Sashe 14
Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Uban me aka yi miki?" yanda ya yi maganar afusace yasa ta ɗan yi baya tana kare fuskanta gudun kada ya kai mata duka, kwafa ya yi sannan ya ce"akwai ubanda ki ke jira anan?" turo ƙaramin bakinta wanda yasha lip gloss kamar ba school zata tafi ba tayi ta ce aciki-ciki "koba kuɗin makaranta zaka bani ba" wani banzan kallo Imad ya watsa mata sannan ya yi wani killer smile, juyowa ya yi gaba ɗaya yana sake ƙare mata kallo ya ce cikin rainin hankali ya ce"wane ya kawo ki gidan nan?" kallonsa Fattum ta yi sai kuma ta ɗauke kai tana zumɓura baki, murmushi Imaad ya yi ya ce"I'm asking you" can ƙasa ta ce"kai ne" ya ce"wane ya siya miki kaya sanda za kizo gidan nan?" asanyaye ta kalleshi sai kuma ta sauke idanunta ƙasa ta ce"Daddy ne" murmushi ya yi for the second time ya ce"da gaske?"gyaɗa masa kai ta yi ya ce"kuma amma shine bai haɗa miki da kudin makaranta ba?, ki ce Daddy baison kije da kuɗi makaranta" da Mamaki Fattomah take kallonshi dan har sannan bata fahimci abinda yake nufi ba. Lura da hakan yasa Imad ya ce"ki huce ki tafi dan ni bazan iya baki wani kuɗin makaranta ba tunda ba ni ne na sanya kiba kuma ba zamana kike ba saboda haka wuce daga nan" tunda ya fara magana Fattum take kallonsa with mouth agape yama za'ayi ta tafi makaranta babu kuɗi ai abinda bazai yiwu ba kenan, ganin har sannan tana tsaye ko motsawa ba tayi ba yasa ya ce"ba kiji abinda na ce miki ba?" cikeda shagwaɓa ta ce"ni wllh bazan tafi babu kuɗin makaranta ba to me zan siya??" baki buɗe Imad yake kalllonta har takai ƙarshen maganartata sannan ya ce"keee, I'm play with you?, kinga alamun Ina yi miki wasa???" shuru Fattomah ta yi dan ita ko kaɗan bai bata tsoro ba kuma yanda ta faɗa bazata tafi ba dole sai ya bata kuɗin school kamar yanda aka saba bata. Jinjina kansa ya yi sannan ya ce"Malama bar wajen nan ko ranki ya ɓaci" ƙin tafiya tayi ta tsaya tana kafeshi da manya manyan idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali, riƙe ƙugunsa ya yi da hannayensa yana sake jinjina gaddama irin tata amma duk iya gaddamarta bata ko kawo ɗan yatsan sa ba. Agogon dake aiki jikin bangon ɗaki ta kalla wajen ƙarfe 7:45am kuma tasan Indai 8:00am tayi tofah baza'a barta ta shiga ba kamar zata yi kuka ta ce"dan Allah kabani wlh zanji yunwa kuma ba'a tashinmu sai la'asar" ko kallonta Imad bai yiba ya haye sama wanda hakan ke tabbatar mata da cewa bazai bata ba.
Waje Fattomah ta yi tana fita taga drivern da zai kaita makarantar already ita yake jira shiga motar ta yi sannan suka bar gidan, saida taga sunyi nisa sannan ta fashe da wani irin kuka, kallonta drivern ya dinga yi ta jikin mudubi har suka isa makarantar tasu. Yana sauketa ta shige makarantar bata ko kalleshi ba, kasancewar ranar Monday ne yasa tana shiga ana assembly ƙin tsayawa tayi ta shige class tayi kwanciyarta ita kaɗai tasan abinda take ji gashi dama ko breakfast bata yiba cikinta banda ƙugi babu abinda yake saboda kwata-kwata arayuwarta bata saba da zama da yunwa ba, runtse idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri kan kuncinta.
Shiru Daddy ya yi na wasu sakwanni sannan ya ce"yanzu me kike tunani?" ajiyar zuciya Mommy ta sauke ta ce"babu komai kawai dai ina missing ɗin yarinyar ne sosai akwaita da shiga rai, amma dai General tana kammala exams ɗin zata dawo ko?" murmushi ya yi ya ce"in Sha Allah haka nake fata daga nan sai ta shiga University ko anan garinne dan banason ta yi nisa damu" Mommy ta ce"Nima haka nake so wlh barima na kira Imad naji ya ya take" daga haka ta ɗauki wayarta dan kiran Imadudden ɗin. Ringing biyu ya ɗaga cikin sakin fuska ya ce"Mommy Barka da safe kun tashi lpy?" murmushi ta yi ta ce"lafiya klao Imad ya naka iyalin?" ya ce"sunanan klao" Mommy ta ce
"Daman kira nayi naji ya Fattomah take kwana biyu kenan banji muryarta ba" Imad ya ce"wallahi tana nan klao Mommy yanzu ma driver ya tafi kai ta makaranta amma tana dawowa zan haɗaku da'ita itama tana ta nemanki" Mommy ta ce"Allah sarki yarinyar kirki kace mata ina matuƙar kewarta yaushe zaka kawomin ita Imad?" murmushi ya yi yana shiga cikin motar tasa ya ce"soon in Sha Allah Mommy", ta ce"Tom Allah ya yarda dear sai anjima" Ameen ya ce sannan ya kashe wayartasa.
