← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan Al ada kuwa da na Kira banza kuwa itace ba za a taba daura Auren su da matar da Yake so ba sai sunyi gwaji Wai shi Dan sarki ba zai Auri mace ba sai wadda aka tabbatar da zata haihu don Dole ne yadda aka haife shi shima ya Haifa Kuma kamar yadda zai gaji mulkin gidan su shima sai ya bar Wanda zai gajeshi shiyasa ma ake ganin Dole ne ma ya haihu Kuma ba zai taba Auren matar da Bai sani ba ko ba zata haihu ba shiyasa ma suka bullo da Al adar ba za a taba daura Auren su ba sai an kawo yarinyar da zai aura din Koda kuwa tana wata kasa ne sai an kawowa yariman ita ya kwanta da ita tsayin wata uku zata yi a dakin shi tamkar matar shi idan tayi ciki a cikin wannan lokacin na watanni uku to shikenan sai maganar Auren su ta Mike a Dora sanwar Aure ya danganta da yadda suka tsara bikin wata ta haihu a dakin yariman wata Kuma sai ta Tara Yara fiye da biyu ko uku kafin ayi shagalin bikin wasu ma har haihuwa biyar suna yi kafin Auren.

Idan kuwa mace tayi wata uku a dakin yariman Bata samu ciki ba to sai akara Mata wata uku wata shida kenan idan tayi wata shida babu ciki to wannan ba zata haihu ba Kuma duk yadda suke son juna Dole zasu hakura ya Nemo wata Ni kuwa sai nake ganin kamar ba ayi hikima ba wurin yin wannan banzar Al ada shiyasa ma naji na tsaneta ba kadan ba Ashe ban sani ba kaddara ta zano Dani a cikin wadan da wannan lamarin zai sako ciki ba

Muna tsaye a wurin wutar da na Gama tabbatar sai da aka Gama tsafeta don in ba tsafi ba ta Yaya daga kawai mace ta Rasa budurci don an Bata wata tantabara ta Rike ta Zo gaban wuta ba saka tantabarar akayi a wuta ba sai Kawai tantabarar ta mutu? Dole ne akwai tsafi da sihiri acikin Lamarin

Wata tsohuwa me amsa sunan kakar onye ta wurin Uwa ta fito hannun ta da wata yizga ta Soma zagaye su onye amarya da Ango Peter dake gaban wuta tana kada yizgar hannunta me kama da jelar doki sai da ta kewaye su sau ba adadi kafin Suma suka Soma zagaye wutar dake ci harshen ta na kokarin lasosu inda Allah ya fidda onye kunya Bata taba sanin wani namijn ba sai Peter inda tantabarin hannunta ya mace aka Kuma cilla shi sama Amma ya dawo kasa a matsayin matacce amma ita tantabarar hannun Peter da aka cillata sama sai ta tashi sama firrr abinta sai wuri ya kaure da tafin murna da sowa inda Ango Peter ya daga Amarya onye sama Yana juyi da ita inda Uwar Amarya tafi kowa murna da Jin dadin fita kunya da ace an samu matsala to da har gidan sarkin Sai sun fice sun barshi amma yanzu har kyauta sai iyayen Ango da shi kanshi sarkin Sai sun Mata kyauta kuwa ta girma da kasaita Wai ta iya tarbiya

Ango Peter Yana Rike da onye Yana juyi da ita a sama kafin ya sauke ta aka saki kidan Duma inda Kuma fili ya kaure da Rawa sai dai wani abun mamaki Ango Peter Yana dire Amaryar shi onye sai kawai naji anyi sama Dani ana juyi Dani inda naji wani tsoro ya kamani inda na Soma laluben wanda yayi min wannan Aikin idona ya fada Akan yarima Gibson Yayan onye wato yarima me jiran gado sai Kuma fili ya Kuma daukar tafi da sowa me tsanani abinda yayi matukar bata min Rai ya Kuma yi matukar faranta Ran Amaka da Maazi Nkem

Kan kace me? Sai ga sarki da kanshi da matar shi mamar su yarima Gibson har ma da su Maazi Nkem da Amaka har ma da mutanen Arziki sun Rufu Akan mu suna zaba Mana Ruwan nairori yarima Gibson Yana sabe Dani ana zuba Mana kudi wuri na Kara ksurewa da sowa da tabi

Aguje Naga wasu mata dake hidimtawa a gidan sarautar sun karaso a gareni dauke da wasu murjanai na garari suna daura min a hannu da wuyana har da kafafuna

Abunda ya Kara bani haushi Wai duk na meye wannan abun da suke min ? Kuma meye dalilin wannan dagawar da yarima Gibson yayi min alhalin Amarya ce kawai akewa hakan kamar yadda Peter yayiwa onye?..........

