← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 25

Sashe 13

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Ameenatou I Ibraheem#*
*Nanameera ce#*

*Like nd share*

*Juma'at Mubarak to oll muslims Allah ya haɗamu da Alkhairan cikinta🤲🤲*
[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.

*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera ce*

PAGE 23-24.

Kallonsa Jawaad ya yi bayan ya tsaya da driving ɗin ya ce"zuwa gobe zan shigo in sha Allah" gyaɗa masa kai Imad ya yi, murmushi ya yi yana kallon Fattomah ya ce"sai da safe dear" kallonsa kawai tayi amma bata ce komai ba ya juya ya sauka daga motar, sosai gaban Fattum ya shiga faduwa ganin ya rage daga ita sai Imad cikin motar shi kuwa ko nuna alamar yasan da mutum bai yiba ya cigaba da driving ɗinsa har suka ƙarasa gida. Kashe motar ya yi ya fice daga ciki hakane yasa itama ta fito tana bin bayansa kamar wata mara gaskiya, a babban parlon gidan wanda yasha kayan alatu kala-kala ta ganshi tsaye yana magana da Salma wacce itama take tsaye jikin kujera da mamaki ta kalli Fattomah sai kuma ta kalleshi ta ce" baƙuwarmu har ta iso?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"kaita wannan apartment ɗin"okay ta ce sannan takalli Fattomah ta ce"muje Fattum" bin bayanta Fattomah ta yi bata sake yarda ta kalleshi ba. Tsaki ya yi sannan ya haura samansa, sosai apartment ɗin ya tafi da imanin Fattomah dan ya yi matukar haɗuwa kana gani kasan gidan manya ne, kallonta Salma ta yi ta ce"nan ne ɗakinki akwai komai cikinsa including kitchen idan kina son dafa wani abun okay?" gyaɗa mata kai Fattum ta yi sannan ta juya ta fita ajiyar zuciya Fattum ta sauke sannan ta shige cikin bedroom ɗin dan kwanciya ta huta.

Tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonsa ya ce"to kai yanzu ina zaka sake samunta?" murmushi Kamal ya yi ya ce"inada numbernta kuma ko ba haka ba ni nasan zamu sake haɗuwa da Fattomah saboda ita ɗin ta kasance mallakina ce kaga dolene mu kasance tare nasan zan sake ganin kayata" girgiza kai Saleem ya yi ya ce"sannunka romeo kace tama zama taka?" jinjina masa kai ya yi Saleem ya ce"Alhamdulillah finally dai Aboki zai yi aure Allah ka nuna mana lokacin nan ai ka zaunu"murmushi kawai Kamal ya yi bai ce komai ba. A hankali take sakkowa daga stairs ɗin tana ɗan Kalle-Kalle gudun kada ta haɗu da Imad har ta ƙaraso parlon, babu kowa cikinsa ko ina ya yi shiru gwanin daɗin zama, kamar wacce aka yiwa dole haka ta samu kanta da zama kan kujerar tana kallon wata drama da ake haskawa Mbc 3 ƙaunarta da cartoon yasa hankalinta duk ya tafi da ganinsa wanda hakan yasa har batasan sanda ya shigo cikin parlon ba, jin kamar mutum akanta yasa ta juya dan ganin waye a mugun tsorace ta mike daga wajen tana mutstsuke idanu, wani banzan kallo Imad ya watsa mata sannan ya ce"get out!!" yanda ya faɗi maganar ne ya sanya taji jikinta na ɓari ganin kamar bata gane abinda yake faɗa yasa ya daka mata tsawa ya ce"ba dake nake magana ba shashasha kawai!!" fashewa tayi da kuka ta tafi da gudu tabar parlon tsaki Imad ya yi ya ce"aikin banza kawai zanyi maganinki ne soon" yana gama faɗin hakan ya juya yana kallon tv ɗin tsaki ya yi ya ce"yarinya ko wahala".

Kuka ta dunga yi ita daman tasan wannan zaman babu abinda zai ƙara mata sai wahala bazata iya zama da wannan mutumin ba ko kaɗan bashida mutunci, tunawa dasu Mommy ya sanya ta sake fashewa da wani irin kuka tabbas tasan ta shiga uku zamanta anan, haka ta dinga kukan nan ƙasan carpet har bacci ɓarawo ya saceta. Wani kallo ya yiwa Jawaad amma bai ce komai ba Jawaad ya ce"gaskiya na faɗa wlh dole sai kana sanyaya zuciyarka saboda yarinya ce ƙarama batada wayo idan da zaka jata jikinka ka nuna mata soyayya wlh duk abinda kace tayi shine zata yi amma indai zaka dinga nuna baka sonta tofah zata dameka ne gwara kayi tunani" murmushi Imad ya yi irin na rainin hankalin nan ya ce"idan ta fasa rashin hankalin, what do you think?, zan rabu da'ita ta ɓatamin rai ne?, wlh duk sanda ta yi min laifi sai na hukuntata i most punish her saboda haka ruwanta ne ta shiga hankalinta ruwanta ne tayi rashinsa nidai ina nan kan matsayata" shuru Jawaad ya yi yana tausayin Fattomah cikin ransa fatansa ɗaya yarinyar tayi masa biyayya domin duk abinda Imadudden ya ce tofah yana iya aikatashi batareda ya yi duban wani abu ba, cikin sigar lallashi ya ce"Allah ya baku ikon zama lafiya shine kawai abinda zan ce maka, yanzu yaushe zaka koma America?" tsaki ya yi ya ce"ina naga tafiya America yanzu ai dole sai nan da 3months idan ta koma wajen Daddy" Jawaad ya ce"please ka kiramin ita zamu gaisa" harararsa ya yi ya ce"ba'a gidan nan ba ka bari ta koma hannun magabatanta please" tuntsirewa da dariya Jawaad ya yi ya ce"ai kaima magabacinta ne yanzu malam ko bakada labari?" "Allah ya kiyaye" tashi suka yi atare Jawaad ya ce"dan Allah ka kirawo min ita" wani kallo ya yi masa ya ce"bakasan hanya bane?" murmushi ya yi ya ce"ai naga mutum da iyalinsa" kwafa Imad ya yi sannan ya bar parlon.

