← Book details Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 24

Sashe 15

Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Likitoci ne kan FUTHA suna qoqarin daidaita numfashinta wanda ya d'auke Idan kuma ya dawo saiyafara sama hakan yasaka su b'ata lokaci akan ta
Fadeela ita hawaye takeyi, tace Mama lafiya nabarta tana Sallah to mene ya sameta? ba amsa
Alhamdulillah FUTHA ta farka da salati a bakinta, kama bakinta tai magana tafara a hankali nan taga maganar na fita, kabbara tai da qarfin gaske
Lallai dama tanada rabon qara magana Allah Hakeem
Mama ce tashigo, FUTHA kin tashi sannu, Yauwa Mama
Eye! FUTHA kekikayi magana!, nice Mama kabbara tafara da godiya ga Allah mai iyawa, ahaka Fadeela tazo ta same su
Tashi FUTHA tai ta rungume Fadeela tace Fadeela dama zan k'ara magana Fadeela ikon Allah ya sauka a kaina ina sallah najini wani iri kafin na farga Jikina yai weak bansan komai ba, sai yanzu dana ganni maybe nafad'i ne
Rungume juna sukai tanaimata murna, baki rahma ne, jin muryanta siririya mai dad'i saikace ana busa sarewa
Amma daga ji FUTHA ba real Hausa bace dan muryanta hausan bata fita sosai, koba komai jikin ta ya nuna itad'in wani yare ce
Allah cikin Ikonsa ya kaisu Niger lafiya, da pics nata suka fara bawa mutane ko sunsan wannan yarinyar tana qarama 13 years ago, babu wanda ya gane ta ko ya santa, harsun juya sai su kaga wani, nuna masa sukai
Yana gani yace kai ai yarinyar data cinyemun abinci ne a wannan garin
Nan yabasu labari, murna suka fara jin cewa yasan gidan mutumin daya d'auke ta dan shekara 4 ma sun had'u
Haka suka tafi garin Abalak, gidan yana nan, sai canje canje da aka samu
Tambaya sukai wani yace baisan taba, amma ga Gidan Alhaji Raheem suje
Sallama akayi dashi, baijima ba ya fito, gaisawa sukai sannan suka fara fadamasa abinda ke tafe da su
Allahu Akhbar Ikon Allah Allah mai axirtawa ashe yarinyar nan yar babban gida ce, har sun fara murna sai gani sukai yafara share hawaye
Nan ya zayyanemusu zaman datayi, kama daga zuwanta har ranar da suka tafi
Hajiya ce tace kenan sun tashi daga nan, Sokoto suka tafi, muma daga can muke
Ayya ai aranar 16-7-2013 sukabar garin nan aranar kuma Allah yai ikon sa akan hanyarsu mota tayi accident babu wanda ya shura acikin su
Gara kabeer an ganshi, ita gaba d'aya FUTHA qonewa tai ko gawarta ba'a samu ba
Tokarta da babban d'anyatsanta sune aka gani, akayiwa sallah aka bine
Mekkkkkk......kafin kace me ta tafi luuuuuuu mamanta ta fad'i

@ut@r h@jiy@👱🏻‍♀💅🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [31/10 3:48 pm] @ut@r h@jiy@💅🏻💁🏻✍🏻💐:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

