← Book details Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 24

Sashe 17

Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

@ut@r h@jiy@💅🏻👸🏻💁🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [02/11 8:45 am] @ut@r h@jj@ju👱🏻‍♀✍🏻💅🏻📚📝:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Adda Bena Yau ban hawa online, bare nagamu da ke, Jabo ta zugaki nasan balinta, ina off yau hhh*

*page 116-120*

Sosai Abdul yai murna da yaran, haka muka tarkato sai gida, Kowa yana murna amma ni zuciyata a cunkushe take saboda b'atan 'yata
Hajiya da kanta tamun wanka ta gyara yaran, tayimun Tuwo da Miya sai kunun kanwa, ko data kamun ban iya sawa abakina ba inacan tunanin Baby
Kafad'anta Abdul ya tab'a yace Maman Baby kici abinci mana then saikiyi tunanin nasan bana komai bane saina abinda nayi miki nasan badan haqurin ki ba, wallahi bazaki yafeni ba
Nazamto macuci a gareki na danne miki hakk'in ki na yasar da 'yata na cuceta dan Allah kuyi hak'uri Ku gafarcen ba yin kaina bane plx Matar arzik'i?
Kuka na fashe da shi nace na yafemaka duniya da lahira, Amma Baby ta b'ata wajan 6 days kenan ba'a ganta ba
What! kina hauka innalillah wannan wacce irin masifa ce, bashiri ya bazama Sai nema
Danginta suma sunzo da su aka ringa nema amma har tsawan sati biyu ba labari, haka na ta rame na d'ashe bancin abincin kirki addu'a itace abar yina ko wani lokaci
Abban ki saiya zamo nafishi dauriya kullum cikin tashin hankali yake baya Iya cin komi
Rarrashi shine nawa, da ban baki duk da nima ina buqatar mai kwantarmun da hankaki
Chuchu koda tazo gida dayake bata nan, hankalin tashe dataga kowa a dangi ya koma yanda yake mun, gashi Abdul ko sauraronta baiyi ba
A ranar dataje d'akin sa duka ya mata, shi baisan wacce k'addara ce tasaka shi auren Chuchu ba, da da hali daya tsigeta a rayuwan sa
Lokacin da masu gadin gidan suka rink'a bashi labarin abinda yayiwa Zainab kuka ya k'ara saki, lallai Zainab mace ce ta arzik'i
Maman Chuchu dai komai yafara lalacewa dan Abban nasu yafaramata wulaqanci, kafin wani lokaci asirin jikin sa ya karye, nan itama yacimata mutunci yai kuka akan rabashi da tayi da wansa da family nasa
Gashi ta b'ata masa yara, babu na zab'e cikin su, ita ma Chuchu miji babu shi yamanta da ita
Munyi nema munyi nema har ba adadi, Abban Chuchu shine yaji lokacin da suke magana akan itace tasaka aka b'atar da BILKISU
Nan fa yazo yagayamana aranar Chuchu tasha duka koni danakeda d'anyen jego sai dana daketa, kuma yace ta fitomasa da 'ya
Hajiyansa kaf sukace court itace zata rabasu da ita
Dukan da taci shine yasaka taimaza taiwa wanda tabawa Bilkisu ya yar akan yaje yazo mata da ita
Tsit ba labari, gashi lokaci yana qurewa, ganin bazatayi nasara ba yasata Shiga malamai akan tanaso ayimata d'aurin baki adena maganar FUTUHA
Allahu Akhbar wallahi tundaga ranar ban qara magana ba, Har dangin Abban ta gara dangina suna magana
Tsafi gaskiyar maishi dan haka tayi mana, amma wani ikon Allah daga ranar bata k'ara samun dama kan kowa ba
Tayi zaman shekara biyu lokacin yarana sunyi kwari, Abdul ya saketa sakamakon ganin ta da yai da wani, yayi kuka yayi danasanin auren ta
Abban ta shima hak'uri yaita bamu, lokacin shima ya aurar da sauran yaran, itakuma tana zaune amma ba kwarjini
Dawowar mu sokoto dalilin baqin cikin ganinta da yai da wani,
Abokinsa Abban Fadeela sin had'u a Umrah shiyace ya dawo Sokoto
Yanzu gashi munyi zaman mu lafiya, lokaci yanaja nasara da d'aukaka ta zowa Abban ki ya fito takaran governor Allah ya bashi
Kowa yana k'aunar Abban ki, yaranmu suna sonki, duk da bama maganarki amma Su kina ransu, addu'arsu garemu da ke itace tayi sanadiyyar warwarewar komai, har gidan nan tazo kwanaki lokacin da hankali yazo mana
Tafad'i yanda tai, itama yanzu haka tazama bata magana
FUTUHATUL KHAIR ina k'aunarki, inafatan kinga ne ba laifin mu bane nak'in nemanki?
Hajiya Nagode sosai wallahi na yadda ke macece ta gari, bakisan ta ba ki d'auki nauyinta har kike mata komai duk da kinsan bakida tabbas na ganin iyayenta
Kinji abin da ya faru, tana magana tana share hawaye da majina, kowa kuka yake yana tsinewa Chuchu da Maman ta
Allahu Akhbar nan itama FUTHA da ita kanta Maman Fadeela suka bada labarin komai, waih ansha kuka duk da FUTHA batasha wahala ba Amma dai rashin iyaye kusa da ciwo
Bata fad'i rashin arxik'in da dangin Aunty Meimi suka mata ba
Sosai Abban ta yace insha Allah ya d'auki alk'awarin nemosu har ita Mama NAFEE sun taka rawar gani arayuwarta
Idan yai duba da yadda Kabeer da Meimi suka maida ta 'ya komai ita, to ai haka Mama Nafee itama tamaidata 'ya har school tasaka ta
Bata barunta tayi aiki, tana karemata mutuncinta, tana sonta duk da ba ita ta tsince ta ba
Mama kuma aisai godiya da fatan zumunci mai d'orewa, dan sunmata hallaci makaranta wadda ba 'yayan kowa suke ba ita suka sakata IMAN INTERNATIONAL SCHOOL lallai sunyi aiki
Kowa dai yayi k'ok'ari akan FUTUHATUL KHAIR. Murna bata k'arewa Abban ta murnarsa tafita kowa
Dangin Mamanta sunzo suma murna, daga kan Uncles da Aunties nata, sai yammata yaran Yayun Maman ta kamar su d'aya da yaran
Dama tanajin larabci nan fa hira t b'alle sama sukai FUTHA na kusa da Fadeela, komai Fadeela
Rayuwa tayiwa kowa dad'i, yanzu basuda matsala ta komai, sai wadda baza'a rasa ba

