← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.

PAGE 11-12.

Buɗe dara-daran idanuwanta tayi tana kallon inda take kwance itadai tasan ba anan ta kwanta ba, buɗe ƙofar ɗakin akai yasa ta kalli ƙofar dan ganin wanda yake shigowa cikin sassarfa ya ƙaraso gare ta yana kama hannayenta duka biyun ya ce" ya jikin naki Fattum?" kwaɓe fuska tayi cikeda shagwaɓa ta ce" da sauƙi yaya, ina nake nan?" ajiyar zuciya ya sauke wacce shima bai san ya yi hakan ba ya ce" Allah ya ƙara lafiya ya kiyaye gaba Fattomah" shuru tayi tana kallonsa ganin kamar a dame yake ta ce" yaya ina Mommy?" murmushi ya yi ya ce" tana gida kema yanzu zamu tafi" "to ina muke nan?" dafe kansa ya yi ya ce" wayyo Fattum magana dai?, gidan Imad ne toh shine ya ɗauko ki" sosai taji gabanta ya faɗi dan harga Allah tsoro yake bata kwata-kwata batasan haɗa shirgi dashi lura da yanda ta tafi duniyar tunani yasa Jawaad ya ce" keeee!" a ɗan firgice ta ɗago tana kallonsa tana langwaɓar da kai ta ce" yaya kabani tsoro" yanda tayi maganar ne yasa shi tuntsirewa da dariyar da baiyi niyya ba murmushi itama tayi daidai nan Imad ya shigo ɗakin, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai yana zuwa ya zare mata drip ɗin hannunta batareda ya kalleta ba fashewa tayi da kuka dalilin zafin da taji shi kuwa gogan ko a jikinsa dan bama zaka ɗauka yana ɗakin ba

"Kayi mata a hankali mana"

Wani irin shegen kallo Imad ya watsa masa sannan ya cigaba da abinda yake, saida ya gama tass sannan ya juya yayi fitarsa bai sake bi takansu ba, riƙe mata hannu ya yi ya ce" sorry dear zo mutafi gida kinji zan siya miki abin daɗi" dakyar ya lallaɓata tayi shiru sannan suka fito daga ɗakin yana riƙe da hannunta. Babu kowa a parlon sai tv dake aiki hakan yasa kawai ya yi waje tana biye dashi, tsaye suka taddashi jikin mota yana magana da wani maid ɗinsa suna zuwa bai ce komai ba ya shige motar ya fuskanci abinda yake nufi yasa ya kalli Fattomah wacce har sannan bata wani jindaɗin jikinta ya ce" shiga baya kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan ya buɗe mata backseat ɗin ta shiga shikuma ya shiga ɗaya side ɗin ya rufe motar, bakinsa ɗauke da Bismillah ya yiwa motar key suka bar gidan.

Saida sukayi nisa sosai sannan Jawaad ya ce" wai yaushe ne zaka koma America?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" randa Ubangiji ya hukunta" murmushi Jawaad ya yi ya ce" tom Allah ya yarda" lumshe idanunsa ya yi dalilin wani uban traffic da aka haɗa ahanyar, kusan 5mins kafin su samu su shige daga wajen yana shan kwanar round about ɗin ya ce" nikam halin ƙasar nan na ɓatamin rai komai babu tsari abunfa it's too much" dariya kawai Jawaad ya yi ya ce" dole kaga haka tunda ka daɗe rabonka da ƙasar amma da kasa ba zakaji ba komai ba" tsaki Imad ya yi ya ce" Allah ya kyauta" "Ameen".

Da sallama suka shiga ɗakin yana kallon yayan nasa, zama ya yi gefensa yana kallonsa ya ce" yaya ya jikin naka?" gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi domin yanda jikinsa ya yi zafi ko magana ma ya gagara ya yi, tashi Daddy ya yi ya ƙarasa wajensa yana zuwa ya rike hannunsa cikin rauni da kuma dashewar murya yake cewa" kulamin da Faɗimatoh ka aurar min da'ita inda zata samu kwanciyar hankali ka riƙe mini ita amana karka bari wani abu mara kyau ya samu rayuwarta ina matuƙar ƙaunarta dan Allah ka cigaba da kulawa da rayuwarta daga inda na tsaya na tabbata Faɗima bazatayi maraiciba indai kana tare da'ita kuma...... Salƙafewa maganarsa tayi lokaci ɗaya ya hau wani irin tari kamar zai fasa ƙirjinsa, da sauri duka suka taso sukayo kansa Daddy Kabeer ne ya ce" sannu kaji yaya Allah ya baka lafiya" ƙam Abba ya rike hannunsa yana magana dakyar ya cigaba da faɗin"dan Allah ku riƙe min Fateema amana ku aurar min da'ita inda za'a kula da rayuwarta domin na sani yarinyar tanada rauni kuma bataji amma tanada tarbiyya daidai tata dan Allah ku tai....... tai. La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi Sallallahu alaihi Wasalla.."

