← Book details Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gama cin tuwon ta ƙwashe ƙwanukan har da na Umma ta nufo bakin rijiya tana wankewa, Umma dake cikin ɗakin Affa tasa baki ta kira Ruƙayya, ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin.

Gabanta ne ya faɗi san da taga takardar ta a hannun Affa, bayan ta samu guri ta zauna sai Affa ya ce "Ummanki ta sanar da ni zaki tafi Legos?" Gaban Ruƙayya yana faɗuwa ta ce "Eh, can aka tura ni ɗazun naje na amso." Ya ce "A da dai kinje Kano, yanzu ma da Kanon ne ko irin su Katsina jihohinmu na nan Arewa sai in yarda amma ba zan amince ki je gari kamar Legos ba, a'a." Shiru Ruƙayya ta yi har sai da Affa ya gama sannan ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara ne don Allah kayi haƙuri."

Ya ce "Ke ba ajin zancen aure a bakin ki sai dai na karatu,ki sani na matsu naga auren ki, Allah yasan nayi miki yanda zan iya ita wannan ƙawar taki da ku ka je biki,ba gashi ba tayi auran in ma bautar ƙasar ne ai tana ɗakinta zatayi yanzun ko?

Ruƙayya ta ce "Affa su fa karatu zasu cigaba law school zasu shiga dubu ɗari biyu da hamsin, kuma suma wata tara ne zasuyi."

Ya ce koma menene ai yanzu a ɗakinta zatayi shi yi ko? Shiru Ruƙayya tayi Affa ya cigaba da mata masifa kan aure don haka ba batun wani service.

*** *** ****
Goma daidai ta gama tsantsara ƙwalliyarta cikin Ankon bikin Munira da suka yi,ta fito ta shiga ɗakin Umma.

Umma ta ce "To maimakon ki tuna min sannan in sanar da Affanku shine ki kayi shiru." Ta ce yi haƙuri Affa zai ce a'a ne kinsan baya son yawan zuwa." Ta ce ki gaida su, Shagon kusa da lungunsu ta tsaya tayi ma su Mama da su Muhsin tsarabar chizee da bisket. A hankali take tafiya bakin shagon Nasir "Kai Oga gafa mutuniyarka." Inji wani yaron shagon shi "Wa kenan.?" Yaron ya ce "Ruƙayya,kai Oga yarinyar nan aƙwai yanga,dubi tamkar mai tausayin ƙasa , koda yake ai tana da abubuwan yangar."

Nasir ya miƙe daga aikin da yake ya fito ya tsaya suka gaisa ya ce zaya zo da dare. Bayan ta je gidan Murja sun wuce gidan Fati a can ta ce don Allah su roƙar mata Affa ya yarda ta je service suma sun mata ƙorafin aure ta yi musu ƙaryar cewa ai aƙwai wanda suka haɗu dashi bikin Munira kuma shi zata aura.

Kafin ma ta gama service komai zai kammala kuma zaya yarda tayi aikin ta. Sun yanke shawarar kan cewa Ruƙayya ta je ta samu Yaya Amina da Yaya Suwaiba da Yaya Sadiya ta gaya musu su haɗu ranar juma'a kasancewar Affa in ya dawo sallar juma'a baya komawa kasuwa shi ne suke son magana dashi.

*** *** *** ***
Yasha mamaki da ya samu gidan tamkar kasuwa, ƴan jikokinshi suka yi mishi oyoyo, ya ce biki kuke yi ne a gidan?" Ummansu wacce ta fito dan taran shi, ta ce, sun zo gaida kaine affansu." Ya ce "sai dai bayan masallaci don lokaci ya ƙore,in na dawo sai mu gaisa." Sun mishi sannu da zuwa sannan suka koma suka ci gaba da hirarsu.

Ɗakin Umman shi ma ya shigo suka dinga gaishe shi ɗaya bayan ɗaya Sadiya ce ta soma magana "Affa dama gurinka muka zo." Ya ce to ince dai lafiya? Ta ce lafiya lau dama kan zancan Ruƙayya ne. Muka ce don Allah kayi haƙuri ka barta tayi bautar ƙasar tunda wata tara ne. Suwaiba ta ce kuma Affa ai Auta tana da kamun kai munsan zata tsare kanta," Amina ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara kamar yau ne." Su kuma su Murja da Fati suka ce "Haƙurin da aka yi na shekaru kusan biyar ban dama na secondary ai wata tara bazaya ga gara ba.

Ya ce "To duk naji jawabin ku yanzu, Amma ban ji wacce tayi zancan aure ba,ku ɗauki misali a kanku aƙwai wacce ta wuce secondary dukkan ku? Suka ce a'a, ya ce na mata haƙuri ko ban ba? Suka ce kayi, ya ce, to ta haƙura gara ma da da tsayayye ne da sai na amince.

Sadiya ta ce "Aƙwai wanda suka yi magana, haka suka yi tayi kafin daga baya Affa ya ce yana da sharaɗin,sharaɗin sune zasu ɗauki nauyin yi mata siyayya, zuwa kuɗin mota dan bashi da kuɗi. Ya ce karatun ta ne ya cinye komai harda kuɗin da bawan Allah ya aiko mishi da zakka, suka ce mutumin nan ko wanene yana da mutunci, Allah yasaka mai da alkhairi. Umma ta ce ƙwanakin nan ba'a yi sati uku buhun shinkafa huɗu da taliya ya aiko mana gashi nan har yanzu ita muke ci Affa ya ce hakane gashi ya ƙi mu haɗu ina son in mai godiya ba hali. Yaran suka ce Allah ya saka mai da gidan aljanna shima ya biya mishi buƙatunshi.

