← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 19

Sashe 7

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai tunda kukace yaudara ce aikin ku mu da kune in Baku fiddo Mana hakkin mu ta Arziki ba ai zaku fito dashi ta tsiya
Wai Kai Dan Boko ba zaka bada kudi ba sai an baka takardu to ga takardu Nan Amma fa na bogi ne na asalin suna hannun mu idan kazo zaka iya biyan wata million taran na maido maka su don Haka ku fito zamu datse gidan mu...............

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Kar ku Bari ayi Babu ko don littafin GARWASHI daban yake da sauran

Sunana Hadiza Bara'u Gidan

Ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
13//14
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Allah kayi musu Rahama ka yafe musu kayi musu dukkan wata Alfarma da kakewa muminan bayinka

Ba zan taba mantawa da wadan Nan mutanen ba
Anty Jamila Yusha u
Anty Rahane sani Dan Kani
Anty Amina brn kebbi
Antyn Yola Allah ya Kara sutura

Sai haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

............Yaya Abdullahi ne yaga da gaske suke Shirin izo keyar mu waje su Rufe gidan gashi Kuma babu inda zamu Kai kayan da sukayi Mana watsi dasu kofar gida bare inda zamu saka hakarkarin mu mu kwanta

Ya zube Agaban kawu gide yana Rokon shi Alfarma.....

"Kawu kaifa uban mu ne don Allah Kar ku tozarta mu bamu da inda zamu koma kuji tausayin mu sau biyu fa Kuna karbe Mana kudi don Allah Kar ku Rufe Mana gida.....

"Ai tunda kukace ku Yan iska ne Kai da Uwar ka ai kun gamu manyan Yan iska tunda babu Arziki a cikin lamarin ku babu yadda bamuyi da ita ta fiddo Mana hakkin mu ba Taki Kuma Kai da muke ganin namu ne ka goyawa kafurar Uwar ka baya ko gidan ubanwa kuka samo wadan Nan kudin Haka in ba satar su Uwar ka tayi ba? To ko zaku shekara kuna kawo wasu kudin da sunan fansar wannan gidan to muma zamu shekara karbe muku kudi tunda abin naku yazo da Raini da yaudara wannan gidan dai ko kwai kuka NASA cikin shi sai kun barshi in ma Ruhin ku ke ciki sai dai ku marawa ubanku baya

Ya Soma hado Kan get din Yana kokarin Rufewa Dole muka ido kwaso kayan mu Yaya Abdullahi Kuma ya karbi key din motar Ammi dake parking space ya fito da ita muna kallo ya bugawa kofar manyan kwaduna sukayi gaba suka barmu muna tattare kayan mu da sukayi watsi dasu.
Dole gidan mama muka shigar da kayan mu acikin shagon gidan muma Nan mukayi mazauni don can cikin gidan dakin mama ne da na Mai gidan ta sai na Ya'yan su don Haka abban Nana yace idan zamu iya Zama a cikin shagon to mu koma kafin ya cigita Mana gida

Na dubi shagon Wanda kofar shi take cikin soron Kuma akwai wadda ke fita waje inda beraye ke gadar su son Ransu yau anan Allah yayi ikon shi Akan mu da komawa Rayuwa lallai bawa Bai Gama sauyawa ba sai Ranar da ya komawa Ubangiji

Muka koma Rayuwar cikin shago mu duka muka gwamutsu a wuri Daya har da Yaya Abdullahi Wanda yaso ya bar Mana Nan ya koma kwana waje duk da kasancewar yanayin damuna da ake ciki Amma Ammi tace Bata San zancen ba tunda wurin Yana da girma Dole suke wuri Daya shi da sulaiman Ni Kuma Ni da Ammi

Mama tayi ta fada da taji dalilin wannan wulakancin da su kawu sukayi Mana na karbe Mana kudi har sau biyu Kuma sukayi mana watsi da kayan mu......

"Haba Amina wannan ai Ragon azanci kikayi da Kika Bari aka sake Basu wasi kudin mutumin da Bai iya son dan uwan shi ba yaushe kike tunanin zai tausayawa Ahalin sa? Kuma ai maganar Abdullahi ai itace gaskiya da kin bari yayi karar su ai shi alkalin ba irin su Yake ba yanzu irin haka ke da Dadi saboda Allah? In ma da gaske suna da hakkin ai ba zasu karbe muku kudi har sau biyu ba ai in mutum ya Gane kana shakkar shi to shi Kuma lokacin ne zai bude kofofin tozarta ka me akeyi da muguyen dangi irin wadan Nan? Ammi sai hakuri take Bata tana kuka don gani takeyi ta batawa mama Rai don da gaske mama ta fusata ba kadan Amma Dole mama tayi hakuri tace

"Naji babu Dadi ne Amina da ace a gabana hakan ta faru wallahi ba Zan kyale su ba don zanyi wankan tsarki ne in siyi fadan Nan in yaso Ni dasu mu gurfana gaban kuliya manta sabo haba me akeyi da dangi irin wadan Nan ai gara a Raba gari kowa ya tsaya matsayin shi tunda Wanda ya hada ya Raba ko shi din ma ai ba dadin su yaji ba Amina kema kinfi kowa sanin hakan

