← Book details Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Futuhatul Khair Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tafiya tayi kyau anje lafiya andawo lafiya, sai fatan gajiya tabi lafiya
Shima Farouq yazo gida lafiya sumul, koda Mama ta ganshi tasan da matsala tunda ranar aiki ce
D'akin sa ta bari ya shiga, sannan ta bishi, yana kan sopa kansa yana kallon sama ya dafe kansa da hannun sa
Baiji shigowan ta ba sai jin hannun Mama yai akan fuskan sa
Son lafiya kana dawowa daga gaisuwa ko abinci baka ciba kazo ka fara tunani lafiya ko wajan aiki ne ko baka da lafiya?
Mik'ewa yayi yana cije baki saboda kansa daya ke d'an ciwo. Mama ba awajan aiki bane. "wallahi dai inajin Mama 'yar Makaranta aljana ce indai mun had'u to saita sub'ucemun, jiya a logas nagan ta duk k'ok'arin namata magana abin yaci tura"
Nakasa kuma cireta a idona, hmm Omar ba komai kuma insha Allah ba aljana bace, then kadena saka damuwa aranka Idan har matar kace wallahi saika aure ta kaji Omar Farouq d'ina gwarzo na jarumina amma awajan aiki banda wajan 'yar Makaranta
Dariya ce sosai ta kama shi, yauwa katashi kayi wanka sannan kayi sallah kaci abinci sai ayi addu'a kasa nima ko har gida zata zo kaganta
Murmushi yayi, sannan ya mik'e. Yadda Mama tace yayi haka yayi harda d'akko Qur'an yana karantawa
Mama daga nan sai wajan Fadeela jiya namata waya bata d'aga ba, nasan fushi tayi mun tafi, tunda nad'an huce gajiya Bara naje
Ai kuwa dai dan ranar da kuka tafi kamar tayi kuka, dan ma Ahmad yana nan shine fa sukaita hira harta ware
Naji yana magana ma wai yasami mata a 9ja, (Ahmad d'an wan Maman FUTUHATUL KHAIR ne)
Lallai Allah ya tabbatar nasan da batayi fushi ba, tuni tamun waya. Mama natafi dama already ashirye take driver ne ya fito da mota suka tafi
Salamu alaikum Sis Fadeela kaina bisa wuyana nasan nayi laifi, wallahi tafiyan da sauri tazo amma amun afuwa
Fitowa Fadeela tayi tana d'aure fuska tace ni ina ruwana, dama nasan haka zaki ce
Wallahi ba haka ba, to kiyi hak'uri na amsa laifina kinga Mama na kallon mu kada tamana dariya
Namayi dariyar, rungume juna sukai suna dariya,gaishe da Mama FUTHA tayi ta ajiye mata tsaraba. d'aki sukai sai hira, nan aka fara hiran Ahmad da soyayyan da suka fara itadai FUTHA dariya ce tata ita dai batason wata So ba, abinda sai yanzu tamasa mu bakin maganar
Kai namanta broth yana gida kuma baici komai ba, couscous mukayi na zuba masa amma yakasa ci, yanata tunanin 'yar Makaranta
Wace kuma 'yar Makaranta?, wa tace nan ta bata labarin tun farkon had'uwar su kawo jiya
OMG! Allah sarki Allah ya bayyana ta, amma zama bacin abinci da matsala
"Bara kiga namasa faten wake koda kunu ne mai zafi maybe ya iya ci
Haka ta mik'e sai kitchen, wake ta d'obo agyare yake saikayan lanbu da hanta na manja tamasa sannan ta kawo alayyahu mai yawa ta zuba
30 minutes tayi tagama, sai tashin k'amshi, kunu mai kayan k'amshi ga k'amshin lemon tsami haka ta juye tasaka a tray tace Fadeela tazo sukai masa
Lokacin da suka shiga yana toilet, ajiyewa sukai suka juya
Allah sarki Ya Farouq wallahi yaban tausayi, Allah yasa ya iya ci, Am33n Fadeela tace
Tun yana toilet yaji k'amshi yaji alamar shigowa sauri sauri yai ya fito
Gurin tray d'in yayi, wow abinda yace kenan, towel ne ajikin sa ko kaya bai tsaya sawa ba, yafara zirawa kafin me? Sai flask yabari kunun ya tsiyaya shima dad'i
Huum nasan FUTHA tayi shi dan wannan testing d'in food nata ne
Godiya yai ga Allah kafin ya tashi ya shirya, kayan ball yasaka mai tambarin Arsenal bayanta sunan Ozil ne. bayan gida yayi, anan yafara buga kwallonsa cikin kwarewa yana nishad'i haka yaji shi bayan yaci abinci yana murna
Kinga tashi muje wayan Ya Farouq ko yaci mu gani FUTHA tayi maganar, OK let's go
Shiga sukai, wayam yacinye farin ciki sukayi, uhhmmm inayatafi kuma?
Yana baya kwallo yake, zo muje yauwa kinsan kuwa munyi missing kwallo wallahi aitunda kika tafi banyi ba
Gurin suka mik'a aikam yana wajan kallon sa sukai kaikace Christiano Ronaldo yanda sukaga yana buga ta cikin kwarewa harda kai bugawa yake
FUTHA jitayi ya burgeta Bata tab'a ganin saba, amma Idan hakane yafi duk gidan kyau duk da ba fuskansa tagani bayan sa tagani, lokaci d'aya taji yanason tsayawa da saurayi kuma kalan ya Farouq
A Jikin sa yaji kamar ana kallon sa, da kuzarinsa ya juya cak ya tsaya ganin *'Yar Makaranta* agabansa tazubamasa ido

