← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida tayi kukanta mai isarta sannan ahankali ta fara sauke ajiyar zuciya hakan yasa ya ɗago fuskarta akan hannayensa yana kallonta ya ce" I'm sorry kinji na baki haƙuri a madadin Imad" kwaɓe fuskarta ta yi cikin sanyin murya ta ce" yaya ka kai ni wajen Ammina please" sosai ta bashi tausayi jin wacce tskeson gani gashi yasan bashida wannan damar bazasu taɓa yarda ya kai ta ba, shurun da taji ya yi ne yasa ta ce" yayaaaa" lumshe idanunsa ya yi ya ce" na'am ƙanwar yayaaaa" murmushin da batayi niyya ba ta saki ta ce"Allah yaya ka daina banaso" okay ya ce sannan ya kama hannunta, sauri riƙe nasa hannun tayi tana kallonsa, kallonta shima ya yi ya ce" mene?" "bazan bika ba" haɗe ransa ya yi ya ce" bangane ba Fattomah ina ne bazaki bini ba?" sunkuyar da kanta tayi sai kuma ta share hawayen da yake ƙoƙarin fitowa kan idanunta ta ce"ka kaini wajen Mommy kaji Wlh bazan kwana anan ba" sosai ya yi mamakin jin furucin bakinta sanin kuma halin gaddamarta yasa ya ce"muje na ɗauko mota to" naɗe hannayenta tayi a ƙirji ta ce" kaje yaya ina jiran ka anan" girgiza kansa kawai ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan.

Zaune ya tarar da Imad yana danna wayarsa haka ma Salma wacce take zaune tana jiransa, sallama kawai Jawaad ya yi musu sannan ya haye sama ko kallonsa Imad bai yi ba saida ya haye saman sannan ya miƙe without looking at her ya ce"muje" babu musu ta miƙe dan daman sunyi sallama da Ayrah ɗaga mata hannu tayi itama ta mayar mata sannan sukai waje, fitowa ya yi jikin wata jallabiya ash colour wacce ta amshi farar fatarsa da mamaki ya kalli Imad wanda yake ƙoƙarin shiga mota bayan guards sun buɗe masa, ƙara sawa ya yi jikin mota ya yi nocking hakan yasa ya sauke glasses ɗin yana kallonsa ya ce" ina zaka je kuma yanzu fa zan dawo?" ba tare da ya kalleshi ba ya ce" gida" shuru Jawaad ya yi na wasu sakwanni sannan ya ce" okay saida safe" gyaɗa masa kai Imad ya yi sannan ya zuge glasses ɗin.

Komawa ya yi ya shige motarsa saida ya jira motocin Imad suka bar gidan sannan shima ya yiwa motar key ya fita, tsaye ya sameta daidai inda ya barta tana ganinsa ta tawo ta shiga motar sannan ya ci-gaba da tafiya, ganin yanda ta lumshe idanunta yasa ya ce" bacci ki keji?" buɗe idanunta waɗanda suka fara sauya kala ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce a hankali" zazzaɓi nake ji yaya" tsayar da motar ya yi yana taɓa jikinta ya ce"subhanallahi sannu bari na siya miki magani kinji" gyada masa kai tayi sannan ya ci-gaba da tafiyar. Wani pharmacy ya tsaya ya siya mata magunguna Sannan suka fito tafiyar 5mins ta kawosu wajen wani suya spot Banda ƙamshi mai daɗi babu abinda yake tashi a wajen fita ya yi ya karɓo kaza leda biyu sai chilli yoghurt daya siya sannan ya dawo, da idanu kawai Fattomah ta bishi har ya sake barin wajen.

Zaune suka tadda Mommy tana danna system da alama wani abun mai muhimmanci take gabatarwa, sallama sukayi ta ɗago idanunta tana kallonsu zare glass ɗin idonta, kwanciya Fattum tayi akan cinyarta tana lumshe idanunta sosai take jin Mommy tamkar Amminta kodan saboda yanda itama ta ɗauke ta matsayin ƴa ne????, Zama ya yi suka gaisa da Mommy sannan ya kalli Fattum wacce take shirin fara bacci ya ce"keee zo nan" a hankali ta miƙe tana tafiya kamar bata so ta ƙara so wajensa hannunta ya kama ya zaunar da'ita gefensa sannan ya buɗe ledar da ya shigo da'ita, kallonsa ta tsaya tana yi har ya kutsuro kazar yana kallonta ya ce"haaaa" babu musu ta buɗe bakinta ya dinga bata kazar har Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya bata maganin ya miƙe ya ce" yanzu kije ki kwanta saida safe" tashi tayi ta shige apartment ɗinta shi kuma ya yiwa Mommy sallama, Mommy ta ce"wai lafiya naga ka dawo da'ita da daren nan?" murmushi ya yi ya ce"rigima ta sanya sai na dawo da'ita kuma zazzaɓi take" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya fita, nima da naga dare ya yi kuma ga Meeyrah ta sanyani gaba da kallo yasa na tattara alƙamin na ajiye naje na kwanta.

