← Book details Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 21

Sashe 17

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka sabon kishin sa ne yake cin Pretty É—in tashi ko yaya taga matan turawan nan suna kallonshi tamkar zasu haÉ—iye. Haka nan shima bai cika son maza na kallonta ba.

Daga sati biyun da suka ce zasuyi sai da suka yi sati biyar dan ma Dad yanata waya, My Son ka dawo kan harkokin ka fa,ga kuma Zainab da duk sanda ya kirata ta dinga kuka kenan,wai ita ta gaji da rashin shi,da yaga shi yanada wata ita fa? Yasan tanada shegiyar jaraba ya ce bari ya tausaya mata su dawo. Sun yo tsaraba harda ta tsiya, shi dai Dady yawancin nashi duk kayan beby ne duk da baiga cikin ba yana sa ran samu tunda yasan lafiyar shi qalau,sai na Zainab da su Momy ta matsa mishi yayi musu tashi duk da ya bata iyayen kuÉ—i tayi ta ta.

A gajiye suka iso gida gurin ƙarfe biyu dan sun ƙwana a Legos sannan suka biyo jirgin Kaduna. Zainab ta taresu babu yabo ba fallasa,sun gaisa da Ruƙayya sai dai ta firgita da ƙyan da Ruƙayya tayi. Hatta muryarta ta ƙara zaƙi da sanyi ta ɗaure tasa Sunday ya shirya musu abinci duk tana yi ne bisa umarnin bokansu da ya ce kada ta tare su da tashin hankali ya ce cikin lalama zata shanmace su ta tarwatsa su ta hanyar saka musu sihirin cikin abinci ko abin sha wanda ake buƙatar su ci su biyun a lokaci ɗaya. Taso ta haɗa baki da Sunday sai dai tasan cewa Sunday ba zai taɓa yarda da buƙatar ta ba, amma ko a shegen Hollandian nasu zata zuba musu su sha suyi ta zabga faɗa kamar yanda Boka ya yi ma Hajiya bayani.

Ƙwanansu uku da dawowa suka nufi Kaduna sun cika dangi da tsaraba kowa sai tsiya ake ma Ruƙayya wai ko an samo ne ganin yanda tai ƙyau ƙwana ɗaya suka dawo.

A hanya ne Momy tayi ma Dady waya take tuhumar shi anya Pretty ɗin tashi batada ciki kuwa? Ya ce har yanzu indai ba ɓoye min take ba, bayan sun gama wayar yake ce mata Pretty me yasa kowa ya ganki sai ya yi min zancen ciki? Ko dai gaske ne?" Ta ce haba dai da baka sani ba? Allah bani da komai nima haka suke ta damuna, ya ce Allah ya amsa bakinsu, ta yi shiru tana murmushi.

Gidan Munira M Bash ma da taje, Munira ta ce Allah kinada shigar ciki dubi yanda ƙirjinki ya cika dam. Ruƙayya ta musa, M Bash ta ce yaushe ki kayi al'adar ki ta ƙarshe?.

Ruƙayya ta ce "aini tunda nayi aure,ko ince tunda na tare banyi al'ada ba,kin san tunda na samu sauƙin al'ada na dena ciwon cikin nan to sai inyi wata uku biyu banyi ba, Munira ta ce ƙila ma ya shige baki sani ba, ta ce a'a M Bash da naji canji a jikina haka Munira ta haƙura ba don ta yarda ba.

Zainab taso sa musu magani cikin abinci ko Hollandia amma Sunday ya bi ya kanainaye komai tare da sa ido kamar yasan me take son yi. Zaman gidan Dady babu yabo babu fallasa, shima kamar ya É—an soma jin daÉ—in zaman nasu tunda yanzun Zee ta É—an rage matsala kaÉ—an,satin su biyu da dawowa daga tafiya Zainab ta ce mishi zasu je garin su Hajiyanta.