@ut@r h@jiy@💅🏻👱🏻‍♀
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [05/11 11:36 am] Last born👱🏻‍♀✍🏻💅🏻📚📝:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to Bilkisu Sidibe FUTHA LUV*

*Page 126-130*

Wata d'aya akasaka badan komai ba sai don haka suke so, dama maiyayi saura indai mutum nada saurayi zaman zance duk rage lokaci ne
Maman ta bataso haka ba, taso asaka ko irin 3 months d'in nan batagaji daganin 'yarta ba, amma ba halin magana saidai fatan ayi komai cikin aminci
Lokaci na tafiya shikuma alokacin ne aiki yayi masa yawa kansa ta d'auki charge saboda sun gano ana shigo da miyagun abubuwa ta b'arauniyar hanya kuma da sanin staff na wajan
Shiyasa yake k'ok'arin gane su waye sukeda hannu ciki, shinkafa ce Sai carton na Taliya aka shigo dasu daga Niger cikin su kaf bindogogine sai abubuwan banza
Lokacin sa kad'an ne wayama sai dare suke samun yi, da rana baifi suyi 20 minutes ba suna magana
FUTHA an fad'a tarkon Luv kullum cikin tsara sweetest words akeyi agayawa Ya Farouq, ga kwalliya da ake ci asha Selfie
One love plx ai kasan Maiduguri koh?, eh mana ya akayi?
Dama inaso kafin biki naje gidan su Aunty Meimi suma agaya musu daga nan sai sumana kwatancen gidan su Abba Kabeer
Hum waye Abba Kabeer kuma ni bansan shiba kuma ba inda zaki tafiya har wani gari
A'a kada muyi haka da kai, banda kamar iyayena sai Abba Kabeer sai yanzu danasami miji nagari
Kada ka hanani zuwa sune jigon rayuwata sune suka ban tarbiyya sune suka koyan girki sukaban ilimin boko both of islamic
Nan tabashi labarin ta kaf, tunda Fadeela data bashi labarin baiji sosai ba
Nan da nan yace yi shiru to kidena kukan, yi hak'uri kifara shiri gobe zanzo sai mutafi shikenan
Adena mun asaran hawaye, da ina nan saina shanye kayana amma tunda bana nan ayi shiru
Dariya tai tace Allah daga gani kullu zakayi, ko fita kaji nayi kafara fad'a kenan
To ai ina Kishin ki da yawa bakisan kinada qualities da ko wanne namiji ya kalleki bazai so ya d'auke Idon saba
To naji kayi shiru, hhhhh to nayi tunda ankatseni, yammata na
Haka sukai sallama daga nan tayiwa Fadeela da Sahaf sai Basmah yar lele aminiyarta ce sun had'u a school itama Abban ta former Senate ne, tanada kirki Basmah tana sonta shiyasa itama takeji da ita
Tare tayimusu waya akan su shirya za'a Maiduguri gidan su Aunty Meimi dayake batamanta sunan Abban Aunty Meimi ba kuma yayi fice koda sun b'ata daga an fad'i sunan za'a nuna musu
Mamanta tayiwa bayani sosai tayi murna tana alfahari da FUTUHATUL KHAIR yarinyace mai dogon nazari da sanin yakamata
K'arfe 11 na dare yadira agarin na Sokoto duk da tarin ayyukan daya ke dashi haka ya tsallake ya bari dan bin umarnin Amarya
Waya yamata ya dira yace tayi k'ok'ari su shirya before 8am dan suje da wuri,Fadeela zaiyi k'ok'arin itama ta shirya tunda yaga tana gida Basmah da Sahaf agidan suka kwana Fadeela ce take a gida
Abban ta kaya super guda 10, less da Swiss ga shadda da takalma ga dangin kayan zak'i haka ya siyo yace akaimusu kafin shima Allah yabashi lokaci yaje
Kayan gida biyu aka raba.d'aya dangin Meimi d'aya na Abba Kabeer, amma duk da haka saida Farouq yaqara loda wasu kayan
Ita Permpers da kayan yara wajan 20 colours ta siya Mamanta tabata kud'in ga su abincin baby haka ta siya wa Babyn tasan ya girma
Komai cikin tsari sukayi, Safiya nayi suka kama hanya, shida ita agaba su Fadeela agaba tafiya mai dad'i sunayi suna hiran su da murmushi kai gaskiya SO yayi
Suma su Sahaf kowacce hiranta take danata saurayin daga baya aka koma chat
Sudai hiran su suke yi yanayi yana juyowa wani lokacin hannu zata saka ta juyar da kansa daga kallon ta
Dariya ce tasa hararen sa tayi, wow amma kinyi kyau kamar hararan tafi miki kyau k'ara muga one love
Nak'i nak'ara to naji yimun labari ko kimun wak'a plx
Ganin ba zatayi ba yace Idan bakiyi ba zan aje driving harsai kinsa yi oya fara inaji
Huum ba yadda tai dadin ta d'aya sunyi bacci haka tafara masa wak'an larabawa tasu Maryam Haddad, Hanadi Khameel Farha yousef Salma Rasheed wow mirya mai dad'i yauwa cigaba haka tayitaimasa
Daga nan tafara masa na India haka tacigaba kafin me saiganin su sukai a round na Maiduguri sun iso

@ut@r h@jiy@💅🏻👸🏻
[11/10, 8:27 PM] ‪+234 809 308 3613‬: [07/11 3:43 pm] @ut@r h@jiy@✍🏻💅🏻:

*FUTUHATUL KHAIR*

*®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Dedicated to FUTHA LUV*

*Page 131-135*
Chapter 18 · 0% Book details