"Doctor!!! Doctor!!! Doctor!! Yaya!! Yaya!!"

abinda Daddy yake faɗa kenan yana jijjiga ɗan uwan nasu hankalinsa ya yi matuƙar tashi Ammi kuma mutuwar tsaye tayi dan tama kasa ƙarasawa inda yake, da sauri likitocin suka shigo suka rufa akansa hakan yasa su Daddy suka fito daga ɗakin jikin kowa asanyaye sai addu'a suke a zuciyarsu, kusan 35mins sannan likitocin suka fara fitowa, da sauri Daddy ya tafi yana zuwa ya riƙe wani doctor ya ce "ya jikin nasa?" kallonsa kawai doctorn ya yi sai kuma ya ce"I'm sorry sir mun rasashi Allah ya karɓi abinsa saidai haƙu..... bai tsaya sauraren abinda zai ƙarasa faɗa ba ya shige ɗakin da sauri turus ya yi ganin Abba kwance sun rufe masa fuskarsa jikinsa na wani irin kyarma ya ƙarasa gabansa yana zuwa ya riƙe hannunsa a hankali ya zame gyallen, kifa kansa ya yi akan jikin Abba ya na hawaye rabonda ya zubarwa hawayensa har ya manta sai yau dalilin mutuwar Abba tabbas Abba ya yi kyakkyawan ƙarshe sai fatan Allah Ubangiji ya jiƙanshi da Rahama 🤲🤲.

Convey ɗinsa ne suka fara shigowa sannan suma suka shigo lokacin Fattomah na kitchen tana taya maid aiki dan idan batada abinyi kitchen take shiga, miƙewa Mommy tayi ganin an shigo da wani abu kamar mutum arufe kasa magana tayi dan duk tarasa abinda zata yi, Uncle Mansoor ne ya zauna gefen kujerar saboda wani irin sarawa da kansa ke masa Kalle-Kalle ta shiga yi ganin babu wanda yake komai cikinsu duk sunyi shuru, Imad ne ya shigo da sallama Jawaad na bayansa sai matarsa wacce suka tawo tare da niyyar gaisheda Mommy. Da mamaki Jawaad yake kallonsu sai kuma ya kalli gawar dake kwance nan ƙasa cikin rawar baki ya ce" Dad...Daddy..D.. Daddy waye wannan?" kallonsa sukayi duka atare sai kuma sukai shiru, ahankali kamar me tsoron taka ƙasa ya ƙarasa gaban gawar ya tsuguna tamkar an tilasta masa ya buɗe fuskarsa dan gani waye haka, wata irin ƙara da ta saka yasa duka suka juya suna kallonta kafin su ƙarasa ta waɗi ƙasa sumammiya.....

Allah Sarki rayuwa ayau akai sadaƙar bakwan mutuwar Abba wanda ya yi daidai da ranar juma'a, zaune take ta ɗora kanta kan cinyar Ammi banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa domin kukanma ya gagara kasawa take duk ta rame ta fice hayyacinta kamar ba Fattomah ƴar rigima ba tunda randa aka sallamota a asibiti bata kula kowa ba duk irin maganar da zaka yimata kuwa sai kuka dan ko abinci taƙi taci hatta Ammi ta gaji ta rabu da'ita domin duk irin yanda taso ta shawo kanta kasawa tayi, yanzuma tayi shuru tana tunanin Abbanta wanda shine abinda take kwana tana yi Mommy ce ta shigo ɗakin da sallama tana zuwa ta zauna gefen Ammi tana kallon Fattomah ta ce

"Dan Allah dan Annabi Faɗimatoh kiyi haƙuri ki yiwa Abbanki addu'a kinji wannan kukan bashi da amfani ki daina dan Allah" kamar wacce ta zugata haka ta sake fashewa da kuka kamar ranta zai fita rungumeta Mommy tayi tana shafa kanta ta ce" ya isa haka stop crying Baby kiyi masa addu'a" cikin kuka Fattum ta ce" Mommy Abbana ya tafi ya barni Mommy inason Abbana dan Allah Abbana ya dawo wajena kice masa karya tafi ya barni zanta yin kuka bazan daina ba ni inason Abbana Fattomah tanason Abbantaaa" hawaye suma sukeyi domin yanda take kukan sai ta baka tausayi tabbas Fattomah ta saba da mahaifinta kuma tana matuƙar ƙaunarsa kamar yanda shima yake nuna mata wannan soyayyar dan tafi jinsa azuciyarta fiye da Amminta gashi yanzu ta rasashi rasawa irinta har abada. Baccine ya ɗauketa tana cikin wannan kukan Mommy ta kwantar da'ita sannan ta kalli Ammi ta ce" dan Allah A'isha ki ƙara haƙuri karki dinga damun kanki addu'ar ku yafi buƙata yanzu fiye da kukan please" ajiyar zuciya Ammi tayi tana share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata ta ce" Nagode Hajiya amma bazamu taɓa mantawa dashi ba domin shiɗin ba kamar sauran maza yake ba yanada halaye wanda ba kowane namiji yake dasu ba ya kula da rayuwarku cikin walwala dakuma tsanani, yana ɗaukan iyalansa tamkar duniyarsa bashi da damuwa indai yana tare damu kuma muma da haka muka tashi wlh har abada bazamu taɓa mancewa dashi ba Allah Ubangiji ya jiƙansa da Rahama" dafata Mommy tayi ta ce" nasani amma dole sai kun cire tunaninsa cikin ranku sannan zaku cigaba da gudanar da rayuwarku Allah ya gafartamasa" "Ameen ya rabbi".
Chapter 6 · 0% Book details