← Book details Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 21

Sashe 19

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zaro idanu tare da faɗin "haba Dady wannan sharrin daga ina?" Ya ko ɗaga hannu ya wanke ta da mari ji kake tau, ta firgice ta riƙe gurin,Ni ka duka bada haƙƙina ba Dady? Ya ce na mare ki in kika ƙara magana kuma sai na zane ki.. kuka ta cigaba da yi,shi ko faɗi yake shawara ɗaya zan baki kiyi gaggawar zuwa gurin da aka yi sihirin a karya shi tun kafin in yanke hukuncin daya dace a kanki shikenan don Allah ya jarabce ni da sonki, shikenan sai ki maidani ɗan iska, yasa kai ya fita.

Taci kuka har ta gode Allah jikinta ya É—au zafi kafin wayewar gari ta galabaita amma duk da haka ta yanke shawarar tafiya Kaduna. Ta haÉ—a kayan da zata iya É—auka ko wanka batayi ba,ta zura silifas tana fitowa direba ya taso Madam ina zaki je ne? Ta ce a'a ba nisa zanyi ba, ta fita tayi tafiya mai nisa sannan ta samu mota shata ta É—auke ta suka tafi, tasha ta kaita ta shiga motar Kaduna.

Kamar taje gidansu amma sai ta tuna yasan zata ci ƙaniyarta gurin Affansu don haka sai ta wuce gidan su sashen su Momy ta shiga Momy ɗin bata nan ta zube kayan tayi ƙwanciyarta.

Momy ta shigo da jaka ta soma cin karo ta dubi gadonta, Ruƙayya ta gani ƙudundune tana rawar sanyi da sauri ta nufi gadon, Ruƙayya lafiya? Ta buɗe ta a wuyanta tasa hannu zafi taji mai tsanani, ta ce innalillahi keda wa kika zo? Duk ta ruɗe cikin ruɗu ta ɗauki waya ta kira likitansu.

Ya ce gashi nan zuwa ta koma gurin Ruƙayya ta ce keda Dady ɗin ku ka zo? Hannu ta girgiza alamun a'a ita kaɗai ta zo. Abin ya ɗaure kan Momy ta ce yasan baki da lafiya ya barki kika taho? Likitan ne ya yi ma Momy waya cewa ya iso........

🖊️🖊️🖊️
[9/1, 13:10] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Page 9

Ya jima yana mata aune-aune tare da tambayoyi,ya tambayi Al'adar ta,ta bashi amsa tunda ta tare bata taɓa yi ba,don dama tana daɗewa batayi ba, ya ce ma Momy yana son fitsarinta, bayan ta shiga toilet tayo Momy ta kawo mishi sannan ya ɗibi jini, Momy ta ce wannan kumburin na fuskarta fa? Likita ya yi nazarin fuskar sannan ya ce ma Momy Hajiya wannan ba mari ba ne? Ya cigaba wannan babu damuwa mari ne da kuma kuka zai washe,kan Momy ya ɗaure ta maimaita a ranta mari? Yana tafiya Momy ta soma tuhumar ta akan batun mari gaske ne ko ko faɗin likita ne?

Hawaye ya soma bin kumatun Ruƙayya ta ce a'a ba mari bane, Momy tayi ta yi amma Ruƙayya ta ce ba rigima sukayi ba,ta ce to ina direban da kika zo dashi? Ta ce a'a ita kaɗai tazo a motar haya, ta koma ta ƙwanta jikinta na cigaba da rawa, Momy ta ce gashi bai bada magani ba ya ce sai ya dawo zai je yayo test ta kawo mata tea mai kauri,ta ɗan sha Momy ta kira wayar Dady, ya ce Momyna ina shirin kiranki ki ka kirani yi haƙuri yau duk ban kira ku ba.

