Abdullahi a shagon tredar shi Yana zaune inda na ga kayan shagon sunyi kasa sosai saboda Akan su kadai muka dogara acikin su ne mukeyin komai Ashe ko Dole suyi kasa Dama gashi naji Ammi na fadin sufa dama kayan treda ba wata Riba gare su ba
Na dubi Yaya Abdullahi inda na gano Ramar shi wadda ban taba kula da yayi ta ba. Da na tsura mishi ido ma Sai na ga ba Ramar kadai yayi ba har Baki fatar shi tayi sai naji tausayin shi ya kamani musamman da na tuno inda Yake karatu wato Egypt sai Naga lallai Dole zafin Nigeria ma yasa shi Baki
"Yaya ne Zahra me kike so? Halan cakulat din Zaki kwashe min? Nayi murmushi Wanda ya taho da hawayen tausayin shi matukar yaga dayan mu cikin damuwa to yafi mu SHIGA damuwa don Haka nace
"Dama Yaya Abdullahi wani tunani nayi me zai Hana a siyar da wannan sabuwar Jeep din ta Daddy sai inga kamar ta Isa ta fansar Mana gidan mu hannun su kawu gide Koko Yaya kake gani?.....
"Kin ko yi tunani Mai kyau Zahra ya akayi ma bamuyi wannan tunanin Ni da Ammi ba? Muje ma yanzu in fada mata shawarar ki don itace ma mafita
Ammi da taji abinda Yaya Abdullahi ya sanar da ita sai tace
"Shiyasa ba a Raina tunanin yaro kowa da irin balagar da Ubangiji yayi mishi wani azancin magana wani Kuma ta hangen nesa kunyi tunani Bari nayiwa mama magana sai ayiwa abban su Nana magana ya samo Mana me siye
Haka kuwa akayi motar Bata dauki lokaci ba aka siyar da ita kasancewar sabuwa ce ajiki Kuma sabuwar yayi sai gashi kudin ta sun iso kudi masu auki kuwa inda Yaya Abdullahi yace duka ma asiyar dasu ko wani kasuwancin sai ayi da kudin su.
Haka kuwa akayi sai dai su din basuyi Darajar ta farko ba Domin kuwa Basu kaita Daraja ba inda Kuma har yanzu ba a samu Wanda zai karbi motar Ammi ba inda abban su Nana yace Yana tsoron mutane ne saboda ba bu Allah a ransu shi Kuma Yana tsoron ya kawo Wanda zai zalunci bayin Allah Amma yace Ammi ta Kara hakuri in Sha Allah za a samo Wanda zai karba
Kwanakin da su kawu gide suka diba na kwana talatin ya na cika kuwa sai gasu wannan karon daga shi sai kawu madu suka Zo
"Yaya kun tattare kayan ku dai ko Abdullahi? Fadar kawu madu
Yaya Abdullahi yace Eh kawu Amma akwai wani hanzari ba gudu ba Ina son ku Kira dillali yayiwa gidan Nan kudi muji idan zamu iya biya sai mu biya.....
Kawu gide yace ai shi din aikin shi kenan yiwa Kaya kudi don duk dabbobin garin su shike musu kudi wannan gidan ma zai iya mishi kudi....
Yaya Abdullahi yayi murmushi Yana fadin kawu ai dillalin dabbobi daban da na gidaje.......
"Au me kake nufi kenan? Kana nufin ba Zan iya mishi kudi ba kenan? Yanzu in ubanka ne Zaka karyata shi irin Haka? Da sauri Yaya Abdullahi ya bashi hakuri Yana fadin ba Haka bane
Ya Sha mur Yana micincina idanu ya dubi gidan Yana fadin Banda an kashe gidan da kazanta ai har million Tara zai iya kaiwa inda Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da yasa hadamar tasu ba Mai yawa bace Amma Kuma da ya nemi su rage sai suka ce in yayi musu a million Tara din su biya in kuwa Bai musu ba to su nema gaba don yanzu zasu Rufe gidan.......
"Yayi kawu mun gode muje banki a Ciro kudin
Haka suka tafi da kawu gide aka Ciro kudin aka damka wa kawu madu inda Yaya Abdullahi yace su bashi takardun gidan da suka amsa.
Kawu madu ya Kara gyara Rikon da yayiwa kudin Yana fadin
"Ai Kai da uwar ka Baku da wayo tunda kukayi nufin yaudarar mu dama sai da nace akwai kudin marigayi a cikin banki abinda ta kawo Dan debowa kawai tayi ta boye sauran to wadan Nan kudin idan dai har ummaru zai dawo Duniya to zasu dawo gareku idan har son gidan Nan kukeyi sai kun Kuma kawo wata million taran kafin ku zauna acikin wannan gidan su Kuma wadan Nan kudin mun Rage ne daga cikin kason gadon mu don Haka idan Kuna da muradi kwa iya fiddo wasu kudin shima kafin Nan da Rana irin ta yau sati guda Daya Tak muka Baku idan da kudi ku zauni gida idan Kuma babu to na Rantse maka da kabarin uwa ta kayan ku ma waje Zan auna muku su kaji na Gaya maka
Ya dubi kawu gide Yana fadin
"Muje gide. Da Haka suka fice Rungume da tarin kudin har million Tara
Ammi ta sauke tagumin ta da doguwar ajiyar zuciya babu Mai motsin kirki bare magana inda Kuma yaya Abdullahi yace karar su zai Kai Amma Ammi tace Kar ya Fara ya dai Ida kwaso sauran kudin ya basu inda Ni Kuma nace Mata da dai mu Kuma Basu kudin suyi tafiyar su dasu gara mu siyi wani gidan tunda ta Hana ayi karar su don wannan damar da suka samu ce tasa suke tsula iskancin su
Sai dai duk da saka cigiyar da akayi na gidan da zamu siya da akayi kafin cikar wa adin da su kawu gide suka bamu yazo shiru ba a samu ba har zuwa Ranar da su kawu suka dawo don Jin inda aka kwana don Basu ma jira jin wani bayani ba inda kawu madu ya Soma fito da kayan mu Yana watso su kwar gida duk wani Abu da ya tarbi gabanshi surowa kawai Yake Yana watso su waje
Ammi tacewa Yaya Abdullahi ya kwaso sauran kudin dake bankin ya bawa su kawu madu shi Kuma yace Yana tsoron ya dauko sauran kudin ya Basu suyi Mana yadda sukayi a farko Amma ganin sai watsi suke Mana da Kaya yasa yaje ya fito da kudin Amma yace sai sun bashi takardun gidan kafin ya Mika musu kudin.....
Kawu gide ya Miko mishi takardun a cikin jakar da suke tun farko kafin Yaya Abdullahi ya Mika musu kudin suka fashe da Dariya a lokaci Daya kafin kawu madu yace