← Book details Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗan yi murmushin takaici sannan ta ce wannan damuwarka ce nidai bana sonka." Da sauri ya dubeta ta ce Yes,da na soka lokacin bansan menene so ba bansan ƙwalitis ɗin maza ba, yanzun na gane kai ba irin wanda nike so bane." Ido ya tsura mata, maganar ta ta taɓa shi sosai yasa hannu ya shafi fuskarshi sannan ya fesar da wani zazzafan huci, ya dubeta yanzu ya ya zakiyi dani? cikin sanyin murya ya yi maganar. Ta ce "inka gaji ka sake ni ba."

Ya yi murmushi ki sake sabon tunani, domin babu saki cikin auranmu. Ya take yazo gabanta yasa hannunshi ya ɗago fuskarta dube ni nan Pretty ya kausasa murya,sau uku a jere ina zuwa ƙasa mai tsarki ina rungumi ka'aba ɗakin Allah ina hawaye ina Allah ka bani Ruƙayya, Ruƙayya, Ruƙayya nake faɗi, sannan ya bani inyi wasa dake? Sorry ai mutu ka raba ni dake Pretty zan koma wannan shekarar ni dake inyi ɗawafi in kuma rungume ka'aba in gode ma Allah."

Ya saki fuskata ki shirya da ƙyau Sabi'u zai kawo miki kayan da zakiyi amfani dasu gurin dinner ina son a haska min ke yau gidajen T.V na duniya su san nine mijin." Ya juya ya tafi ta ɗaga murya.

"Ba inda zan je don kaji."bai ko juyo ba ya tafi ranshi na suya wai shi Pretty ta ce bata so. Gudun kada abokanshi su gane yasa ya saki jikinshi tamkar baya cikin damuwa.

Ta nufi gida rai ɓace, Yaya Murja ta ce "Haka ki kaje musu turɓunɓun ba ƙyan gani? Fati ta ce ai Ruƙayya har ma da iskanci ke in Dady bai ƙiki ba ai ko bazaki gujeshi ba duk da yana namiji yafi ki komai, ta ce ni ina ruwana da ƙyan shi Ni bana son shi. Amina ta ce munafuka bari ta shige gidan shiru zakuji ta." Ta ce Allah ya kiyaye,nan dai sukayi ta tsokanar ta.

An dawo sallar magriba Affa ya ce kai kowa ta tafi gidanta, Ruƙayya ta soma musu dariya. Suka ce kema ai tazo kanki yarinya." Ta ce "eh dai ai ba yau ba." Dady ya kira Amina........

🖊️🖊️🖊️
[8/13, 08:28] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Page 5

Ya ce ga direba nan da saƙo, don Allah dinner anjima ya kira su Murja da Fati ya ce su gyara mishi ita,gurin Amina ya amshi lambobinsu. Nan suka kira mazajen su suka ce zasu dinner tamkar haɗin baki kowa ya ce zai zo ya kai matarsa. Wani shegen leshi ne mara nauyi da kuma takalmi da jaka sai gyale ashe ba kayan tafiyar bane, sai da ƴan'uwan suka matsa mata ta shirya. Sabi'u ne ya ɗauke ta su kuma mazajensu ne suka ɗauke su sai gurin dinner wadda aka shirya ta a command sai ka nuna kati.

Sabi'u ya kawo musu katin amma amarya gidan Momy ta ga an nufa da ita duk da cewa dare ne ta gane layin, ta ce da direba yaya kayo nan da ni? Ya ce haka aka ce min." Tayi shiru ta bishi da ido.

*** *** ***

Gidan su Dady tamkar yau ne bikin farko ganin jama'a ta rufe fuska, tana zaune cikin mota. Sabi'u ya kira Ƴallaɓai, ya gata nan, takaici ya cika Ruƙayya. Dady yazo Sabi'u ya fito ya buɗe motar ya shiga jikinshi sanye da suit baƙaƙe. Duk ta cikin gyale take kallonshi ya yi matuƙar ƙyau, fuskarshi babu walwala ya ce "kin iso Prettyna? Yanzun zaki shiga Momy ta shirya ki." Ta dube shi baki buɗe.

"Bana shirya ba." Ya ce bazaki gane ba,zo muje ya jawo hannunta ta fisge, ta ce nifa bazan shiga ba, ya ce to shikenan ya ciro waya ya kira Momy ya ce "kizo ki fito da ita Momy wai kunya take ji." Ta harareshi na ce maka? Sai ko ga Momy har ma da wasu aminanta waɗanda suka ƙoshi.

Ruƙayya mai sa'a tunda yawanci sun so ya auri ƴaƴansu ya ƙi.

Cikin farin ciki Momy ta fito da Ruƙayya ta rungume ta suka yi cikin gida,sai ɓoye fuskarta take yi, wani ɗaki aka kaita wasu mata suka soma shiryata cikin kayan aure irin na arna, ranta ya ɓaci sam bazata iya shiga jama'a da wannan kayan ba, sai da suka kira Momy sannan ta ce Kiyi haƙuri ƴan awoyi ne. Wasu ne suka shirya muku kin ji? Haka ta haƙura aka sa mata riga doguwa mara hannu sai safar hannu tare da na kai shine ma ya rufe kafaɗun ta dogon farin takalmi suka fente mata fuska tare da gyara mata gashi.

