← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankali tashe Fattomah ta ɗago idanunta ta kalli Daddy lokaci ɗaya hawaye ya game kyakkyawar fuskanta bakinta na rawa ta ce"Da..Dad.Daddy dan Allah ka barni anan gidan zan zauna ni kaɗai ko gidan yaya Jawaad kaji Daddy" yanda tayi maganar dole ta baka tausayi hakan yasa Daddy ya taso ya zauna gefenta ya kamo hannayenta cikin nasa ya ce"Fattum kiyi haƙuri kinji ki ɗauki Imad matsayin yayanki na tabbata zai kula dake koda kuwa bakuyin shiri sosai bazai yiwu ki zauna gidan Jawaad bane da can zaki zauna sannan bana son zamanki a fada shiyasa bance Muhammad ya tafi dake ba kiyi haƙuri zaman wata uku kawai zakiyi daga nan zaki dawo kuma Imad bazai cutar dake ba muddin baki saɓa masa ba kinji" cikin kuka ta riƙe hannun Daddy ta ce"Daddy wlh tsoronsa nake ji dan Allah karka barni wajensa wayyoo Allahna Daddy" rungumeta Daddy ya yi ahankali yake faɗa mata kalamai masu kwantar da hankali wanda duk suka saka jikinta ya yi sanyi, saida yaga tayi shiru gabaɗaya sannan ya ɗago fuskarta ya goge mata hawayen ya ce"karki damu kinji zan dinga kiranki mu gaisa kuma Imad zai dinga kawo ki one's in a tym saboda haka you don't need to worry dear"jinjina masa kai tayi ya shafa kanta ya ce"good gurl Allah ya yi miki albarka" a hankali ta ce"Ameen Daddy" miƙewa ta yi Mommy ta ce"ki je ki shirya zuwa anjima zamuje super market sai a siyamiki abubuwan buƙata"toh kawai Fattomah ta ce sannan ta shige ciki. Zama Mommy ta yi tana kallon mijin nata ta ce"wlh ina tausayinta" kallonta Daddy ya yi ya ce"akanme kuma?" numfasawa ta yi ta ce"bata saba da Imad ba kuma kasan Imad ko mutum ya saba dashi toh fa yanada wahalar sabo sannan gashi ita kanta matar tasa bawani alaƙa ce mai kyau tsakaninsu ba kaga kuwa kullum zata kasance lonely" tashi Daddy ya yi ya ce"babu wata mafitar ne sai wannan dole hakan za'a yi" "Allah ya rufa asiri" Ameen ya ce sannan ya yi waje.

Tunda ta shiga ɗakin take kuka bata taɓa jin kewar iyayenta irin wannan ranar ba tabbas da suna kusada ita to makamancin wannan abun bazai faru da'ita ba, da yanzu tana wajen iyayenta suna rayuwa cikeda farin ciki kamar yanda suka saba kowane lokaci Allah sarki rayuwa batada tabbas ko kaɗan bata taɓa tunanin rayuwarta zata juye zuwa haka ba sai gashi cikin ƴan watanni komai ya koma upside down, tasan zamanta gidan Imad tamkar ƙarewar farin cikinta ne domin ko kaɗan baya ƙaunarta wanda take sa ran farin ciki daga gareshi yaya Jawaad ne kuma gashi ya juya mata baya haka tayi ta saƙe-sakenta har akayi sallar azahar sannan ta tashi ta shige toilet dan shiryawa. Kamar yanda Mommy ta ce haka ya kasance karfe biyar suka isa super market ɗin, siyayya sosai sukayi Fattomah tana tsaye wajen ɗaukan chocolate saboda ƙaunarta da'ita kamar daga Sama ta ji ya ce

"Nima ki siya mini man"