*Bayan Sati 3*
Farouq komai ya kwance masa abin tausayi, Fadeela kanta tana tausaya wa Broth nata, gashi anyi nemanta har cikin super market amma abin shiru
Addu'a ita yasaka agaba, Mama taji labari itama addu'a take masa Allah ya bayyanata idan da alkhairi
Yau Lagos suka tafi gidan Aunty Benaxir cousin na Abban tace, yankin Ikeja
Sunje lafiya kai garin Lagos yana kyau, sun sha yawo anje beach anje unguwanni da dama
Yau zasu tafi itada K'annen ta suka zo, sai wasu 'yan uwan su
Dan haka itace a gaban motor anata hira tana kyalkyala dariya kanta ta juyar tana kallon gari, batason hawa flight tace gari zata gani ko a tawowar su saida suka tsaya a Kaduna nan ma tazaga
Shikuma daidai lokacin fitowar sa kenan daga office zaije gida ya d'auko wasu files
Cikin nishad'i yake driver nasa hira yake masa, idonsa a rufe yana hango 'Yar Makaranta da yanayinta da yaga gani lokacin da suka had'u a shopping
Idonsa yake bud'e wa a hankali yana murmushi, gefen da zai kalla waih itace k'ara kalla yai wallahi itace da sauri yace driver yi sauri ka tsaya, ya zata tsayawa zasuyi amma ina saiyaga kamar ma qara speed yai na motor d'in
Da sauri ya shiga da kansa yake driving d'in ya kusa kamosu 🛣 traffic 🚦ta tsayar dama gashi sun shigo wajan cunkoso duk k'ok'arinsa nayai sauri ya wuce abin yaci tura
Sun wuce gashi shi mai adalci ne bayan haka ko da yazo wucewa motoci sunyi yawa
Kansa ya buga a sitiyari hawaye ya fitar mai zafi, office d'in da baikoma ba kenan yafara had'a kayansa ya tawo Sokoto

@ut@r h@jiy@💅🏻💁🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [03/11 10:17 am] @ut@r h@jj@ju👱🏻‍♀✍🏻💅🏻📚📝:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Page 121-125*
Chapter 17 · 0% Book details