Sashe 10
Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyowa tayi tana kallon wanda yake mata sallama dan ita dai tasan ita kaɗai ta fito batareda wani ba kuma babu kowa a wajen da take, idanu biyu sukayi da Kamal wanda yake sakar mata wani kyakkyawan murmushi, shuru Fattomah ta yi ba tace komai hakan yasa ya ce"haba baiwar Allah ko bazaki kulani ya kamata ace kin amsa sallama a matsayinki na musulma ko?" shiru ta yi sai kuma ta ce "wa alaika salaam" murmushinsa mai kyau ya yi ya ce"yawwa nagode sosai" bata sake ce masa komai ba kusan 2mins hakan ya sa ya ce"dan Allah idan bazaki damu ba kibani number wayarki idan yaso sai nazo gidanku later" da sauri ta kalleshi taga ya kashe mata ido ɗaya saurin ɗauke kanta ta yi sai kuma ta ce a hankali"nikam karka dameni please" dariya Kamal ya yi ya ce"toh Madam ai girmanki ne yanda kika ce haka za'a yi" taɓe baki Fattum ta yi dan har cikin ranta ya fara damunta da magana gashi babu alamar napep a hanyar daman kuma titin ba'a fiye samunsu ba duk sai motocin gida, numfasawa ta yi sai kuma ta ce"nifa ka tafi please kada ma wani ya ganmu tare" Kamal ya ce"idan baki so aganmu a hanya kibani address naki sai nazo nima banason tsayar dake akan hanya ko kuma ki shiga motana na kai ki inda zaki sai mu ƙarasa maganar" wani kallon kayi hauka Fattomah ta watsa masa sannan ta ce" Allah ya kiyaye na shiga motar namiji har abada" girgiza kai Kamal ya yi sai a sannan ya fahimci cewa yarinya ce kuma daman auran irin su shine muradin zuciyarsa tabbas sai ya mallaketa matsayin matarsa. Ganin lokaci na tafiya yasa ya ce"ki bani number kin ji dan Allah" ajiyar zuciya ta sauke kusan 2mins sai kuma ta fara karanto masa numbern wayartata,
"Fattomah!"
Aɗan firgice ta juya inda sukayi 4eyes da yaya Jawaad sai taji gabanta ya faɗi dukda bawai tsoronsa take jiba kuma tasan babu abinda zai mata amma sai taji kamar bata kyauta ba, kallonsa Kamal ya yi sai kuma ya kalleta ya ce"Kinsan shi ne?" gyaɗa masa kai tayi tana sauke kanta ƙasa cikin sassarfa ya ƙaraso wajen without looking at her ya ja hannayenta kasa cewa komi Fattomah ta yi har ya sanyata amotar sannan ya shiga cikin ƴan sakwanni suka ɓace daga wajen, da kallo Kamal ya bisu har sukayi disappearing a wajen kallon wayarsa ya yi yaga ta gama sanya masa numbern hakan yasa bai damu ba ya koma tasa motar shima yabar wajen.
Har suka je gida Jawaad bai ce mata komai ba amma kana ganinsa kasan ransa a ɓace yake, yana gama parking ya fice daga cikin motar bai ko kalleta ba samun kanta tayi da kasa fitowa daga cikin motar dan ko ba'a faɗa mata ba tasan yaya Jawaad fushi ya yi da'ita ga abinda ya faru ɗazu ita da Ayrah shiyasa ma tabar gidan bata jirasa ba, kusan 10mins tana cikin motar kafin a hankali ta fito daga ciki ta shiga cikin gidan kamar wacce kwai ya fashewa ajiki.
