← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dariya Khaltum tayi tana kallon yayan nata ta ce" tab ɗijan yanzu yaya ka rasa wacce zakace kana so sai Fattomah tab wlh kuwa kana tare da wahala dan ka rigada kasan halinta kuma yanzu ma bata gida ɗazu Mama tace Ammi ta faɗa mata a asibiti" zaro ido ya yi ya ce" dan Allah ina ta tafi kuma?" "Wai yayan Abbanta ne ya ɗauketa tana gidansa a tudun yola" numfasawa ya yi ya ce" nikam babu ruwana dole sai naje inda Fattomah take domin har cikin raina ita ce wacce nakejin zan iya rayuwar aure da na daɗe inason yarinyar cikin raina bazan bari na rasata ba in sha Allah" kallonsa kawai Khaltum take dan ita batasan sanda ya koma haka ba shida magana ma bata damesa ba amma duk yabi ya rikice akan Fattomah, saida yagama fadar duk abinda yakeso sannan ta ce" yaya wlh ka cire ranka da Fattomah kaga yanzu ta koma gidan yan gayu kuma daman ita tafi kala da masu kuɗi idan kace zaka zira jiki ranka zai zo yana ɓaci abanza kawai kayi haƙuri ka rungumi Hafsarka itace take daidai dakai nidai a tawa shawarar" girgiza kansa ya yi ya ce "wlh bana daina son Fattomah ba har ƙarshen rayuwata kuma in Sha Allah sai na aureta ta zama mata agareni" rasa abinda zata ce masa tayi dan taga abin nasa ya fara sauka daga kan layi kuma duk irin shawarar da zata bashi ba ɗauka zai ba yasa ta ce" Allah ya taimaka yaya" miƙewa ya yi ya ce" Ameen Ameen shine abinda yafi dacewa ki faɗa" gaba ya yi ta bisa da kallo tana tausayin halin da yake ƙoƙarin sanya kansa.

Har wajen ƙarfe 10pm Daddy bai shigoba ita kuma taƙi kwanciya tana zaman jiransa babu yanda Mommy batayi da itaba tace ba bacci take jiba dukdan yadawo taji halinda Abbanta yake ciki, kallonta ya yi ganin yanda take bacci akan kujera kana gani kasan baccinne ya ɗauketa ƙarasawa ya yi gabanta yana kallonta sosai yaga tana bacci hakan yasa baiyi tunanin tashinta ba ya ɗauketa tamkar Baby ya shige da'ita saman.

Yana shiga ya kwantar da'ita sannan ya jamata duvet ya lulluɓeta addu'ar bacci ya yi mata sannan ya ƙaro gudun AC ya juya ya fita kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa.

*Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 09121033575 or 08106571862 WhatsApp*

*FATTOMAH*

*Nanameera ce#*

IDAN HAR KIN KARANTA TO KIYI SHARING ƊINSA SISTER.[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITER'S ASS.

BOOK ONE

PAGE 7-8.

Kallonsa Mommy tayi ta ce" babu yanda banyi da'ita ba amma taƙi yarda taje ta kwanta wai batajin bacci dukda nasan daman ta gaji" murmushi ya yi ya ce" Allah sarki kawai ta damune akan halinda mahaifinta yake ciki in sha Allah gobe zakije ki dubashi sai ki tafi da'ita" okay tace masa sannan ya shige toilet dan watsa ruwa. Kalle-Kallen inda ta kwanta ta hauyi dan ita dai tasan ba anan wajen tayi bacci ba hasalima batasan sanda ya yi bacci shuru tayi na wasu mintuna sai kuma ta sakkoda ƙafarta a hankali ta miƙe ta shige toilet ɗin, shiryawa tayi cikin uniform ɗinta ta fesa turare wanda har Saida ya fara yawa murmushi tayi ita kaɗai sai kuma ta ce" I'm Fine gurl" tuntsirewa tayi da dariya Ni kuwa nace Fattum anajida yarinta. Kallon wanda yake zaune a parlon takeyi har ta ƙara so ɗaga kansa ya yi aikuwa cikin sa'a idanunsa ya shige cikin nata saurin ɗauke nata idanun tayi tana sunkuyar da kanta murmushi ya sakar mata ya ce" Hello!" sunkuyawa tayi ta ce" ina kwana?" "Lpyklao ya kike?" tana zama kan ɗaya daga cikin royal cusion ɗin parlon ta ce" ina lafiya" shiru sukayi duka na rashin abin faɗe dan ita bata taɓa ganinsa ba kuma shima haka tsinkayar muryar Mommy sukai tana faɗin

" Jawaad yaushe ka shigo?"

Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce"kina can ciki Mommy daman banason na tashe kine that's why nayi zamana anan sai kuma naga wata baƙuwa" ya ƙarashe maganar yana kallon Fattomah, murmushi Mommy tayi ta ce" kai kam bakada dama toh ba baƙuwa bace cousin ɗinku ce" sake kallon Fattomah ya yi sai kuma ya kalli Mommy yana dafe kansa ya ce" sai yanzu na lura Mommy wllh tana kamada Family" zama Mommy tayi tana murmushi ta ce"kadai ji dashi, Fattomah kin ci abinci?" girgiza mata kai tayi Mommy ta ce" ok bari na saka akawo miki amma ki dinga shiryawa da wuri saboda lokaci kinga yanzu ma kusan 7:25am ne" Tom tacewa Mommy sannan ta cigaba da wasada fingers ɗinta.

Murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" Abbana sannu kaji ya jikin naka?" Shafa fuskanta ya yi ya ce" nasami sauƙi Faɗimatoh ki daina damuwa kinji" goge mata hawayen fuskanta ya yi da hannunsa ta sakar masa murmushi, murmushin shima ya mayar mata ya ce a nutse "Allah ya yi miki albarka Faɗimah" "Ameen ya Allah Abbana".

Saida aka idar da sallar isha'i sannan suka baro asibitin wanda azahirin gaskiya bada son ran Fattomah suka baro ba dan tafi ƙauna zama wajen Abbanta da Amminta, murmushi Mommy tayi ganin yanda take ta cin magani a hanya suna zuwa wajen wani mall tacewa drivern ya tsaya, parking ya yi sannan ta kalli Fattomah ta ce" Baby zo muje ki rakani ciki" gyaɗa kanta tayi sannan Mommy ta kama hannunta suka fito Da motar dan shiga cikin mall ɗin, duk irin yanda take moody saida ta saki jikinta tana zaɓar duk abinda taga ya burgeta awajen domin Fattomah batada rufi indai abu ya yi mata tofa sai ta ɗauke shi har suka gama siyan duk abinda suke buƙata aka kai musu mota sannan suka shige gida.

Murmushi tayi ganinsa zaune a parlon da alama kallo yake yi zama tafi kan kujerar cikeda gajiyawa ta ce" washhhh!!" Kallonta ya yi ya ce" keee Fattomah yaushe kika gajin?" dariya tayi tana kallonsa ta ce" ayyah yaya Jawaad wllh nagaji sosaima" harararta ya yi ta gefen ido ya ce" babu wani nan"tuntsirewa tayi da dariya ta ce"kaga yanda kayi kyau kuwa yaya?" waro idanunsa ya yi yana kallonta dan yagama fuskantar raina masa hankali take ƙoƙarin yi ya ce" zan kamaki ne yarinya zaki gane ne" gwalo tayi masa lokacin tana hawa kan stairs ɗin benen ya kalli Mommy wacce take tsaye tana dariya ya ce" Mommy watarana sai nayiwa wannan yar taki duka tunda batajin magana" dariya tayi ta ce" aikuwa baka isa ka taɓa min ƴa ba sai dai can ku ƙarke amma ba duka ba" gyaɗa kansa ya yi ya miƙe yana gyara zaman t-shirt ɗin jikinsa ya ce" shikenan tunda kince haka ni zan tafi dan Daddy yana nemana" okay tace sannan ya juya ya fita.

Tsaye suke ƙofar makarantar tasu dan tashinsu kenan, Aysha ce ta kalleta ta ce" Nifa zanyi tafiyata wllh" marairaice fuska tayi ta ce" Ayyah bestie ki ɗan jira mana na tabbata suna hanya wlh banason abarni anan ni kaɗai nasan ke kaɗai zaki iya yimin haka please" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta murmushi Aysha tayi ta ce" to kuka zakiyi ne?" tuntsirewa sukai da dariya atare kamar haɗin baki su kansu ba susan abinda suke wa dariyarba, wata ɓakar mota ce ta tsaya ƙirar Accord sport sai sheƙi take kana ganinta kasan bata ƙananun yara bace tsayawa kowa ya yi yana kallon motar ganin tunda tayi parking babu wanda ya fito kusan 2mins. Murmushi tayi ganin Jawaad ya fito daga motar yana nufo inda take, kallonsa tayi tana murmushi ta ce" yaya kai ne kazo ɗaukana?" gyaɗa mata kai ya yi yana rike hannunta bye bye tayiwa Aysha sannan tabi bayansa. Da sauri ta ja baya ganin kamar mutum daga ɗaya side ɗin mai zaman banza na motar

"Ki shiga baya Fattum"

Kallonsa tayi sai kuma ta buɗe back sit ɗin ta shiga, yana shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar. Duk yanda Fattomah taso taga wanda yake gidan gaban kasawa tayi domin koda wasa bai yarda y juyo ba kuma bai ɗago fuskarsa ba har suka ƙarasa gida, yana gama parking ɗin ya ce" yawwa Fattum ki shiga gida za muje unguwa kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan a hankali ta sauka daga motar kamar me tsoron wani abu, shiga motar ya yi yay reverse yabar cikin gidan da kallo tabisu duka har suka ɓacewa ganinta ko wane wannan?????? abinda zuciyarta ta faɗa mata kenan ɗaga kafaɗarta tayi alamun ko'a jikinta sannan ta kama hanyar entrance ɗin shiga gidan..

*Manage this lover's abubuwan ne sun min yawa☹️☹️🥰*

*Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 08106571862*

*Kina sane da cewa free pages ya kusa ƙarewa ko kuwa A'a, kindly make ur payment sister 🤝🥰*

*Nanameera ce#*
[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.

PAGE 9-10.
Chapter 4 · 0% Book details