Ta ce kaini ba wannan ba me yasa ka turo Ruƙayya babu lafiya kuma a motar haya? Zumbur ya miƙe daga kan kujerar shi tuni rannan nashi ya soma zugi a ranshi ya ce motar haya? Babu izni lallai kuwa, amma ya yi ƙoƙari ya ce tanace sai tazo Momy, direban su ya fita Ni ku Sabi'u zai kaini ofis,ta ce wannan ba dalili bane me yasa tunda kasan bata lafiya baka tuƙa kanka Sabi'u ya kawo ta ba,ta numfasa aƙwai abinda ya faru kuke ɓoye min kai da ita domin likita ya ce mari ne yasa fuskarta ta kumbura.

Ni ba mahaukaciya ba ce Dady yanda nasan ka keson Ruƙayya in ba akwai wani abu ba da zaka bar komai ne kuzo tare, amma koma menene ku kuka sani, tunda kunƙi faɗa, ta kashe wayar ta tazo gaban Ruƙayya tana faɗin ke mace ce ke zai ƙwara gara ma ki...... Aman da ya taso ma Ruƙayya shi ne yasa Momy saurin tare ta tare da yin shiru da ƙyar suka isa toilet ta dinga ƙwarara amai tamkar zata amayar da ƴan hanjinta. Hankalin Momy ya yi matukar ttashi ta kuma kiran likitan ta shaida mishi ya ce yana nan zuwa so yake sai ya gama test.

Kafin wani lokaci ta galabaita,tuni numfashinta ya soma ɗaukewa, to amai ya yi yawa ga cikinta bata ci komai ba. Tsoro ya cika Momy ta yiwa likitan waya ya kai sau shida, sannan ya iso gudu-gudu bayan ceto numfashinta sannan yasa mata ruwa tare da allurai cikin ruwan nan da nan ta samu bacci, likita ya miƙa ma Momy takardun yana murmushi ya ce Hajiya ga sakamakon test ɗin yarinya tana da juna biyu.

Da sauri Momy ta miƙe da gaske Doctor? Likitan ya ce tabbas ga shaida nan cikin takardu, alhmdllh ita ce kalmar da Momy take ta faɗi tare da yiwa likitan godiya, bayan tafiyarshi Momy ta je ta zauna kusa da Ruƙayya tana shafa gefen fuskar Ruƙayyan hawayen farin ciki suka zo mata shekaru sama da talatin da biyar basu ji kukan ƙaramin yaro a gidan su ba sai dai na jama'a in sun zo. Wani sabon son Ruƙayya ya ƙara shigar ta, Allah ka bamu masu albarka, ta furta tare da miƙewa, wayarta ta ɗauka ta kira maigidan, ya ce yaya dai Madam? Ta ce goron albishir nake son ka bani, ya ce goro? Ta ce yes,ina sauraren ka. Ya ce to na baki duk abin da kika zaɓa don nasan baki albishirin banza, ta ce ƴarmu Ruƙayya mata Son ɗin ka tana da ciki yanzun haka gata nan, ya ce Alhamdulillahi gani nan zuwa.

Kafin yazo sai da ya kira Son É—in nashi yana murna da faÉ—in congrats My Son ina farin ciki tamkar ranar da likita ya sanar dani cikin ka, Allah ya bamu masu albarka ya kashe wayar.

Dady ya ɗaure haƙiƙa ƙila gatse yake mishi mahaifin nashi,yana nufin ya yiwa Ruƙayya wulaƙanci ba haka ba murnar me zaiyi mishi? Nan ya samu kanshi da tunanin ya ƙyauta mata kuwa? Can kuma wata zuciyar ta ce ita ta ƙyauta maka kenan da tayi sanadin sunnar ma'aiki, ya miƙe yana shirin fita a ranshi yana raya zai matsa sai ta faɗi gurin da taje ta yo asirin nan dan ma ita ce taci albarkacin so.