Sun gama yanke shawarar su kowacce zata bada daidai aljihun ta mata kenan sarakan zumunci,Yaya Fati ta dubi Ruƙayya "Auta don Allah gidan mutumin nan na kusa da Bus stop zan aike ki,mai saida litattafan Hausa, ina son wani littafi ne sabon fitowa ne,na je shagon shi ya ce min suna gida.

Ruƙayya ta ce "To ki koma shagon mana tunda yanzun dai nasan baya gida ƙila ma ya kai takardun shago, Fati ta ce "Ke dai baki son zuwa ne bari in zamu wuce zan biya da kaina."

Sadiya ta dubi Fati ta ce "har yanzu kina nan da shegen karance-karancenki É—in nan."

Murja ta ce "Ai in gaya miki sai abin da ya yi gaba in dai Fati ce tunda mijinta ya É—aure mata gindi.

Fati ta ce "Dole ne ya ɗaure min tunda yana ganin amfanin shi, Allah ku kun jahilci karatun Hausa ne kawai, amma yana da fa'ida sosai matsawar za kiyi amfani da abubuwan da ki ka gani na ƙaruwa zaki koyi kula da mijinki yanda zaki zauna da kishiya da dangin miji,ban da wannan ga kalolin soyayyar da zaki ma mijinki koda gurin ƙwanciya ne, sannan....." Dundu Amina ta sakar mata tare da faɗin.

Lallai Fati Yaya Sadiya ki ke gaya ma maganar ƙwanciya da miji?.

Suwaiba ta na dariya ta ce "Allah ya ƙyauta miki Fati." Ita ko Ruƙayya sai tayi waje, Sadiya kuma ta ce "Uhm ni dai ai kallon ta nake yi." Fati ta ce "Kun ji ku da wani abu, dukkanmu ba mata ba ne.

Murja ta ce "kina da wani da yake bayani kan ƙwanciyar ki ara min." Ta ce bari in kinzo gidana sai muyi maganar.

*** *** *** ***
Ruƙayya ƴar gata sun haɗa mata komai ta tafi garin Legos. Haka aikin nasu ya yi ta cigaba ƙwanci tashi yau sati shida kenan Ruƙayya tana garin Legos, duk waɗanda suke tare tafi shaƙuwa da Nuraddeen M Adam ɗan Kano ne ko yaushe suna tare.

Yau sati ta fito sanye da baƙar doguwar riga gyalenta baƙi takalmi da kuma baƙar jaka. Ta yi ƙyau sosai, Nuraddeen ya dube ta,sai ina Ruƙy, ta ce "Ina son naje saloon gashina ya yi datti ina son na ɗan wanke, ya ce to bari muje, suna tafiya suna labari har saloon bayan an gyara mata ya nemi ta rakashi kasuwa sun shiga gari sosai kafin su ga wani super market.

Gaban Ruƙayya ya yi mugun faɗuwa, ta tsaya, Nura ya ce "Kin gaji ne?" Ta ɗan wayance.

Sosai ma, ina son na huta" ya ce "To mu ƙarasa daga nan sai gida suna shiga idon ta ya sauka akan Dady,yana tsaye yana waya ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskanta ta kuma shige ɗaya gefen.

Dady bai kula da ita ba sai dai gaban shi ya yi mugun faɗuwa, waige-waige ya shiga yi tamkar mai neman wani. Lokaci guda kuma ya fita wajen. Sun jima sannan suka fito bata ganshi ba tanata yi ma Allah godiya. Sai dai kuma taji sanyi ganin da tai mishi. Shi kam Dady tana ganin kullum ƙara masa ƙyau ake yi,yaya zata yi da son Dady?.

*** *** *** ***

Hajja ta dubi Dady sannan ta dubi aƙwatunan gaban ta. Haƙiƙa kaya sunyi tuzuru, sai dai nace Allah yasa kada itama muji shiru irin na wancan lokacin, don wannan karon in bai yiwu ba Allah ƙauye zamu je ma samo maka mata,mun gaji da ganin ka haka,ko so kake sai na mutu? Ya ce "Allah sarki Hajja insha Allahu sai kin goya min ƴaƴa da jikoki."

Ta ce "Allah ya tsare ni in samu ma inga auran naka,ai ko yanzu nagode ma Allah.

Ya ce "To Hajja zan wuce amma ranar juma'a zan zo nan Kaduna don haka zan iso da azumi zan buɗe baki a nan, Please ai min waina da fankasu,in kuma samu Hollandia mai sanyi, ta ce Allah shi kaimu, yanzu ai kayi hankali ba irin da ba, ya ce da me nake yi? Ta ce wancan auren da kayi bai yiwu ba ai kayi rawar kai,nan fa kazo kasa ni gaba kana cewa ga waya in ma Momyn ka magana su wuce da wuri kai kayan lefe,yayi murmushin yaƙe tare da girgiza kai don Hajja ta tuno mishi wani abu mai motsa rai ya ce "Hajja bazaki gane ba ne wancan auren da man aƙwai bambanci,na tabbata inda ace Pretty ce zan aura wannan auren tabbas cewa za kiyi da,ban yi komai ba saboda rawar jiki ya tsura ma window ido tamkar a nan zai ga Pretty ɗin shi a gurin. Wasu ƙananan hawaye suka taru a zagayen ƙwayar idonshi. Ya furta a hankali "Allah ya rage ma aya zaƙi." Ya dubi Hajja har in mutu zan kasance ina son Pretty."

Hajja ta yi data sanin furta mai maganar auran shi na da,
Chapter 2 · 0% Book details