Dady be musa ya ce sati nawa zakuyi? Ta ce ba zamu fi ƙwana uku ba, ya ce maimakon kuyi koda sati ɗaya, haushi ya kamata ta ce don ka gaji da ganina komin kora da hali? Ya ce a'a naga ƙwana uku yaushe aka gaisa da dangi? Ya cika ta da kuɗi ga waɗanda ta sata,har ƙofar ɗakin Ruƙayya taje tai mata sallama, Ruƙayya ko har ƙasa ta rakata inda direba zai ɗauke ta zuwa gidansu, tunda da Hajiyarta zasuyi tafiyar,ta shiga motar tana faɗin zaki ci mai garin garinku wannan tafiyar dan ke zanyi ta da bebyn naki,dama kun ishi mutane da beby beby, zan gyara muku zama a ranta take saƙa wannan abun,sun isa suka tadda Hajiyarta har ta shirya don haka ta sauka motar mijinta ta shiga gida, suka rankaya. Bala direban Hajiya shi ne ya jasu suka ɗauki hanyar Minna.

Zahiri ba garin su Hajiya zasu ba,gurin Boka kanfa suka nufa, domin ta kasa amfani da maganin.

*** *** ***

Bayan zuwan su Minna sun ɗauki hanyar Bidda. Suka yanke suka shiga cikin wani ƙursumin daji sun wuce ƙauyuka da yawa har duhun dare ya soma shigowa kafin suka zo wani bakin rafi Zainab ta dubi Hajiya ta ce "Hajiya ba dai ruwan nan zamu shiga ba?" Hajiya ta ce ga masu fito nan za mu bar motar mu hau ƙwale-ƙwale, tsoro ya kama Zainab ta ce na shiga uku! Gaskiya Hajiya mu haƙura mu koma yaushe zan shiga ruwa ban taɓa shiga ƙwale-ƙwale ba, Hajiya ta ce da Allah ni yi min shiru saboda uban wa zan shiga ruwan ba saboda ke ba,sai mun koma ki damu mutane.

Sun shiga ruwa Zainab ga tsoro ga faɗan Hajiya,har suka fita. Daga nan suka yanki wani daji a ƙafa,gurin duk ƙarafa ne irin dutsinan nan masu faɗi can suka hango bukkar Bokan,suna isa Bala ya ce Hajiya ina son yin sallah don na tabbata yanzun anyi isha'i. Ta ce sai ka koma can baya nan ba gurin sallah, ya saki baki yana dubanta nan kuwa ya juya ya ce zan jira ku gurin mota in ma ƙwana ne sai in ƙwana ciki, ta ce haka ya yi,ya juya yana tunanin halin Hajiya shi kam ya kusan barin aikin nan, ya tafi ga yunwa ga gajiya ga rashin sallah.

Su kam suna tsugunne gaban Boka bayan ya zunduma ashar sannan ya hau zagin Zainab kaga Æ´ar tsinanninya Æ´ar abun uba mu baki maganinmu ki ajiye? Ke sarkin tsoro to bama bawa mai tsoro magani, ya É—ago maganin ya nuna mata kinganshi nan mun saka aljani ya É—auko mana abun mu Æ´ar tselan uwa,sai kuma bada kuÉ—i sannan mu maida miki,mamaki ya cika Zainab da taga maganinta.

Hajiya ta ce godiya muke Boka a yanzun muna neman afuwa a gurinka ka bamu taimako,ya dubi Zainab da idanunsa jajaye bakinsa ɗoyi na fita duk sanda ya buɗe, ya ce in na baki bakiyi ba to zan barki da aljanu su bi min haƙƙina,ƙa'idar maganina sati ɗaya in ya wuce zanyi hukunci ya ce ya kika ce? Ta ce zanyi, ya ce kisa ko rashin lafiya kike son a ɗorawa ja'irin mijinki da matarsa?.

