← Book details Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Garwashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban tsinke da wannan lamarin ba sai da muka tashi tahowa inda aka lodo kayan akwatuna na garari da kasaita aka hado mu dasu tare da dukiya Mai yawa Wai kyauta tace daga yarima Gibson Kuma Yana Nan Zuwa mu gana ko ince mu fahimci juna

Duk wannan Abu da Yake faruwa ban San komai akai ba sai da muka Zo gida naji labarin da Amaka ke fadawa Yan uwana su Sony da Emmanuel Wai Ni din na shigo Duniya a sa a inda yarima Gibson ya ganni ya Kuma zabeni a matsayin matar Auren shi

Su Sony ma murna suke son suna ganin Ni Kam bayi Dace tunda Zan haifo princess in Kuma Zama matar 🤴

Dukan da wannan magana ta Amaka tayi min har ciwon Kai naji Yana sauko min ta Ina Ni Zan iya yarda da wannan abubuwan da na Dade da tsana na bikin Auren Yan yaren mu? Kuma ma Ni babu wani Gibson a Raina bare kaunar shi
Sai kawai na kudirewa Raina da zuciya ta Koda za ayi me ? Ba Zan taba Auren wani Gibson ba ni ai ba Yar sarki bace su kuwa basa Aure sai Ya'yan sarakuna to yaje ya Nemo wata Yar sarkin amma ba Ni ba don kuwa banayi bana kamar inayi...............

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Labarin Nan daban yake da sauran Kar ku sake ayi Babu ku

Sunana Hadiza Bara'u Gidan iko ke cewa saduwar ALHERI🥰
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
27//28
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Iitattafan Gidan iko
Jan kunne
Wuka a makoshi
Zan fasa kwai
Sai A lahira
Mugun kulli
Matar sarki

Dukkan su published ne Amma an dawo da Zan fasa kwai da sai A lahira online

Sadaukarwa ga iyayena guda biyu Uwa da Uba Wanda har abada bani da kamar su Allah kayi musu Rahama da gafara kasa su tabbatacci agidan ALJANNAH

Uwa ta ta kaina haj Habiba Abubakar magaji Yar Adua Allah ya Kara lafiya da nisan kwana Mai Albarka

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

...........Ina zaune cikin tafasar zuciya da Bakin cikin wannan Al amari Wanda su Amaka da Maazi Nkem ke ta fama yaya ta maganar musamman Amaka da take ta faman Kiran waya tana fadin a Taya ta murna Wai zanyi Aure a gidan igwai wato gidan sarauta ko da ya ke ba Amaka kawai ba hatta Maazi Nkem ma sanar da mutane Yake Aure na a gidan igwai din inda Ni Kuma nake ta ganin wautar su

Nasha mamaki da aka bude akwatunan da yarima Gibson ya Rako Ni dasu domin kuwa kayane irin na gidan sarauta tare Kuma da tarin murjanai da kayan Ado Amaka sai kakabin kayan takeyi tana murna ita da Maazi Nkem

Da Ranar zuwa coci kuwa tayi Amaka ba ta boyewa fastor komai ba har ta nemi a yi mata addu a yarta ta SHIGA gidan igwai da kafar dama in da Kuma fastor ya tambayi Amaka sun dai sanar da igwai matsala ta ta aljanu ko? Tace A a ba su fada ba yace to su fada musu don Kar suce an cuce su idan Gibson Yana Sona a Haka ko acan sai suyi min magana tunda lalura ce

Da Amaka ta dawo Bata boyewa Maazi Nkem yadda sukayi da fastor ba inda su duka cikin su ya duri Ruwa don suna ganin idan Gibson yaji ba zai Auri me cutar aljanu ba sai kawai sukayi mursisi suka ki fada

Ni kuwa tunda na kudurtawa Raina da zuciya ta ba zan Auri Gibson ba to Haka nake nufi banayi bana kamar inayi sai na shiryawa zaman jiran inji wata magana da ta danganci batun Auren mu da Gibson don in fashe fashewar da komai zai tarwatse

Zuwa wannan lokacin na Gama yarda matsalar ciwo na tana saga Alkur ani kamar yadda sumayya ta fada min sai kawai na SHIGA laluben ta Yaya hakan zata faru?
Sai kawai na Soma da Rufe tsiraici na tunda ta fada min harda shigar tsiraici ke jawowa mutum aljanu
Dama Ina da less less da atamfofin ma kawai dai nafi son shigar kana Nan kayan NE irin su English wear da sauran su don Haka sai na Fara da saka less da atamfa Ina Kuma sirkawa da kana Nan

Wata Rana na dawo daga makaranta Ina tafe a mota ta sai na kunna Redion motar abinda ban Faye yi ba ko da kuwa Zan kunna din to CD ne Zan saka naji cred debit ko 2 pac ko dangogin su amma a yau sai na latso cenal din FM inda Kuma najiyo ana Rera Kira a cikin wata murya Mai dadin sauraro sai dai ba muryar ce ta ja hankali na ba irin abinda naji Yana ratsa zuciya ta wato karatun kanshi naji Ina so

Gaba Daya na bawa karatun Nan hankali na da nutsuwa ta har na karaso gida Ina muradin karatun Nan Kuma bana son ya Kare don Haka da na Zo parking space din gidan mu ban fito ba sai nayi zamana A motar Ina sauraron karatun Ina Kuma Jin wani Abu na keta zuciya ta Yana SHIGA har Yana sauko min da wata nutsuwa ta musamman wadda ban San abinda ya kawo min ita ba ko da Yake ba zance ban San abinda ya kawo min ita ba tunda Bai wuce wannan karatun ba