Da ta dubi madubi sai da gabanta ya faɗi bata san ita ɗin ba ce ba ita bace. Momy da ƙawayenta sun yaba da ƙyaun da tayi, shi ko Dady sai ya ji tamkar ya ce a fasa zuwa don kar mutane su gane mishi mata. Suka shiga bayan mota aka ja su yayin da sauran motocin suke take musu baya fuskarta babu walwala ta ɗan kallo gefenshi ta ce ai wannan ɗabi'un arna ne, ya ce inji wa kice dai ba al'adar Hausawa ba ce ko larabawa suna sawa,nima ba son raina bane wasu Abokaina ne suka shirya mana har kayan sune suka kawo ta taɓe baki.

Gurin tamƙam sanda suka iso, suna fitowa haske kawai kake gani hotuna ko ta ina, gidajen T.V da masu ɗauka cikin waya. Hannu ya riƙe mata suna tafiya har kujerar da aka tanadar musu, guda ɗaya ce mai ɗan faɗi, suka zauna matsi juna mutane na ƙasa su suna sama P square ne suke waƙa a gurin anyi raye-raye. Kuɗi ake zubawa kamar ƙasa in anzo rawa Dady sai ya janyo ta jikinshi sannan suke rawar.

Haka gurin ya kasance,keck sai da ya ƙwanto da ita a kafaɗunshi sannan yasa mata a baki, haka da zai bata juice wai don mai gabatarwa ya ce ya nuna zai ci da ita, ita kam ɗan russunawa tayi da zata bashi dan bazata iya wannan abin ba, haka da za'a yi musu hoto gaban keck ɗin rungume ta ya yi tsaf. Suka koma suka zauna sannan aka soma ciye-ciye ta tuna da aminanta Armaya'u da M Bash tasan zasu yi fushi da ita in suka ji wai tayi aure duk da ita ma batasan da auran ba.

*** *** ***
Ɗaya saura aka tashi tana son taga ƴan'uwanta ina, waɗannan ai sun yi bacci ma a gidajensu, tunda suka ga abin bana ƙare bane suka tafi. Mun fito muna shiga mota ya dubeni da murmushi na ce "Allah ɗazun dan naga mutane ne shiyasa har na bada kai, ya ce na dai gode.

A gidan su Momy ban zauna ba kaya na canza na ce ni gida zanje Momy ta ce na ƙwana,na ce a'a dole Dady da wasu Abokanshi suka kaini. Sai da suka buga gida sannan aka buɗe musu ina ji Affa ya ce "lafiya cikin daren nan?" Suka ce Ruƙayya muka rako. Affa ya ce "Shirmen banza can ɗin baƙon guri ne da bata ƙwana?" Dady ya ce Momy tayi ta yi taƙi yarda.

Ita dai ta shige sai ɗaki ta cire kaya tasa rigar bacci doguwa ta kitse gashinta kitso ɗaya,ta faɗa gado. Komai haka yake dawo mata tamkar yanzun yake faruwa,ita ce ƙwance a jikin Dady wai mijinta? Ta mirgina ta rungume filo har Yanzun ƙamshin turaren Dady jikinta keyi,ƙamshin da shi kaɗai ta sani dashi tana son Dady shima tasan yanzun yana can yana tunaninta.

Wata zuciyar ta ce kodai yana can tare da matarshi, gabanta ya faɗi haka nema,yana can tare da matarshi yana gaya mata daɗaɗan kalamai,kishi ya turnuƙe ta, Dady yaci amanar son da yake mata, can ta tashi ta ɗauko wayarta bari ta kira wani yaji yanda ake ciki.

Tayi ringing sau biyu yana yankewa ana uku ya ɗauka cikin yanayin bacci yake magana...... Prettyna lafiya na neme ki ban same ki ba? Ta ce kai dai bari wai kasan menene? Ya ce a'a, ta ce aure.........bata ƙarasa ba taji ɗif ta gurin shi ashe shi da chaji ne,ta neme shi ta gaji.

Zuwa can wayar ta soma ringing a zaton ta Nuraddeen ne don haka ko number bata tsaya dubawa ba ta ɗauka tace Nuri kana jina? Gaban Dady ya faɗi, ya ce Pretty wanene Nuri? Itama gabanta ya faɗi ta ce kai mai maganar wanene? Ya ce ki dai yi hankali yanzu ke matar aure ce, shiyasa nike ta neman number ɗin ki ana ce min Number busy ashe kina ta hira da wani ƙato ko? Ta ce kaima kayi da matar ka kada ka dameni, ya ce ki iya da harshen ki kuma ni ina da izinin hira da matata amma ke baki da wannan damar ki kiyaye ina da kishi bana wasa ba. Ya kashe wayar ya jefar da ita can gefe yarinyar nan fa yaga kamar bata son shi da gaske,kai ko bata son shi zai zauna da ita koda zata rinƙa yankar naman jikinshi kullum. Alwala ya yi ya soma gayawa Allah.

Saɓanin ita data shiga kuka rurus wai ita Dady yake gaya ma yana da damar hira da wata mata? To zata nuna mishi mata suna suka tara.

*** *** ***

Da safe sai ga Sabi'u niƙi-niƙi da kayan tea, Ruƙayya suna zaune ɗakin Umma har da Affa ta ce Affa yau zan koma tunda yau Lahadi, gobe ina da aiki." Ya ce "wannan ke da mijinki,ni menene nawa?,ni da zai zo ma yau ki tare gidan shi ai da yafi min." Na ce "Affa ai min agaji in ƙarasa." Ya ce "To ai yarda da haƙuri yana gurin mijin naki ko? Ta ce"shikenan."

Misalin ƙarfe sha ɗaya ta gama kimtsawa ta ce bari inje gidan Amina. Umma ta ce kin sanar da mijinki? Babu ruwa na fa. Ran Ruƙayya ya ɓaci ta koma ɗaki ita dai bazata kirashi ta tambaye shi ba sai dai kar da taje.
Chapter 9 · 0% Book details