← Book details Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 24

Sashe 20

Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Amarya tayi tsaf gyaran jiki ake mata wanda ya fiddo da tsantsan kyau da hasken ta, batada damuwa ko d'aya saita rashin abokin tsokana kusa.
Duk da kullum suna mak'ale q waya, amma sosai suka jigata da rashin juna baran d'an kwanakin da sukayi tare sunyi shak'uwa
Dangi an had'u, yan katsina duk sunzo wasu gidan Hajiya suka sauka, Aunty Meenah itama da nata tawagar da yaranta da jikokinta biyu na wajan 'yarta duk suna zo
Dayake lokacin kad'an suka saka, sai Yau aka kawo lefe akwati two set, sai sark'an English gold data Gold k'iran Dubai tareda awarwaron su
Sai 100k acikin kayan, shinkafa buhu6, gero 6 Sugar shima haka buhu 6, sai chewing gum carton 6, komai yayi ba k'arya Idan ma akwai da kud'in yin ne
Dangin Aunty Meimi kamar gori kusan duk yammatan Sai da suka zo Sodangi itace kan gaba
Fadeela itama tanad'an mutsikka abubuwan gyaran jiki itama tai kyau, angama komai da ake buk'ata
A Yau Thursday akayi Igbo Day a harabar gidan su akayi, Ango baizo ba sai gobe dama mata ne zallah saboda shigar da sukayi exactly Igbo girl sunji dad'i ma dabaya gari
Abban su yayi musu order na kayan, so duk wanda yazo Idan ya cancanta sai abashi, kafin ranar and'anyi rihaza akan yadda rawar zata Kaya
Ko da aka gama aka watse yammata sallah da wanka sukayi, itadai bacci tayi, su kuma chat aka hau (kamar Auta tanason zuwa wani waje babu mai hanata chat)
Friday Ango yazo nan ma anyi Lunch maikyau da k'ayatarwa a NAGARTA multipurpose Hol anan akayi
Amarya shigan Material yellow tayi sai head da takalmi blue tayi kyau, Ango kansa yasan yes ce amaryar tasa
Washe gari Abuja suka tafi, Uban gidansa ya had'a masa dinner a Sharaton Hotel inda daga amarya har Angon Kakin Custom suka saka shida abokan sa, kyau dai koban fad'a ba kunsan za'ayi
Light make up Fateema Ta Annabi tamata, gashin ta yasha gyara guri guda aka ajiye shi mata shi, sai wani net maikyau tayafa asaman kayan sai takalmi da jaka colourn kayan tayi kyau
Save Ur self ne awajan, nan naga K'ungiya ta writers kowacce ta d'ebo abinci cikin plates ga nama ga chicken paper da chicken noodle ga juice kowacce ba magana sai zirawa take cikin gayu taunarma a hankali Gayu nace dole kuja aji
Daga baya naji wani k'amshi na tashi azuciyata nace wace wannan haka, meimi bee tace Auta Kwaiseh ce yar garin mu, wow ashedai writers ganin su yafi jinsu
Baran danaga Maman Bobo, STYLICH, Ya Hajja Queen Meemi Jabo Nafeesa Anker, Aunty Lubie itada Amaah kai Lallai writers yan gayu ne ga Faty malunfashi wai carkwad'i kowacce taci gayunta tana tafiya da cin abinci cikin nutsuwa
Ni gefe naja ina kallon su, shigowar wasu su biyu itace ta tsaidani da abinda nake. Kai Jidda Ja'o dama zakizo? Nazata baku gama presentation d'in ba?
Wallahi bamu gama ba, inason zuwa dai maganarta mai sanyi, a d'an sauri itada Rookie Sadau ne
Anan suka zauna kowacce tafara hiran school da exams ko test da zasuyi, Anee banganta ba inji Feedoh yar ficika, eh tana exam itada Amrah