Aɗan firgice ta juyo idanunta suka sauka kan Kamal wanda yake kallonta da murmushi afuskarsa, sunkuyar da kanta tayi ya ce"sannu ya kike kwana biyu?" kallonsa ta yi amma bata ce komai ba ya sake cewa"I'm sorry rannar na saka anyi miki faɗa nasan kiyi haƙuri kinji" sai a sannan ta ce"babu komai" murmushi ya yi ya ce"me zaki siya?" kamar bazata yi magana ba sai kuma ta ce"chocolate zan ɗauka" "can i help you?"shiru tayi batace komai ba ya fara zaɓar mata chocolates ɗin masu matuƙar tsada ita kuwa Fattum tsayawa ta yi tana kallon ikon Allah juyowa ya yi suka haɗa ido ta tuntsire da dariya tsayawa ya yi yana kallonta ganin yanda dariya tayi matuƙar yi mata kyau tabbas Fattomah kyakkyawace ajin farko. Murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"me kike yiwa dariya ne?" ta ce"wannan kayan na wane?" waro idanunsa ya yi ya ce"naki mana Fattomah" da sauri ta ce" a ina kasan sunana?" dariya Kamal ya yi ya ce "naji yayanki na faɗa rannan" jinjina kai ta yi sannan tabar wajen hakan yasa shima yabi bayanta.

"Meyasa kake bina ne nida Mommyna muka zo fa" Kalle-Kalle ya shiga yi ya ce"tana ina mu gaisa please" sakar baki Fattum ta yi tana kallon ikon Allah ganin da gaske Mommy ɗin yake nema su gaisa, haɗe rai ta yi tana kallonsa ta ce"nikam please banason abun kunya sai anjima" gaba tayi ya yi saurin biyota hakan yasa ta ƙara tsayawa ya ce"chocolates ɗin naki fa?" "bana so ni wanda na ɗauka sun isheni" girgiza kai ya yi ya ce"ko ki karba ko kuma naje har inda Mommynki take na baki agabanta sai ki zaɓa" Fattum ji tayi kamar ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka amma babu dama hakan yasa ta ce"Dan Allah idan ba so kake raina ya ɓaci ba kayi tafiyarka" murmushi ya yi ya ce"ki karɓa shine kawai zai ceceki" dafe kanta ta yi ta ce a shagwaɓe"idan Mommy tazo wajen nan kaida Allah wollah" dariya Kamal ya yi ya ce"kin shirya karɓa?" ganin da gaske ba rabuwa zai yi da'ita ba yasa ta gyaɗa masa kai a hankali, ya yi murmushi ya ce"good gurl". Saida ya biya kudin sannan ya koma ya cigaba da ɗaukan abinda ya kawo shi ita kuma ta koma inda Mommy take tsaye, sai gab da magrib sannan suka baro super market ɗin duk sun gaji saboda yawo, har suka zo gida babu wanda ya ce komai dan duk sunyi laushi....

Sosai Fattomah tayi mamakin irin kayan da Mommy ta siya mata dan ita bata ɗauka sunkai haka yawa ba kayana irin latest ɗin nan kuma unique kana gani kasan kuɗaɗe aka sa aka siyesu, duk yawancinsu ƙananun kaya ne sai abayas only fews ne traditional clothes saida ta gama ganin kayan sannan ta mayar ta ajiye ita kuma ta fito dan zuwa wajen Mommy, banda ƙamshi babu abinda parlon keyi ko'ina very cleaned and tidy, zama tayi kan royal cusion ɗin dake zagaye da parlon ta lumshe idanunta a hankali wata nutsuwa ke saukar mata,

Cikin wani babban gida wanda ya kasance kamar lambu ko'ina iska mai daɗi ke kaɗawa wasu irin kyawawan furarrani ne ke zubowa kamar irin a film ɗin, da sauri Fattomah ta tafi wajen Abbanta wanda yake kallonta yana sakar mata murmushi faɗawa jikinsa ta yi ta fashe da kuka cikin shagwaɓa take cewa"Abbana meyasa ka tafi ka barni?, banajin daɗi Ababana gashi Ammi ma tayi tafiyarta sai ni kaɗai banida kowa Abbana dan Allah kadawo kaji" shafa fuskarta Abba ya yi ya ce"Faɗeematoh rigima, kiyi haƙuri kinji tabbas akwai ƙalubale sosai a rayuwarki amma inason ki kasance mai juriya akowane irin hali kika tsinci kanki kada kiyi ƙasa a gwuiwa, ki zama mai jin magana Faɗeemah domin shine farkon abinda zai haddasa miki matsala cikin rayuwarki ki daina rashin jin magana kome ya faru watarana zai yi ƙarshe kuma kece wacce zaki ci riba ki ƙara haƙuri akan wanda kike dashi Faɗeemah komai ya yi farko zai yi ƙarshe"

"A'a Abbana kada kace haka Please ka dawo wajena dan Allah Abba!!!"