~*page 101-105*~

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wannan wace irin rayuwa ce?
Daga wannan sai wannan, ruwa aka d'ebo aka zuba mata ajiyar zuciya ta sauke hawaye mai zafi shiya ciga ba da zuba a idaniyar ta
Yanzu kenan sunga samu sunga tashi, yarinyar ta ta mutu, batada rabon ganin ta
Kuka itama kanta Hajiya tayi, saboda ayanzu taji tana qara qaunar jikar ta
Basu zauna ba haka suka kamo hanya zuwa sokoto tunda basu samu abinda suka zo nema ba
A motor sai rarrashinta suke akan ta d'auki qaddara, Hajiya wallahi inaji ajikina BILKISU tana da rai, amma nabarwa Allah komai shi yafi ni sanin abinda ya b'oye akan ta
Yauwa haka suke tafiya ransu ba dad'i, Abba kansa daure wa yake, dan shi yafi qaunar Bilkisu akan sauran yaransa tun kafin ma samu yaran
A can murna dai FUTHA baki ya bud'e, takasa sarrafa murnarta sai dariya take, a haka suka tarkata sai gida
Hajiya Zainab taji d'aci da ciwo na mutuwar 'yar ta, haka ta kasance sukuku har bayan komawar su gida
A gidan Mama sunkasa zama daga suyi ta mata magana dan suji muryanta saisiyita waqoqi, Fadeela ita ganin abin take kamar cikin mafarki
Mama da kanta tarunga bugawa 'yan uwanta waya suna tayata murna, Sahaf itama saiga wayarta sun jima suna magana
Waya Fadeela ta d'auka tace Broth FUTHA bakin ta ya bud'e tana magana I'm really happy
Huum sisto wace FUTHA kindameni da ita?, komai na abinci ace itane tayi wace ita?
Yaya tsintar ta akayi fa, kuma tanada kirki gata kyakyawa kamar Balarabiya , maganarta kamar sarewa dan dad'i
Anya kuwa duk kyanta Bata kai 'yar makaranta ba, komai ita ta had'a, duk da kallo d'aya namata
Nan yabata labarin yarinyar, ayya broth zaka ganta insha Allah, ashe broth he fll n lv, lallai to Allah yasa aganta ko mayi biki agidan mu
Haka suka fara hira, ya manta yace abashi FUTHA su gaisa, duk da baisan taba
Tafiya dai tasha ruwa dan sun manta da wata Hajiya Zainab da gidanta da zasu, sai wajan 8 sannan FUTHA tace Mama anmanta da gidan qawarki
Wallahi kuwa aje wataran, Yau ai ranace mai tarihi da farin ciki a wajan mu
Amma FUTHA zaki Iya sanin sunan garinku da Abban ki?
Kai ta d'aga (kunsan dama harda mantau aka saka mata)(amma koda babu Mantau a shekarunta bazata iya fadar wani information Maikyau ba)
Mama nasan dai Baby Maman mu ke cewa, then a Katsina muke amma daga nan bansan komai akai ba
Mama na a Libiya take, muna zuwa, da Abuja wajan Aunty na
Yauwa to a katsina wacce unguwa Abban ki kuma ya sunan sa?Mama ke tambayar ta
Abba kawai ake cewa, haka dai sukaita tambayar ta ita kanta taso ta tuno wani abu amma ta kasa
Haka zamanta yaci gaba, HAJIYA Zainab taiwa Mama waya akan batada lafiya sun tafi garin su
Sosai ta jimantamata akan Allah yabata lafiya, bata fad'a mata cewar ga abinda yasameta ba
Saboda batason tunowa, yawan maganar shine yasamata ciwo, gashi jininta har yakai 200 abinda ba'aso kuma
Ya Farouq acan bashida tunani saina 'yar makaranta, har ya dawo yana tuna ta, wajan kwana 2 yana zuwa qofan school en amma Allah baisa ya ganta ba
Yau yana CBN qrts gidan su Leemcy wanta abokin sane, kamar ance d'aga kanka itace cikin motor suda Fadeela, motar bata Gidan su bace, ita yagani kad'ai ba Fadeela da gudu ya tashi,amma ina kan yaje sun qule
Abin tausayi ayanzu duk wanda yasanshi yasan yanada damuwa ko Mama tayi tambayar shiru
Yau wajan shopping yaje itama haka, lokacin ita tare suke da class mate nata, tunda sauran kwana 2 candy nasu shine aka zo siyayyan gift wanda zasu bawa teachers nasu
A wajan cashier suka had'u, matsawa yai kusa da ita, jikinsa har rawa yake ganinta da wata baqar abaya anyi rolling ga kanta yai tum, ga giranta baqa data qawatamata fuska
Yana qarasa wa har yace yammata........ sai qirr yaji Waya, kamar bazai d'aga ba, saboda yaga har anfara musu lissafi suna biyan bills
OMG ogansaneke kira da sauri ya d'aga dan yayi yayi yagama wayan ya juya
Saidaya qare sannan ya juya wayam, innalillah, dubawa yafara harda fita waje amma shiru ba ita ba labarinta
Hankalinsa ya tashi, sosai yafara tunanin kodai aljana take masa haka?, bashida answer
Mama ce Yau dai tasha alwashin lallai sai anje gidan Hajiya Zainab suyimata sannu da kuma gaisuwa had'e da jaje, Maigidan ta yagayamata komai
Haka kuwa duk suka shirya

@ut@r h@jiy@👱🏻‍♀💅🏻
[11/10, 8:26 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [01/11 6:09 am] @ut@r h@jiy@💅🏻💁🏻✍🏻💐:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*page 106-110*
Chapter 15 · 0% Book details