Bai samu jirgi ba dole Sabi'u ya jashi a mota, sun isa Kaduna ana magriba, don haka shima masallaci ya wuce, yana dawowa gurinsu,sai dai ba kowa, duk suna bedroom É—in Momy can ya tadda Pretty É—in shi tana ta bacci su kuma Momy da Hajja da tazo dubata suna cin abinci.

Ya shiga da sallama yana raba ido suka amsa idonshi ya sauka kanta tana ƙwance da sauri ya isa gurinta a ruɗe ganin ana yi mata ƙarin ruwa gashi ta rame tamkar ta daɗe tana ciwo ya zauna yana shafa fuskarta, Momy haka Pretty tasha wahala? Tana murmushi ta ce kai kayi wauta sannan kana cewa tasha wahala? Bayan kai kasa ta biyo motar haya,suma ta dinga yi min ɗazun, ya ce suma Momy cikin tsoro, ta ce ƙwarai kuwa,ai tunda likita ya yi mata allura shikenan tayi bacci ta tashi ɗazun ta kuma komawa gata dai har Yanzun ya dubi Dad ya ce Dad Allah ya soni da Pretty ta rasu ya zanyi?.

Hajja ta ce ba gani ba inta rasu, ya ce a'a bafa zan iya da tsuhuwa ba, Momy ta ce ai da tsohuwar zuma ake magani, ya ce a'a yanzun an daina sai sabuwa farar saƙa,duk suka saka dariya ya ce Momy me likitan ya ce game da jikin nata? Dad ya soma murmushi dama Momyn taka bata sanar maka ba na kira ka ina taya ka murnar zan samu jika,ya tsura mishi ido, Dad da gaske kana nufin Pretty tana da ciki? Momy ta ce ƙwarai ƙyautar da Ubangiji ya yi maka kenan kana wasa da ita ka barta ta kamo hanya cikin murna ya cicciɓeta tana bacci cikin firgici ta farka tana yunƙurin amai, Momy ta ce ai gashi nan zaka taso aman.

Nan ko ta soma sharara shi har shi sai da shi kanshi ya tsorata likitan dai aka kuma kira yazo ya ce bebyn nan yana wahalar da Maman shi, Dady ya ce Dakta ya ya za'ayi ta daina wannan aman ne? Doctor ya can wannan kam sai dai haƙuri dan bazai dena ba har sai cikin yayi ƙwari sosai sai dai muyi ta sa mata ruwa kawai.

Bayan likitan ya maida mata ruwan tare da wasu allurai ta koma baccinta, Dady hankalinshi ya tashi su Momy da Hajja suka dinga ƙwantar mai da hankali, Dad ya tafi maida tsohuwa gida, Hajja ta tafi tana mai tausayin Ruƙayya shi kam Dady ya ƙe ƙashe ƙasa ya ce nan zai ƙwana dole Momy ta tafi saman Dad.

Ciwo ance in yaji dare domin a wannan daren har wasiyya Ruƙayya ta soma bari inda take cewa ya yafe mata kuma yasa su Affa da Umma da Yayyanta su yafe mata,ba shiri Dady ya yi ma su Momy waya ya ce suzo Pretty zata mutu,suna zuwa suka sare, domin lokacin da suka zo jikin nata ya yi tsanani tana ta neman gafara sumanta biyu,ruɗewa ta ƙarshe Dady ya yi,kiran sallar farko suka nufi asibiti inda yace da likitan shi dai kam ya haƙura da cikin da ƙyar su Momy suka shawo kanshi ya haƙura aka bar cikin,satin ta ɗaya a asibiti taɗan samu ƙwarin jiki bata cin komai sai tuwon Hajja da miyar yakuwa kullum sai an yo yaje ya amso su Affa da Umma da sauran Yayyanta kuwa kullum sai sun zo Dady ne me gaya musu ina da ciki ne duk abokanshi sun sani kai har Armaya'u da Sadiya duk ya yaɗani don haka kullum cikin ƴan dubiya muke,an sallameni kamar yau washegari ya koma.
Chapter 19 · 0% Book details