Kallonta Aysha tayi ganin yanda duk tayi kamar mara lafiya ta ce"Fateemah bakida lafiya ne?" shiri Fattomah ta yi dan ba komai take magantuwa akansa ba duk da tanajin yunwa kamar ta mutu ta ce"kaina ne yake ciwo kawai babu komai amma" cikin rashin jindaɗi Aysha ta ce"wayyo bestie sannu kinji zo mu ci abinci Kinga an fita breakfast sai mu karɓo magani a clinic" girgiza mata kai Fattum ta yi ta ce"ni bana ci na ƙoshi kije ke kaɗai please", wani banzan kallo Aysha ta watsa mata tana harararta ta ce"dallacan taso malama bana son iskanci"shiru Fattomah ta yi mata bata ce komai ba kuma bata da niyyar tashin, bank yanda Aysha bata yi da'ita ba sai haƙura tayi ta ta miƙe afusace ta ce"kije ki ci kanki da masifaffiyar gaddama"tsaki tayi sannan ta yi waje. Sake gyara kwanciyarta tayi tana riƙe cikinta wanda takejin yana barazanar fashewa akowane lokaci saboda matsananciyar yunwa.
Murmushi ya yi yana kallon friend ɗin nasa ya ce"yanzu ya muke ciki dakai?", waro idanu Imad ya yi ya ce"nifa banason irin haka Kamal gaskiya ka daina yimin irin haka kai meya hanaka yin auren?" tuntsirewa da dariya Kamal ya yi ya ce"ai aure sai Allah ya yi kuma in sha Allah nakusa dan na haɗu da irin yarinyar da nakeson aura soon zakuji ance ku shirya" gyara zama Imad ya yi yana kallon abokin nasa ya ce"bani nasha friend" murmushi Kamal ya yi ya ce"ai aboki ba'a magana yarinya ce haɗaɗɗiya irin ta gaban motar nan na tabbata kaf TAWAGARMU babu wanda zai auri kamar ta excluding You" harararsa Imad ya yi ya ce"da ka haɗa dani mana ɗan rainin hankali" Kamal ya ce"kai ai nasan kanada mata kuma Salma kyakkyawa ce babu ƙarya amma fa wlh wannan tafi Salma kyau nesa ba kusa ba kawai ka zuba ido ta fashe min Friend zanyi ƴaƴa kyawawa zasu gaji ubansu ƴan ball nakeson su zama" dariya ya yi ya ce"toh Allah ya tabbatar friend kace zamu ƙara yawa time ɗin mu mun barwa yara Ball" ya ce"aikuwa dai gaskiya, yaushe zaka koma ne?" ya ce"kullum abinda ake tambayata kenan ni kaina nagaji da zaman 9ja kuma gashi sai nan da 3months" Kamal ya ce"Ayyah to Allah ya kaimu daman bamu gaji da zama dakai ba idan ka tafi sai anganka" tashi Imadudden ya yi ya ce"zanje na karɓi result ɗin" miƙewa shima ya yi ya ce"muje nima zan duba patient.
Kallonta Aysha ta yi ta ce"kinga drivern naki yazo Fattum" gyaɗa mata kai tayi sannan ta saki hannunta ta ƙarasa inda ya yi parking ɗin, buɗe mata motar wani guard ya yi ta shiga sannan shima ya shiga suka bar harabar makarantar, tana shiga ta kwanta nan ƙasan carpet tana riƙe cikinta ta fashe da wani irin kuka, yanda take kukan zaka san a matuƙar wahale take dan ko muryarta ba'aji kuma babu hawaye
Da sauri ta ƙaraso tana kallonta ta ce"lafiya Fattomah?" kasa magana ta yi sai miƙa mata hannu da tayi sunkuyawa Salma ta yi ta riƙe hannunta, sosai ta ji jikinta da zafi hakan yasa ta taimaka mata ta zauna kan kujera ta jingina da jikinta
"Bakida lafiya Fattum?"
Dakyar ta buɗe bakinta tana harhaɗa kalmomin ta ce"aunt.aun.aunty Salma yunwaaaa." ta ƙarashe maganar wasu hawaye na zubuwa kan fuskarta, da mamaki Salma ta ce"yunwa kuma Fattomah?, baki tafi da abinci ba?" gyaɗa mata kai tayi ta miƙe da sauri ta shige kitchen dan samo mata abinda zata ci. Saida tagama jera kayan kan wani ƙaramin Centre table sannan ta ce"taso ki ci" a hankali ta dawo kusada shi ta zauna Salma ta zauna gefenta ta buɗe plate ɗin, chips ne ciki sai wainar kwai wacce taji wadatacciyar albasa da kayan ƙamshi Fattomah da jikinta har wani rawa yake ta saka hannuta dan ko spooon bata nema ba ta fara cin chips ɗin da kwan har wani lumshe ido take saboda tsananin daɗi, mug ɗin tea Salma ta miƙa mata ta karɓa, tunda ta kafashi a bakinta bata ajiye ba saida ta shanye tass sannan ta ajiye mug ɗin tana sakin wata gyatsa ji kake "ƙettttttttttttttttttt😂"
Murmushi Salma ta yi tana kallonta tabbas ba ƙaramar yunwa take jiba cikin yan mintunan da basu shige 10 ba ta cinye abincin tasss babu abinda ta rage, saida ta gama sannan ta kalli Salma wacce take kallonta tun ɗazu, rufe fuskarta ta yi tana murmushi ta ce"Aunty Salma ban ƙoshi ba" waro idanu Salma ta yi ta ce"da gaske Fattum?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"keee Fattum wanne wane irin yunwa kika ji?" turo baki tayi bata ce komai, murmushi Salma ta yi ta ce"yanzu bari na zubo miki abincinki na lunch kinga daman wannan ai breakfast kika yi" gyaɗa mata kai Fattum ta yi tana murmushi.