Rayuwar mu ta koma a gidan mama inda Yaya Abdullahi ke bude shagon shi na tsohon gidan mu muna samun na hidimar yau da kullum duk da kayan shagon sunyi kasa kwarai mun cinye sai Dan abinda ba za a Rasa ba

Akace zari dai Daya Bata barin Dame domin ko sannu ahankali kayan shago suka Kare kaf mun cinye su tas har ta Kai abinda za a Kai baka sai Mama ta tallafa Mana inda duk muka fita a kamannin mu na asali muka koma wasu Yan Allah ya Baku mu samu😭

Hakika mama ta taka Rawar gani Akan mu da Rayuwar mu domin ko tsayin zaman mu a gidan ta tayi Mana hidima da dawainiya ita da mijin ta Wanda shima ba karfi ne dashi ba . Idan ammi na kuka tana godewa mama akan karamcin da take Mata sai Mama tace ai Nima kinyi min karamci Amina shi kuwa Dan halak baya manta halacci Ni meye bakiyi min ba lokacin da muka SHIGA namu halin kwatankwacin irin wannan? Sai na Gane akwai hikima cikin wata Karin magana da malam bahaushe yayi da yace ka yada ALHERI ka tsince shi a gaba domin ko ban mance ba lokacin da Ammi keyin girki ta aikawa mama sau uku a Rana lokacin da Abban Nana yayi tafiya neman kudi komai ammi bawa mama takeyi ko ta nema ko Bata nema ba hatta da omo da Sabulu aika Mata takeyi sai gashi yau da ace ammi irin Rayuwar Nan tayi irin ta kaza me ci ta goge Baki ko muguwar makotaka tayi Ashe da bamu San inda zamu jefa Kan mu ba

Muna cikin wannan halin tsaka Mai wuyar ne Kuma aka samu gidan haya Amma a can kofar marusa sai dai kudin da zamu Fara biya ma babu su sai mamace ta biya Mana muka kwaso muka dawo kofar marusa muka baro makotan kirki irin mama muka dawo wata unguwa me cike da kwatoci da gidajen laka Mai Rufin kwano ko silin Babu kasa Kuma babu tiles Sai daben sumunti. Daki biyu ne a gidan inda mukayi masauki a Daya Ni da Ammi da sulaiman muka barwa Yaya Abdullahi Daya sai dai Kuma inda take a kasa take dabo shine babu abinda zamu juya na Sana a Wanda Dole sai da shi ko da Rayuwa zata tafi yadda ake so saboda bukatun yau da kullum Dole muka Rungume hannuwa inda Kuma mama da Abban Nana sukayi Mana karamcin nasu suka biyo mu da shinkafa da garin masara da garin Dan wake Ni da kaina naji araina da ace abban Nana ne danginmu akasin su kawu gide da zumunci Bai zamo zumuncin zamani ba Kuma da ba a zagi Yan uwa da dangi ba Haka muka Mike da kaddarar da Ubangiji ya zano zata same mu . Gidan da muke ciki na wata masifaffiyar tsohuwa ne marar hakuri kamar zawo wadda Allah yayiwa Arzikin gidaje da shaguna Wanda ta bayar ake haya ake biyan ta kudin hayar Wanda Kuma ya kuskure Bai biya ba zai jita tamkar yaji a ido ko Kuma in yanayin damuna ne baka biya ba tasa a kware maka kwanon Rufin dolen ka ka biya ko ka Kara gaba
Kuma baka Fara SHIGA muhallin ta sai ka biyata kudin da kukayi na wata ukune ko shekara

Na dawo Daya makaranta inda na shigo sabuwar unguwar mu inda nake wuce mutane suna min Rakiya da ido na Kuma San Rashin sani NE ya kawo hakan ko da Yake nasan a yadda nake ko da Rayuwa tayi Mana sauyi me yawa na Rashin abubuwa masu yawa Amma Kuma hakan Bai sa na Rasa abubuwa uku ba wato kwarjini da tsabta da Kuma kyawu ba wannan Kam Koda na Rasa komai ban Rasa su ba don Haka sai na wuce Abu na bana kulawa Kuma dama Ni din ba me son wasa ko shirme bace bare sharholiyar Yan mata masu irin shekaru na komai nawa cikin nutsuwa da kame Kai ko cikin kawaye ban Faye SHIGA ba kawaye na ma biyu NE a makaranta Suma ba nice na SHIGA jikin su ba sune suka shigo Wai Ina burgesu sai muke kadaran kadahan don ban saki jiki dasu sosai ba

Na shigo gida na iske ammi a tsakar gida tana girki tsakar Rana don babu kichen a gidan sai tsakar gida take girki inda na iske ammi na sakun Dan wake abinda na tsana a Rayuwa ta don duk Ranar da Kai Dan wake a cikina Koda kwara daya ne sai nayi ta zagawa bandaki cikina baya son sa Amma sanin da nayi ammi ta San bana son shi yanzu ne da na furta zata ce zata sama min wani abun Dole na maye kiyayyar Dan waken da soyayya bayan nayi Mata sannu da gida da Kuma aiki

"Yauwa Zahra ta kiyi hakuri kici Dan waken Nan sai ki Sha Yar kanwa gata Nan ba zai Bata Miki ciki ba naso na sama Miki ko garin kwaki ne Amma abin ya gagara.....
Chapter 7 · 0% Book details