Ok Allah yabada sa'a, ansha rawa da kid'a anyi selfie writers ansha photo na tarihi da selfie stick
Taro an tashi lafiya, amarya Ango yaso su kwana amma tak'i adaren suka biyo flight suka dawo
Biki daidai gwargwado anyi shi cikin ni'ima da k'ayatuwa Maman Ango itakanta wannan shine bikinta na farko bajinta daidai anyi, ankashe kud'i dama akwai su
Tare sukai mothers day, da Maman FUTHA tunda kusan k'awayen d'aya, Ango da amarya nan ma sunje
*Yau ranar Lahadi 10:00 aka d'aura auren Fadeela Abdallah da zakaran mijinta Omar Farouq Ahmad*akan sadaki mafi k'aranci 50k saboda neman albarka
[08/11 12:15 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻: Amarya tayi kyau, Gexna tasaka wadda kayiwa stone work, ajiki have gown ce make up maikyau, ga danginta baibaye da ita
Marok'a sunsamu abinyi, Abdallah yana mak'ale da ita
Taro dai anyishi cikin lafiya amarya ankaita gidanta dake kusa da gidan iyayen mijin ta. Wajan Mama aka fara kaita, fad'a akamata na tsakani da Allah
Abbanta saida yai hawaye yanason FUTHA kodan ladabin ta
Bayan kukan rabuwa da gida da tayi, da kuma kukan rabata da Abdallah da akayi harta tawo tanajin kukan sa, kan saiya bita
Gidanta plat house ne, gidane ko cikin Maitama Sai haka, iyayenta sunmata abin arziqi da bajinta koina cike yake da Kaya gadonta biyu komai dai biyu akamata ga gara da aka kaita da ita
K'annenta hardasu aka kawota, kuka take sosai, jin yadda siketa tsokanar ta gasu Sodangi sunce gobe zasu juya kuma harda Abdallah abin biyu ya hade mata ga zafin rabuwa da iyaye gana Abdallah
Fadeela da Sahaf suma shak'iyanci suke mata akan yau za'ayi wuju wuju da wata, Lallai broth namasa murna zai kwashi gara irin wannan gyara da kika sha haka waih broth zai jishi daam
Kada dai ki rikitamana Yaya ehe, kwashewa sukai da dariya
Basu suka tafi ba saida Ango yazo shi kad'ai yazo batare da kowa ba, turus yai ganin su Fadeela
Ku mekuke yi?, dama kira muke kazo sai mu tafi kada abarta ita d'aya. Ok a tashi to
Haka suka mik'e kowacce tana k'unshe dariya
Suna fita ya haye gadon yana murmushi one love sun takuramiki da magana koh?
Itadai shiru tai. Lek'a fuskanta yai data ke k'unshe cikin Maroon lifaya
Kai one love me kikayi idonki yayi ja haka, ko duk kukan ne?
Kai ta kad'a OK, bakison akawoki gida ne shiyasa kike kuka, yan kaki zanyi ko cin naman ki zanyi, tab'a jikin ta yai, OMG Plx kidena kukan haka jikin ki yayi zafi Plx abage kiyi shiru
Haka yayita lallab'ata harta ware jikin sa ya d'orata lifayan yafara warwarewa mata acewar sa akwai zafi
Da wayo da dabara sai ganinta tai !! waih rigar dake cikima ya cire kanta ta cusa da k'irjin sa tace plx one love meyasa kalli kaga kasaka ni jin kunyarka kuma ai nibanjin zafi
Tana magana a shagwab'e,dariya yai yace to ai inajin zafi nidai oya tashi nasaka miki rigarki muyi alwala muyi sallah ga almara'i da cocktai na tawo miki dashi
Yauwa tashi kare jikinta tafara shikuma yana k'ara sata jin kunyar sa

©@ut@r h@jiy@💅🏻

[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [08/11 1:37 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 141-145*
Chapter 20 · 0% Book details