← Book details Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko daya shiga d'akin sa brush yai, sannan yasaka boxer da singlet fara qal, system nasa ya janyo yafara bincike akan aikinsa
Stool ya janyo wanda ya d'ora mug na lemon Kan kana aciki yana aiki yana sha haka harya gama
Baisan ya shanyeba saidaya d'aga mug d'in yaji ba komai, dariya yaiwa kansa
Bashi ya tashi ba, sai wajan 1 na dare, bawa idan yagama aikin ba, a'a saidon wayar da Abbansa yasamasa
"hello" Abba lafiya da night haka?
"Eh naji ajikina bakayi bacci ba, so maza kayi bacci, kada aiki yasaka ka shiga bad conditions, bacci yanada nasa important en
So u better get rest plx Omar
" Insha Allah Abba yanzu zanyi
Yauwa Allah yaimaka albarka
Ameen Abba adduar ka garen tanada amfani, a kullum burina naji bakin ka nasamun albarka Allah ya k'ara girma yaja da ran ka
Ameen Omar Allah yabaka mace ta gari, yasaka maka da mafificin arziqi mai d'orewa da albarka
Ameen Ameen Ameen Abba, ayi bacci lafiya
Kit ya katse wayan, yana mai farin ciki
Toilet ya shiga, bai jima ba, ya fito sai gado, addu'a yai ya janyo bargo ya kashe light
A can Fadeela labarin santin lemon da Ya Farouq yai take bawa FUTHA, dariya tai a hakan dai take tayi magana ta kurame, tace Ya Farouq yanada kirki tunda yasha abin da nai
Huum harkin bashi lambar yabo, wallahi ba wani kirki gareshi ba da yawa ba
Kai ta kad'a kawai, a haka sukayi baccin su mai cike da farin ciki
Safiya nayi kafin Fadeela ta tashi hartayi wanka, ta taimaka wa Iya Ladi da aikin gida, kafin 7:30 tayi driver ya jata sai IMAN INTERNATIONAL SCHOOL inda nan aka maidata bayan dawowar ta gidan
Yanzu exam ba kama hannun Yaro ita take sun gama WAEC sauran NECO, lesson suke shiyasa taje
10:00 kowa ya fito cikin shirin sa, danyin break fast, Yam balls ne sai tea mai kayan qamshi da na'ana ga qamshin lemon grass dayake tashi, plantain a soye itama
Kowa zama yai, gaishe da Iyayen sukai, bayan nan Fadeela tayi saving nasu cikin plates
Madara ta d'akko da Milo ta ajiye kowa ya zuba dai dai shi
Harya janyo madara sai yaji bara dai yasha a haka, wow so sweet whts kind of tea na Mama do 4 us
Ba magana haka kowa ya sha batare da madara ba, a tare suka dire cup alhamdulillah wannan tea haka?
Nima abinda zance kenan, wallahi nidai ban tab'a shan shayi mai dad'i haka ba, Mama kina mana shi plx
To ba Mama tayi ba, FUTHA ce, dan ita ta Iya komai, kaci yam balls en nan kaji?
D'aya ya d'auka bakinsa yai, lumus aifa saida Abba ya riqe hannun sa yace kabarshi haka, bazakayimana irinta jiya ba, ka shanye duka lemon, yanzu ma Ka cinye yam balls d'in nan ba
Inasonsa FUTHA ta iya girki, tsayawa yai yace Abba wace FUTHA? new house gal ce ko kuwa
Amma koma mene ta iya girki, ace ina gaidata
Yana gama fada ya miqe bai saurari jin wace FUTHA ba
Kwanan sa goma agarin yanxu ma yana shirin tafiya wajan aiki, bai tab'a had'uwa da FUTHA ba, itama haka
Duk lokacin da zasu had'u sai wani sab'ani ya gifta, gashi girkin ta ya namasa dad'i, ya lura ta iya girki
Baitab'a neman taba, saboda a tunanin sa house gal, ce amma wataran Ji yake kamar yace a kirata yai mata kyauta
Amma baiyi hakan ba, Fadeela bata tab'a lura cewa basu had'u ba
4:00pm dai dai lokacin ne driver'n Farouq ne ke driving dan kaishi airport zai koma aiki ta Titin BYPASS suka biyo anan IMAN take school d'in su FUTHA
FUTUHATUL KHAIR ita alokacin suka fito tareda qawayenta STYLICH da PHARTY BB, tafita take tanata dariya saboda wata magana da sukai akan qawarsu NAFEE ANKER
Fuskanta smooth tana kyalli take washe baki ga school uniform d'in ya karb'eta
Shikuma daidai lokacin yasha kwana da fuskanta yafara arba Hasbunallahu wa ni'imar wakeel, Allah yayi hallita
Jiyai jikinsa ya tsaya cak, kafin ya farga ya nemeta ya rasa, ihu yasaka plx driver back back
Kayi sauri kada ta ba'ace haka yai gudu, yammatan yagani amma kamar ba ita?, hakan ce ta kasance dan babu ita
Zagaye wajan sukai amma ba ita
Haka ya qaraci duba dubensa ya ce a tafi fuskansa cikin yanayi na rashin dad'i