Bataga kowa cikin parlon ba hakan yasa Kawai ta shige bedroom ɗinta dan daman batason haɗuwa dashi, har akayi sallar magrib Fattomah bata fito ba, kwata-kwata ta kasa fitowa parlon gudun kada ta haɗu da yaya Jawaad ga wata uwar yunwa da take ji dan rabonta da abinci tunda tayi breakfast ganin babu sarki sai Allah ya sanya ta sakko daga kan gadon ta ɗaura veil ɗinta sannan ta fito parlon tana ƴan kalle-kalle, gabanta taji ya faɗi ganinsa da tayi zaune kan kujera 2seater yana operating laptop ɗinsa kasa ƙarasowa gabansa tayi unlike da da take zama tana kallon abinda ya ke yi suna hira, ji tayi wasu hawaye sun zubo mata ta sanya hannuta ta share sannan ta shige cikin kitchen ɗin da sauri ta fito ganin Ayrah tsaye da alama abinci take dafawa, rasa inda zataje tayi hakan yasa a hankali kamar me koyan tafiya ta ƙarasa gaban Jawaad.
Tsugunawa ta yi daidai wajen ƙafafunsa cikin rawar murya ta ce" yaya Jawaad" shuru ya yi mata babu reply badan bai ji abinda ta ce ba, sau uku tana kiran sunansa amma ya ƙi amsawa wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, cikin sanyin murya da kuma rauni take cewa
"Dan Allah dan Annabi yaya Jawaad kayi haƙuri wlh ba laifina bane ko kulashi banyi ba dan Allah yaya" rufe system ɗin gabansa ya yi sannan ya zuba mata narkakkun idanunsa akanta, sunkuyar da nata tayi dan bata iya jure kallonsa, kusan 3mins suna haka sannan ya ce"wane shi?" girgiza masa kai tayi ta ce"wlh ban sanshi ba" "amma kike kulashi har kike ganin kin isa tsayawa da samari akan titi daman irin tarbiyyar da aka miki kenan?" girgiza masa kai kawai take dan ta gagara magana batasan da wani harafi zata yi masa bayani ya fahimceta ba sai faɗa yake mata akan abinda bata da laifi, cikeda masifa wacce batasan Jawaad ya iyata ba yake cigaba da faɗin
"Wlh Fattomah duk ranar dana sake ganin kamamancin wannan abun ya faru nayi miki alƙawarin ɓata miki rai irin wanda ba'a taɓa yi miki ba, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci daga ke har shi shegen wanda kike kulawar, har yaushe kika yi girman kula saurayi nawa kike?, You Are just 15yrs amma kina tunanin namiji kodan kin ganki da girman jiki?, toh ki sani ko nan da 2yrs baki isa barinki tsayawa da wani ƙato ba bare yanzu shashasha kawai get out of my side"
Da sauri ta tashi har tana ƙoƙarin bigewa ta shige bedroom ɗinta tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananci kuka, kallonsa Ayrah ta yi bayan ta ajiye food flask ɗin hannunta ta ce"doctor lafiya?" tsaki ya yi ya ce"babu komai" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"haba dan Allah ai tunda naga kana wannan faɗan dole akwai abinda ta aikata dan Allah ka sanar dani" numfasawa ya yi sannan ya bata labarin abinda ya faru briefly. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke ta ce"toh akan wannan kake ta faman faɗa doctor macace fa dole daman ai maza su biyota musamman Fattum" wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"Eh tunda ita mace akuyace da ake barinta sakaka ke kina kamar shekarunta aka fara barinki tsayawa da samari?" Murmushi ta yi ta ce"Allah ya baka haƙuri yallaɓai ni da wasa nake, saida na kammala secondary school na shiga University sannan Daddy ya fara barinmu" harararta ya yi ya ce"okay shine ita kike son abarta tun yanzu ko?" girgiza kai tayi ta ce"tuba nake dear" murmushi ya yi sannan ta fara serving nasa.
Tashi tayi duk idanuwanta a kumbure dalilin kukan data kusan kwana tanayi, a hankali ta sakko daga saman without making any sound ta fice daga parlon, ko kallon masu gadin gidan bata yi taje ta buɗe ƙofa tayi fitarta, cikin Sa'a ta samu wani napep ya shiga ɗaukan ƴan makaranta ta faɗa masa inda zata ya ce to tahau suka tafi.