Kallonta Imad ya yi ganin yanda take bacci a ƙasa duk ta takure jikinta, tsaki ya yi sannan ya sanya ƙafarsa ya ɗan shureta, a mugun firgice ta farka saboda daman cikin tsoro ta yi kukan, wani shegen kallo ya watsa mata sanda suka haɗa ido ya sa ta sauke idanunta ƙasa

"Tashi ki fita"

Abinda Imad ya furta kenan sannan ya yi waje, miƙewa tayi tana ɗan turo bakinta itama ta fita wajen. Da sauri ta ƙarasa wajensa tana murmushi ta ce"yaya Jawaad" mirmushin shima ya mayar mata sanda ta zauna gefensa ya ce"Fattomah" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce a shagwaɓe"yaya Jawaad ka tafi dani gida please nan babu daɗi" shafa kanta ya yi ya ce"Ayyah sorry dear ki bari kin kusa dawowa gidana forever" Fattomah bata gane abinda yake nufi ba ta ce"kawai mu tafi yau yaya" murmushi Jawaad ya yi yana kallon Imad wanda ya haɗe rai ko kallonsu bai yiba, cikin sigar rarrashi Jawaad ya ce"kiyi haƙuri ki zauna anan in sha Allah kina gama exams zan tafi dake amma yanzu kiyi haƙuri" raurau tayi da idanu ta ce"Allah yaya kayi alƙawari?" gyada mata kai ya yi ya ce"yeh! amma yanzu ki shirya gobe ki tafi makaranta" jinjina masa kai ta yi ta ce"toh yaya kai zaka zo ka tafi dani?" waro idanunsa ya yi yana murmushi ya ce" Fattum rigima to driver zai kai ki" haɗe rai tayi ta ce"toh ni bazani baaaaa" yanda tayi maganar cikeda shagwaɓa yasa ya yi dariyar da bai shirya ba, wani kallo Imadudden ya watsa musu da ya sanya tayi ƙasa da kanta shi kuwa Jawaad murmushi ya yi ya mike yana kallonta ya ce"saida safe dear ki shirya da wuri kinji" jinjina masa kai tayi ya ce"good gurl Allah ya yi miki albarka" murmushinta mai kyau ta yi ta ce"Ameen yayana" kallon Imad wanda yake danna wayarsa ya yi ya ce"saida safe Footballer" can ciki ya ce"good night dear, Allah ya tashemu lpy" Ameen Jawaad ya ce sannan ya juya ya fita. Miƙewa ta yi ta shige ciki yabi bayanta da wata uwar harara ni kuwa nace abanza 😂😂.

Da sassafe ta tashi ta shirya saboda abinda yaya Jawaad ya ce mata, bayan ta ɗauko school bag ɗinta ta sakko ƙasa dan tafiya makarantar, tsayawa ta yi dalilin Imad data gani tsaye jikin dinning table hannunsa rikeda mug na tea, a ɗan duburbarce ta ce"ina kwana?" idan table ɗin dake gaban Imad ya yi magana to Imad ma ya yi magana ganin haka yasa ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba amma tana tsaye dan batasan wane wanda zai kaita makarantar ba. Kusan 5mins tana nan tsaye shikuma har sannan bashida niyyar gama abinda yake ko kuma kulata, fashewa Fattomah ta yi da kuka da ƙarfi, da sauri Imad ya juyo ya kalleta dan ganin abinda aka yimata

Tsabar baƙin ciki ji ya yi kamar ya jawota ya yi mata duka, a matuƙar fusace ya ƙaraso gabanta yana kallonta ƙirjinsa sai ɗagawa yake dan idan da Abinda ya tsana a rayuwarsa bai shige kuka ba ya tsani yaga ana kuka musamman yanzu da take masa kukan na rashin dalili, cikin wata shaky voice ya daka mata tsawa ya ce".

*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*

*Like nd share*[5/13, 9:30 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*

Ameenatou Nanameera

PAGE 25-26.
Chapter 13 · 0% Book details