Ta ce nafi son na faɗan suyi ta zabga faɗa, ya ce kin samu gashi,ya miƙa mata maganinshi na farko daya bata ya ce kije kisa cikin abinci ko ruwan sha ki tabbatar sun sha tare lokacin zukatansu zasuyi zafi su dinga jin zafin juna, amma fa in kika bari ɗaya ya ci wanda ya cin shine zai zama mai zafin rai kuma asirin zai karye bada jimawa ba, sannan asirinki zai tonu, Hajiya ta ce Boka matsalar ta yaron gidan dake musu aiki yasa mata ido, ya yi dariya ya kai hannu kan wasu ƙoƙuna ya ciro wani ɗan ƙullin magani ya yi surkulle ya miƙa mata, riƙe wannan zaiyi maganin shegen yaron.

Zaki mallake shi yanda ko uwarshi ki ka ce ya kashe zai aikata bare sama wata magani, ta ce to ya zanyi Boka?

Ya ce "Kiyi tsirara sannan ki shafe jikinki gargaɗi kada ki yarda ya shafi gabanki,da kin yarda ya shafi gabanki sai dai kiyi haƙuri yaron zai amfana dake,Ta dubi Boka da sauri,ya cigaba sosai daga nan zai bi umarnin ki in kuma kika bari maganin ya taɓa gaban yaron zai liƙe miki kema haka.

Hajiya ta ce "to Boka tayi amfani dashi gurin mijinta mana maimakon ta mallake wani sai ta mallake mijinta." Ya ɗaga sauti da ƙarfi kul! Kul! Tayi amfani dashi gurin mai sallah, mijinta yana sallah aljanun mu zasu ƙone in mun turasu gurinshi ke kar ki fara uwarshi tana tsaye kanshi tana yawan yi mishi addu'a.

Zainab ta ce to Boka a canzan wani, ya ce ina ai sharaɗi magani shine dole ayi in an karɓa,in kuma anƙi aga ɓacin rai,ku tashi ƴan tselan uwa maganar kuɗin aiki sai magani ya ci zan fanshe a jikinki,kije da kuɗin ki dinga shan madara rana ɗaya zan zo in shanye peak zaki sha sau uku a rana zan zo miki insha jikinki da zaran kinyi amfani da maganina ya ci,ku ɓace min a nan bari jinnu su kai ku gurin motarku, kafin suyi magana sai jinsu su kai fuu anyi waje dasu sai tif a ƙasa kusa da mota, cikin tsoro Bala ya buɗe mota ya leƙo bai gane su ba saboda dare, ya soma addu'a, Hajiya ta ce Bala ya gane muryarta ya ce Hajiya kune? Suka ce Eh maza tada mota mu bar dajin nan haka suka kamo hanya sha biyu suka zo wani ƙauye, dole suka nemi gidan maigari don ƙwana.

Washegari suka ɗauko hanya a cikin Minna sukayi masauki cikin wani hotel don su ƙwana biyu tunda sunce ƙwana uku Bala ma sun kama mishi nashi ɗakin. Zainab dai ba'a cikin sukuni ta ƙosa a koma tayi gaggawar aikata aikin Boka gashi ya ce ta dinga shan madara zai zo yasha a jikinta abin ya yi mata yawa.

Tun safe suka ɗauko hanyar Abuja sha biyu suka shigo dan ma sun samu matsalar mota a hanya. Daidai lokacin Pretty da bebyn ta suna gida suna shagwaɓa juna, kullum da ƙyer yake tashi ofis. Yanzu da suka zube a falo tana sanye da gajeren wando na jeans sai riga ɗamamma sai gashin ta gefe ta kama da ribon shima kalar wandon, tayi ƙyau kanta yana jikinshi yana wasa da gashin kanta, ta ce beby yaushe zan koma aiki ne? Ya ce an kusa gama ofis ɗin ki na Kaduna? Kuma gashi ban son muyi nisa ace sai weekend zan ganki? Ta ce niko nafi son haka saboda nafi son in ganni daga ni sai kai,ya ƙara jawo ta jikinshi ina sonki da yawa Pretty har ban san kalar son da nike miki ba.
Chapter 17 · 0% Book details