Murmushi ta yi ta ce"kayi kyau sosai doctor" jan kumatunta ya yi ya ce"kema haka dear" dariya ta yi ta ce"mu tafi?" girgiza kansa ya yi ya ce" kirawo Fattum" haɗe rai ta yi sai kuma ta juya ta shige bedroom ɗin da take, kalle-kallenta ta gama ta fito tana kallonsa ta ce"dear bafa ta cikin ɗakin" da mamaki Jawaad ya ce"kamar ya?" ɗaga masa kafaɗa tayi alamar bata sani ba, da kansa ya shiga ɗakin dan tabbatar da gaske Fattomah bata ciki ɗin, tsaki ya yi sannan ya fita wajen masu gadi zuwa sannan hankalinsa ya fara tashi yana zuwa ya kalli gateman ɗin ya ce"kai ina kaga Fattum?" cikeda ladabi yake cewa" yallaɓai naga sanda ta fita ina yi mata magana taƙi kallona wajen 3hrs kenan" da mamaki Jawaad yake furta kalmar ta fita ɗin toh ina ta tafi da safiyar nan da sauri ya shiga motarsa Ayrah ma ta shiga sannan suka bar gidan.
*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*
*Like nd share*[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.
PAGE 19-20.
A hankali yake ƙarewa farfajiyar gidan kallo wacce ta kasance iya ganinka sosai ya yi mamakin ganin fadawa a wajen kenan mai martaba yazo???, kama hannun Ayrah ya yi wacce itama take kalle-kallenta suka shiga cikin gidan. Zama ya yi aƙasa bayan sunyi sallama cikeda ladabi ya gaida iyayen nasa kallona Uncle Kabeer ya yi ya ce"son meyasa ka makara Faɗeemah ta ce kuna bacci ta tawo?" Jawaad ya ce"Eh wlh Abba naɗan tsaya yin wasu abubuwa ne shiyasa"okay ya ce sannan ya kalli Imad wanda tunda ya shigo bai ce komai ba ya ce"kaifa goga?" ɗan murmushi Imad ya yi amma bai ce komai ba, mai martaba ne ya yi musu addu'a sannan ya fara cewa
"Kamar yanda kuka sani mun tara wannan taron ne saboda sanar daku abinda ku baku saniba da kuma irin hukuncin da muka yanke a tsakaninmu"
Shiru kowa na parlon ya yi dan jin abinda zasu faɗa Uncle Mukhtar ne ya cigaba da faɗin
"Kunsan yaya zai bar garinnan zuwa Friday sannan kuma Fattomah tana karatu cikin garin nan bazai yiwu ya tafi da ita ba saboda haka muka yanke shawarar zata zauna gurin ɗaya daga cikinku wanda kuma Imad kaine wanda zata zauna cikin gidanka"
Da wani irin expression Imad ya ɗago kai yana kallon Uncles ɗin nasa ba shi kaɗai ba harda su Adda da Fulani Jawaad kuwa mutuwar zaune ya yi, kasa magana Imad ya yi amma banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa ke yi baya jin zai iya zama gida ɗaya da wannan mara hankalin yarinyar ba wacce batada nutsuwa ko kaɗan cikin lamuran rayuwarta tabbas saidai idan ta zauna gidan Jawaad amma ba nashi gidan ba, gyaran murya mai martaba ya yi sannan ya cigaba da faɗin
"Kasan kuma bazai yiwu ace anbar yarinya budurwa ta zauna cikin gidanka ba kuma ba muharramar kaba tabbas anyi ganganci bawai dan ba'a yarda da kai ba a'a saboda ita rayuwa abar tsoro ce za'a iya zuwa mas'asal da ake buƙatar muharraminta awajen kuma babu, saboda haka muka yanke shawarar aura maka ita yanda duk abinda zai je ya dawo babu tashin hankali ko fargaba aciki"