Da mamaki Mommy take kallonta ta ce"Fattum kedawa?" A firgice ta buɗe idanunta tana zazzaresu, kallonta Mommy ta yi ganin yanda take haɗa gumi dukda AC dake faman aiki cikin parlon ita kuwa Fattomah ta kasa gane abinda yake shirin faruwa da'ita ashe daman mafarki take ba gaskiya bane?, da gaske Abba ya mutu kuma bazai dawo ba?, mene ne abinda Abba ke ƙoƙarin faɗa mata???, rasa abinda zata yi yasa kawai ta fashe da kuka tana riƙe kanta wanda take jin yana mata wani irin ciwo. Zama Mommy tayi gefenta ta dafata ta ce"Fattomah lafiya meya faru?" kasa magana Fattum ta yi sai kukanta data cigaba, rungumeta Mommy tayi ta ce"dan Allah ki yi hakuri ki daina wannan kukan karki zo kina rashin lafiya kinji kiyi shiru" sosai Fattomah tasha kukanta kafin daga bisani tayi shiru ta koma sauke ajiyar zuciya har bacci ɓarawo ya yi gaba da'ita.

A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga tana ɗan Kalle-Kalle, zaune ta ganshi kan kujerar dake gefen gadon da alama ya yi nisa cikin duniyar tunani dan bai ma san ta shigo ba, zama Ayrah ta yi kan gadon a hankali ta ce"Doctor!" ko kallonta bai yiba wanda ya sake tabbar mata dacewa tunanin yake har sannan sauke idanunta ƙasa tayi cikin sanyin murya ta ce"Doctor dan Allah ka daina wannan tunanin da kake please" ganin har sannan bai juyo ba yasa ta miƙe ta ƙarasa inda yake, saida ta taɓa shi sannan ya kalleta aɗan firgice ya ce"Ayrah lafiya?" numfasawa ta yi ta ce" ka tashi mu ci abinci please" gyaɗa mata kai ya yi ya ce"I'm coming" girgiza kai ta yi ta ce"kawai ka tashi muje idan ba haka ba zama zaka sake yi" murmushi ya yi sannan ya kama hannunta suka fita daga ɗakin.

Banda kuka babu abinda Fattomah keyi ta ruƙunƙume Mommy sai kuka take kamar ranta zai fita ita kanta Mommy ƙarfin hali kawai take dan tana matuƙar jin Fattomah aranta, ganin abun nasu ba mai ƙarewa bane yasa Daddy yazo ya janyeta daga jikinta yana kallon Fattomah ya ce"ya isa haka dear zaki dinga zuwa you don't need to worry kinji"tana kuka ta ce"Daddy ku tafi dani" murmushi ya yi ya ce"shikenan next week Imad zai kawo ki kinji" kallon Imadudden ya yi ya ce"please ka kula da'ita yanda ya kamata tym to tym kana kawota"Okay kawai Imad ya ce sannan ya yi gaba, kallonta Jawaad ya yi ya ce"ki yi shuru mu tafi gida" gyaɗa masa kai tayi sannan ta bar wajen su Mommy akan idanunsu jirginsu Mommy ya tashi zuwa garin Abuja, wani sabon kukan taji yana neman kwace mata Jawaad ya riƙe hannunta suka fara tafiya, back seat ya buɗe mata ta shiga sannan ya shiga gaba Imad ya yiwa motar key bakinsa ɗauke da Bismillah suka bar Airport ɗin, a hankali ya gangara gefen hanya ya yi parking da mamaki Jawaad ya kalleshi kafin ya yi magana ya juya yana kallon Fattomah ya ce"whether you keep quiet or get out okay?" a hankali ta fara rage sautin kukan nata tsaki ya yi sannan ya ci-gaba da tafiya batareda ya sake cewa komai ba.
Chapter 12 · 0% Book details