Sai da awa Daya ta cika kafin aka janye karatun Wanda banso ba Dole na hakura na Kuma kashe Redion na fito na SHIGA gida na samu Amaka tana fadin Ina na tsaya yau ban dawo Kan lokaci ba? Nace Mata a makaranta ne aka tsaida mu wani gwaji

Washe gari da ma sai da na kunna Redion ko zanji karatun Nan amma sai na Tara's suna want program Wanda yasani Jan tsaki na kashe Redion

Bayan mun fito ne nake tambayar fauziyya ko tana da karatu a wayar ta ta tura min? Ta tambaye Ni wane irin karatu nake so? Nace Mata na Alkur ani nake so. Ta Jima tana kallo na kafin tace min Ina dashi amma me zakayi dashi? Na fada Mata jiya ne naji shi a mota Kuma yayi min Dadi shine nake so don nayi ji duk lokacin da nake so

Sai ta shiga yi min bayani akan Alkur ani da maganin da yakeyi Wai har maganin kunci da Bakin ciki yakeyi Kuma shi din maganin kowace irin cuta ce Kuma waraka ne

Ba Zan karyata hakan ba don Ni da kaina naji ajikina don Haka sai na ce mata kwarai na yarda da hakan don Nima naji hakan. Nafisat Rabi u Umar itama duk muna tare a wurin Kuma taji duk abinda muke magana akai sai tace
Amma kuwa Justina iyayen ki ba zasu damu ba idan sukaji kina Jin karatun Alkur ani? A garin mu fa gombe akwai wata yarinya da iyayen ta suka kashe ta don kawai tace tana son hijabi tana kuma Sha awar yadda ake sallah sai kawai suka kashe ta Wai gara ta mutu da dai tace salla tana burgeta kenan zata iya shiga wata Rana.
Nabi nafisa da kallo don Ni nasan nafi waccan yarinyar da aka kashe hadari don Amaka ko taraiya da masu salla Bata son nayi bare Kuma addinin su ya burgeni ai idan akwai abinda yafi kisa to sai Amaka tayi min shi Amma sai nayi maza na cewa nafisat Babu matsala

Hikimar da nayi itace hearphon nake sakawa a kunne na in saurari Kira ata yadda nake so babu Wanda yasan me nakeji

Abin mamakin da na kula dashi Ni da kaina shine yawan mafarkai da nakeyi Wai gani Ina kallon mutane suna salla wani lokacin ma Zan ganni a cikin sahun salla anayi tare Dani Kuma Wai wani gari ne da ba Legos ba don mafi yawan mutanen da muke sallar tare dasu farare ne tas masu dogon gashi Matan su Sanya da hijabi da Nikabi mazan kuwa sanye da fararen doguwar Riga sun Kuma yafa wani farin mayafi ko ja ko Baki kowa dai da kalar dake kanshi
Idan na farka sai inji Ina begen wannan wuri da na ganni in Kuma ji muradin inyi salla amma Kuma Ina tsoron Amaka ta ganni Dole nayi shiru

Kwana biyu Ina sauraren karatun Nan Ran Nan sai tsautsayi ya samu waya ta ta lalace gashi Kuma muna cikin strike wato yajin aiki bare fauziyya ta sake tura min karatun Alkur ani Dole na wuce kasuwa na siyo CD masu yawa na kawo mota na zube idan fita ta Kama Ni na saurara idan kuwa babu kowa a gidan sai na dawo mota na kunna na saurara

Tsautsayi Wai in ya wuni baya kwana Ranar Nan Yaya na Sony ya dawo gida babu kowa ya iskeni na kure volume cikin Kira a ta malamin da har na hardace sunan shi wato sudais na kasa kunnuwa Ina saurare har ban San lokacin da Sony ya shigo ba sai da Naga inuwar mutum akaina na farga dashi a tsaye ya zubo min idanu Yana Huci tamkar zai hadiye mu Ni da motar tawa inda Kuma na San kashina ya bushe don gashi can ma ya kwarmatawa Amaka da Maazi Nkem kafin Nan ma nasan shima ba kyale Ni zaiyi ba sai naji a jikina............

Labarin GARWASHI na kudine ga duk me bukatar Jin cikakken labarin zai biya 300 ne kacal Akan wannan account din 1780003378 Eco Bank ko Kuma katin MTN Akan wannan layin 08035191669

Kar ku Bari ayi Babu ku don labarin GARWASHI daban yake da sauran

Gidan iko shine sunan ke cewa saduwar ALHERI💃🏿
🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

🍒🍒🍒 GARWASHI🍒🍒🍒
Page
29//30
Hadiza Bara'u Gidan iko

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne Kuma abin kiyayewa ne

Sadaukarwa ga haj Lubabatu Ali Mai chanji marubuciyar Amaryar zamani akan Rashin mahaifin ta Alh Ali Mai chanji marnar gangare Allah yayi mishi Rahama yasa kwanciyar shi hutawa tare da namu iyayen duka dama dukkan musulmin duniya

Fatan ALHERI ga mahaifiyata haj Rabi atu Abubakar magaji Yar Adua Allah ya Kara nisan kwana Mai Albarka
Chapter 13 · 0% Book details