*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*
[5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 15-16*

Kusan 5days kenan basu haɗu da Imad ba dan daman Jawaad ne mai nemansa sosai kuma shima ransa ya ɓaci, kasancewar yau Friday yasa da wuri suka tashi daga makaranta, tsaye suke itada Aysha tana mata hira wacce ita kaɗai take abarta dan Fattomah ba saurarenta take ba, tsaki Aysha ta yi tana kallonta ta ce"wai ke wannan wane irin wulaƙanci ne ina yi miki magana kin yimin shuru" langwaɓar da kai ta yi ta ce"bana cikin yanayi na magana ne Aysha please ki rabu dani" murmushi Aysha ta yi ta ce"shikenan thank you" gaba ta yi Fattum ta bita da idanu dan ko ajikinta. Har wajen 12:30pm babu wanda ya zo tafiya da ita hakan yasa ranta ya ɓaci duba jakarta ta yi taga tanada kuɗi hakan yasa ta tsayar da keke napep ta sanar dashi inda zai kaita sannan ta shiga, shiga parlon ta yi bayan tayi sallama babu kowa cikinsa sai tv dake faman aiki ita kaɗai hakan yasa tayi shigewarta apartment ɗinta dan a matuƙar gajiye take, wanka kawai tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar riga ta lace ɗinkin bubu sosai ya yi mata kyau musamman yanda maroon colour ɗin ta haska fatarta, veil ta ɗauko fari ta sanya sai takalmi half cover shima fari yi tayi kamar amarya dalilin mayafin data ɗora akanta, wasu yari da sarƙa ne na gold wanda Mommy ta bata ta ɗauko ta sanya sannan ta saka agogo wanda yaya Jawaad ya siya mata lokacin da suka je super market, Masha Allah sosai Fattomah tayi kyau abinta bazaka taɓa cewa she's under 16yrs ba domin ko ƴar 20yrs ba zata gaya mata cika ido ba sannan kuma nutsuwarta dan idan ba magana tayi maka ba bazaka taɓa ganin yarintar tata ba da zarar tayi magana tofah zaka gane yarinya ce.

Fitowa parlon tayi tana faman zuba ƙamshi murmushi Jawaad ya yi yana kallonta ya ce"enyeeee kinyi kyau sosai princess" rufe fuskarta tayi da hannunta cikin shagwaɓa ta ce"Allah yaya bansooo" yanda tayi maganar ya kwaikwaya ya ce" Allah kanwa inasoo" tuntsirewa da dariya ta yi shima yana taya ta ya ce"nima ai na iya shagwaɓar" turo bakinta wanda yasha lip gloss ta yi ta ce"Allah babu kyau" murmushi ya yi ya ce"shikenan muje lokaci na tafiya" gaba ya yi tana biye dashi abaya har suka fice daga cikin parlon.

Kalle-Kalle kawai Fattomah keyi tunda suka shigo cikin gidan sarkin wanda bata taɓa zuwa ba kafin sannan, sosai gidan yake bata sha'awa dan tana shige shi idan zata tafi Makaranta, ko ina suka shige bayine ki tsugunawa suna gaishesu ita ce kawai take mayar musu da murmushi shi kuwa Jawaad ko kallon inda suke ba ya yi, a babbar fadar gidan suka zaune inda nan ne suka tadda mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Baira, murmushi ya yi yana kallon Fattomah ya ce"sannu kinji" yanda ya yi maganar tamkar Daddy ne ya yi yanayinsu ɗaya kana ganinsu kasan sarauta da arziƙi ya gama ratsa su, sunkuyar da kanta ta yi hakan yasa Jawaad ya ce"Dad wai kunyar ka take ji fa" murmushi mai martaba ya yi ya ce"wai haka Faɗeemah?" Saurin girgiza kanta ta yi tana kallon Jawaad, murmushi Jawaad ya yi ya ce"hakane mana"turo baki tayi amma batace komai ba saboda mai martaba da yake wajen, sosai ya dinga janta da hira tun tana sunkuyar da kai har ta saki jikinta itama tana bashi amsa. Sai wajejen ƙarfe 6pm sannan suka baro gidan sarkin kai tsaye kuma gidansa suka shige, suna shigowa gidan bayan ya yi parking ta kalleshi ta ce"wai yaya naga ka kawoni nan?" Yana kashe motar ya ce"E, meya faru?" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"Ni fa gida zan koma" Jawaad bai ce mata komai ba ya sauka daga motar ya shige gidan da kallo ta bisa tanajin zuciyarta na tafarfasa wato yama mayar da ita ƴar iska, kwafa tayi sannan tabi bayansa tana turo baki, zaune ta tarar dashi yana magana da Ayrah wacce take zaune gefensa kamar ta shige jikinsa, sunkuyar da kanta ta yi ta shige bedroom ɗin ba tare da ta yarda ta kallesu ba.

Murmushi ta yi tana kallon Daddy ya ce"Eh mana yaushe zaku gama ni kuma nayi alƙawarin kai ki kamar yanda nace" dariya Fattomah ta yi ta ce"sauran 3months kaga yanzu Waec zamu fara" Daddy ya ce"okay toh Allah ya bada sa'a dear" murmushi ta yi ta ce"Thank you Daddy", murmushi Daddy ya yi lokacin da Imad yake zama gefensa bayan ya yi sallama cikin parlon da sauri Fattomah ta miƙe tana shirin barin wajen Daddy ya ce"ina kuma zakije Fattum?" cikin rawar murya ta ce"Daddy zan ɗan duba abune a ɗaki"okay Daddy ya ce sannan ta fice daga parlon da sauri har tana ƙoƙarin tuntube. Taɓe baki Imad ya yi bayan yaga shigewarta, kallonsa Daddy ya yi ya ce"Imad daman inason magana dakai" kallonsa ya yi ya ce"ina jin ka Daddy" Daddy ya ce"in sha Allah next week zamu tafi Abuja kasan daman zama nake temporary anan, kuma akwai abubuwa dayawa" kallonsa Imad ya yi ya ce"Okay Daddy Allah ya kaimu" tashi ya yi ya ce"Ameen zuwa gobe zan sanar dakai abinda ake ciki" tashi shima Imad ɗin ya yi yana zube hannayensa cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya ce"Allah ya kaimu bari naje wajen Mommy"okay Daddy ya ce sannan shima ya yi waje.
Chapter 8 · 0% Book details