@ut@r h@jiy@👱🏻‍♀
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [30/10 8:42 am] @ut@r h@jiy@💅🏻💁🏻✍🏻💐:

*FUTUHATUL KHAIR*

______*®NWA*_______

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV &Anee Maman Ayman Aseef habeebaty ana bihibak bikil Hayatee*

*Page 96-100*

Shi kansa driver'n ya lura oga kamar yana d'an neman wani abu, gashi basu ganshi ba
Haka har suka isa airport ya direshi ya juya shi kuma ba wani jimawa jirgi yazo aka fara Shiga
FUTHA lokacin da suke hira adaidai nan driver ya qaraso d'aukanta shiga tai yai gaba, shine dalilin da yasaka baiganta kusa ba
Ko cikin jirgi dariyar ta yake hanga da siririyar wushiryarta mai ban sha'awa
Bayan kwana 2, yau gidan Aunty Zainab zasuje shiyasa ko Malam na islamiyya suka masa waya kada yazo, FUTHA ita tunda aka ambaci za'a gidan hankalinta ya tashi tarasa sukuni addu'a take yi azuciyarta kawai tasan duk tsanani itace maganin komai
Su Ahad da Waheed haka suka kasance suna zuwa wajan Malam addu'a kullum da saukar Al Qur'an ita ake, sai rubutu da ake yayyafawa cikin gidan
Alhamdulillah sunga sauyi dan sau dayawa damuwar da suke gani afuskan iyayen yanzu babu ita sosai
Kuma dukka pics na FUTHA da aka cire tun kafin Haihuwar su, sun d'akko sun goge sun maidasu kusa dana iyayen
Hajiyansa kanta yau sai gashi Allah yabata ikon cewa Bilkisu ta b'ace kenan babu maganar ta?
A daidai lokacin ne kuma, acan katsina gidan su na farko ana gyara Gidan aka tone wani qulli kamar bazasu bud'e ba masu aikin sai kawai sukai shahada, Innalillah wata laya qatuwa sai gashin akuya baqa kuma ga hayaqi daya fito addu'a suka fara anan wani yai shahada yasaka ashana ya k'one kayan
Sallah FUTHA keyi, bayan ta fito daga wanka ayi shirin tafiya gidan Aunte ZAINAB, fit taji ajikinta kamar fitar allura cikin tsoka taji zafi
Sai kanta daya juya, ahaka ta sulale ta fad'i awajan ba tareda sanin kowa na gidan ba
Fadeela akai sa'a ta shigo saiganin mace tayi yashe a k'asa ba alamar numfashi, kuka tasaka Mama kizo kiga FUTHA ta mutu wayyo Allah
Da gudu itada Abba suka haura upstairs girgizata sukai shiru, haka ya d'auketa sai Asibiti dan jin ko menene
Abdul Abdul BILKISU 'yata ina kaganta wayyo Baby were ar u?, kizo ga Mama
Nan da nan aka taru kowa kuma saiya fara tuna FUTHA, tana ina? basu sani ba shekara wajan 13 innalillah a ina zasu nemeta?
Me yasaka suka manta da sanyin Idaniyr su?, nan fa kowa yashiga tashin hankali baran pics nata da suka gani a parlour ma'aikatan gidan wajan Su 12 kowa jimami yafara
Ana maganar ne Hajiya da Aunty Meenah suka shigo suma ina FUTHA?, kururuwa aka fara ina zasu tarki nemanta?, kuma gurin wa?
Parlour suke tafiya saijin hayaniya sukai, ana dubawa CHUCHU ce ta shigo a hargitse, tana shikenan Bilkisu kin cuceni kin kassaramun rayuwa, wayace a tone wajan, boka yace bazata dawo ba, ta tafi kenan
Kutmar yau zanga shegen daya tone layar danasaka ita kuma tayi addu'a asirin jikinta ya karye
Zainab kin zama muguwa duk abinda nake saida kika tona, kai Mama kin cuceni, sumbatu kala kala
Kowa kuma ya fuskanci itace Ummul aba'isin saka FUTHA cikin bala'i tayi sanadiyyar rabata da mahaifar ta
Abdul ne kuka ya kwacemasa yace CHUCHU kin cuceni Allah ya isa tsakanina da ke, burinki ya cika ada, amma ko adan baiyi tasiri yanda kike so ba
Mari yafara bata yace ina takaimasa 'ya maqurar dataji yasa tace kayi haquri nayi dana sani, tana Niger nan nasaka aka kaita
Numeiy aka ajiye ta, aaaaà tana qoqarin magana amma takasa
Asirin ya koma kanta, tazama kurma sai kuka take dama ta yamushe tazama wata tsohuwa
Abba kuka Zainab dasu Hajiya kuka ina zasu fara nema?, Abban FUTHA shine yace ba jira aka hanya atafi Niger
Basuyi gaddama ba, Motoci aka d'iba aka tafi
Chapter 14 · 0% Book details