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me son Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Kar ku Bari ayi Babu ku don wannan Labari daban yake da sauran

Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI😂
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
25//26
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga yan uwana
Yaya shamsu Bara'u
Yaya murtala Bara'u
Yaya Sulaiman Bara'u
Yaya isma il Bara'u
Yaya Yusuf Bara'u
Yaya Ibrahim Bara'u

Fatan ALHERI har kullum gareku masoyan Rubutun Gidan iko kune gidan iko Baki Daya tunda kuke yinta 🥰

Haj Saliha Abubakar Abdullahi Zaria Allah ya Kara lafiya

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

...........Gibson ya zuba min ido tamkar yaga wata bakuwar halittar da ta bayyana a gareshi yanzu wadda Bai taba gani ba. Abinda ya bakan ta min Rai don bana son wani namiji ya tabani bare shi Gibson irin daukar da yayi min har hucin nunmfashin sa najiyo Akan fuska ta

Nima na zuba mishi nawa manyan idanun muka SHIGA kallon kallo inda na SHIGA fasalta suffar yarima Gibson kyakkyawan mutum Wanda shima ya fita daban a cikin Ahalin gidan su duk kuwa da kyauwu irin na Ya'yan sarkin to yarima Gibson ya zarta su don shima kamar ba Dan Nigeria ba fari ne tas har yellow yellow yakeyi ga cikakkiyar suffa ta maza da Bakin gashin Kai da kwantaccen saje da manyan idanu da gashin idanu masu kyau Kai karshen magana dai irin namijin Nan ajin farko

A yadda onye ta taba sanar Dani Ya'yan sarakunan da suka so yarima Gibson basa kirguwa Amma shi yace duk basuyi mishi ba Wai har wata Yar sarki da ta so shi ya kita mutuwa tayi saboda tsananin son da take mishi Kuma kasancewar ta ya daya tilo a wurin ubanta da ta mutu ubanta yace tunda yarima yayi mishi sanadin Yar shi zai ga abinda zai faru don ba zai taba yarda son shi ya kashe mishi yarshi ba saboda kiyayyar da Yake Mata to shima zaiga abinda zai faru.

Babu Wanda ya dauka furucin wannan sarki zai Zama matsala sai da yarima Gibson ya samu wadda Yake masifar so wata yarinya ce itama Yar gidan sarauta wadda suka so juna kamar su hadiye kansu Amma da akazo Kan gwajin da sukeyi na sai matar yarima tayi ciki ko zata shigo gidan shi da sunan matar Aure sai aka samu matsala domin ko sai da ta shafe watanni shida babu ciki babu Alamar shi inda a kace babu maganar Aure Dole Kuma a Rabu Amma soyayyar da sukeyi wa juna ta Hana su yarda da wannan daddadiyar Al ada tasu inda kuma Suma iyayen suka CE Dole ne a Rabu kowa yaje ya samu Wanda zai haihu dashi

Son da Gibson yajeyiwa budurwar shi yasa ya kwanta ciwo Mai tsanani Wanda ya haifar mishi gagarumin ciwon zuciya Wanda kadan ya Rage ya kwanta Dama wato mutuwa

Abinda ya dauke hankalin yarima Gibson daga Kan duk wata mace da zai kalla da sunan burgewa ko yaji zuciyar shi ta amsa Akan ta har ma ya Daina tuna zaiyi Aure Nan gaba sai gashi kwatsam kallo Daya yayi min ya manta da ajiyar da yayiwa mata wadda ake watsarwa a maliya

Azahirin gaskiya yarima Gibson bashi da wata makusa ta kowane fuska gashi dai kyakkyawa ajin farko gashi jinin sarauta gashi Kuma Mai tarin dukiya me Kuma yayi saura? A fuskar wasu kenan wasun ma kuwa irin su Amaka da Maazi Nkem Wanda suke cikin farin ciki da murna yau su kuwa wace irin sa a ce dasu da har suka haifo Yar da zata taka gidan sarki da sunan matar yarima Gibson?

Inda Kuma muka samu sabanin Ra Kenan don Ni ko ga farcen yatsana banji yarima Gibson ba bare ya burgeni a ido har yayi nasarar SHIGA zuciya ta inji Ina son shi ko kusa Haka Kuma ko Alama Ni ba Zan taba yarda ayi min wannan banzar Al adar da suke tutiya ba badon ba Zan iya yarda ayi min ba tunda Ni dai ko hannu na wani namiji Bai taba Rikewa ba sai dai don kawai bana Jin son yarima Gibson a Raina ba Kuma Zan so shi ko da kuwa mutanen garin Legos da imo zasu Kare

Na fincike daga Rukon da Gibson yayi min Ina Shirin barin wurin ne naji wasu Mata da na lura suna suka daura min murjanai din Nan ne suka dauko Ni Dan das suka nufi cikin gidan sarautar Dani inda naji haushin su ya Kara kamani Ina Shirin balbale su da masifa ne Naga sun shige dakin matar sarkin wato uwar su Gibson da onye har tsakiyar dakin ta Wanda ya gaji da kayatuwa da kayan kawa da ado irin na sarauta

Kan kace ? Suka shigo fito da wasu Kaya na daban suna Shirin saka min inda na Gane sun Raina min wayo tunda har suke Shirin kwabe min Riga gani zaune

Na Mike a fusace Ina zuba masifa suna bani hakuri suna sunkuyar da kawuna kamar wasu munafukai sai ga Mah wato matar sarkin itace ta sani nayi shiru ta Kuma nunawa Matan Nan kofar fita da hannunta suka kuwa fice suna sauri ita Kuma ta Soma saka min kayan Wanda ta Kare da Rataya min wasu murjanai a wuyana da Kuma Dora min wasu a kewayen gashina

Sai ga su Amaka sun shigo wadda ke ta murna da Jin Dadi Ni Kuma na Rasa Gane duk ana me ake min wannan tarairaya?

Haka biki ya Kare Amma ba tare da Ni ba don an hanani SHIGA cikin yan Mata Wai na fita a layin su
Chapter 12 · 0% Book details