Sashe 2
Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru Fattomah ta yi tana cigaba da kukanta dan ita kaɗai tasan abinda takejin a jikinta gashi batason shan magani kuma batason taje gida Abbanata yaga alamun an daketa, goge idanunta tayi batareda ta cewa kowa komai ba ta miƙe ta fice daga cikin class ɗin da idanu Maa Zainab ta bita sai kuma ta girgiza kai cikin ranta ta ce"Allah ya shiryeki Fattomah".
Ɗakinta ta shige a hankali gudun kada Ammi ta fito tsakar gidan ta ganta tana shiga ta zare hijab ɗin jikinta sannan ta zauna kan katifarta tana ƙarewa jikinta kallo sosai jikinta ya kumbura duk ya yi Ja dukda ita ba fara tass bace amma tanada haske sosai, hawayene ya shiga biyowa kuncinta tana tsinewa malamin aranta dan ita ba taga abinda tayi masa ba dazai daketa
"Fattum!! Fattum!!"
Da sauri ta kalli ƙofar ɗakin jin Ammi na kiranta ko yaushe taga shigowarta????, Jin yanda take ƙara kiranta yasa ta miƙe a hankali ta maida hijab ɗinta sannan ta fito tana kalle kalle, "shine ki ka shigo babu sallama sai takalmanki na gani ko?" turo baki ta yi ta ce" koba nayi sallamar ba" girgiza kai Ammi ta yi ta ce" a yaushe ki kai sallamar banason ƙarya" zumɓura baki ta yi ta ce" shikenan naji ban yiba ay mantawa nayi" taɓe baki Ammi ta yi ta ce" ke kika sani ki shige ki cire kayan nan kizo zan aike ki" da sauri ta kalleta sai kuma ta langwaɓar da kai ta ce" ayyah Ammi ina zaki aikeni kina ganin yanda ake rana a garin nan" sakar baki Ammi ta yi tana kalllonta har takai ƙarshen maganarta Sannan ta ce
"Ohhhh nufi kike bazaki ba ko me?"
Girgiza kanta ta yi ta ce"Ni ba cewa nayi bazani ba ai zani mana" harararta ta yi ta ce" Allah ya baki sa'a Fattum karki daina rashin jin magana" bata sake cewa komai ba ta juya ta shige ɗakinta ita kuma ta tura baki gaba sannan ta koma ɗakin dan cire kayanta.
Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta yadi wanda akayi ɗinkin straight gown milk colour ta sanya mayafi baƙi sannan ta fito tana tafiya kamar bataso daman indai ƙiwa ce tofa Fattomah number 1 ce a wannan fagen.
Tsugunawa ta yi gefen Ammin tana kallon rai a haɗe ko kallonta Ammi batayi ba ta miƙa mata leda tana cigaba da aikinta ta ce"kije ki kaiwa Adda kice mata wai ankon bikin Hafsa ne" ƙoƙarin buɗe ledar ta shiga yi Ammi ta ce
"Wai ke mene ne yake damunki ko ajiya kika bawa mutane da kike ƙoƙarin buɗewa?"
Rufe ledar ta yi sannan ta miƙe tana kallon Ammin ta ce" Ammi kuɗin mota" a fusace ta ce" kuɗin jirgi zan baki bana mota ba a gidan ubanki zakiga masu mota a hanyar" da sauri ta fita waje tana zuwa soron gidan ta fashe da kuka, da gudu tayi waje ganin Ammi ta nufo soron haka har ta fita layin nasu tana haki tana juyowa taga ko ta biyota abaya.
Ita kuwa Ammi addu'ar neman shiriya ta roƙa mata wajen Ubangiji dan lamarin Fattomah har tsoro yake bata yarinya kamar wacce ke mu'amala da aljanu
*FATTOMAH isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 8106571862*
*Nanameera ce#*
[5/3, 4:20 PM] Nanameera: * FATTOMAH*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.
* PAGE 3-4*
*Nanameera ce#*
Tafiya take kamar bataso har ta ƙara so bakin layin gidan da Ammi ta aiketa
"Fattum!"
Da sauri ta juya dan ganin wanda yake kiran sunanta, murmushi ta saka tana washe baki ta ce"laaa yaya Aslam ina yini" murmushin shima ya mayar mata ya ce" lpyklao Fattum ya Ammi?" "Tana nan klao gidanku ma zani" waro idanunsa ya yi ya ce"dagaske?" gyaɗa masa kai tayi tana wasada ledar hannunta ya ce" okay tom dama nima can zanje sai mu tafi tare" toh ta ce masa sannan suka cigaba da tafiya yana janta da hira har suka iso gidan nasu. Murmushi Adda ta yi ta ce" Faɗimatoh yaushe rabonki da gidan nan?" sunkuyar da kanta Fattomah ta yi tana ɗan murmushi Aslam ya ce"wlh kam Mama rabonda naga Fattum har na manta ta ɓuya abinta" turo baki ta yi ta ce"ayyah yaya naga mun haɗu dakai rannan" "a makaranta ba" dariyarta mai kyau ta yi ta ce"ai dai mun haɗu ko Mama?" murmushi Mama ta yi ta ce" nikam nayi fushi dake" kwaɓe fuska ta yi ta ce"Hajiya Adda Mamata nasan ai kin haƙura zaki dafamin dambu ko?" Tuntsirewa sukai da dariya Mama ta ce"shikenan zan dafa miki amma ai kwana zaki yi ko?" girgiza kanta ta yi ta ce" A'a Mama ban faɗawa Abbana ba kuma kinsan faɗa zai yimin" haɗe rai Adda ta yi ta ce"saboda baisan gidan wa kika kwana ba?" shuru Fattomah ta yi Aslam ya ce"kawai kiyi zamanki kinga yanzu su Abla zasu dawo daga makaranta" narai-narai ta yi da idanu dan kwata-kwata hankalinta bai kwanta data kwana ba domin batason abinda zai ɓatawa Abbanta rai ko ya yake,
Da gudu tazo ta rungumeta tana dariya ta ce" oyoyo sister sai yau?" murmushi Fattomah ta yi ta ce"wlh fa kowa ya ɓuya ina Khaltum?" Zama Abla ta yi gefenta ta ce"wai laifi suka yiwa Sheikh ɗinsu shine ya ce bazai tashesu ba sai anyi magrib kinsan kwata-kwata ƴan ajinsu basaji" jinjina kai Fattomah ta yi ta ce"okay bari ta dawo" "amma dai kwana zakiyi?" girgiza kanta tayi, tsaki Abla tayi ta ce"lailai ma ƴar nan mu amma muke zuwa gidanku mu kwana ko?" murmushi tayi ta ce"kiyi haƙuri sister in Sha Allah zan dawo na kwana soon kinga akwai makaranta gobe kuma zamu haɗu wajen biki" "saboda haka ne bazaki kwana ba?, dan Allah ki kwana kinji Fattomah" ajiyar zuciya Fattomah ta sauke sannan ta ce" amma gobe da wuri zan tafi gida" murmushi Abla ta yi ta ce"Eh to Allah ya kaimu", tashi tayi tana kallonta ta ce"toh uwar san jiki sai ki tashi muje ɗaki" murmushi Fattomah ta yi sannan ta miƙe ta kama hannunta suka shige ɗakin nasu.
Haɗe rai tayi tana kallon Khaltum ta ce"toh mene ne amfanin kula saurayi bayan kinsan ba aurensa zakiyi ba?" wani irin kallo Khaltum tayi mata ta ce" lailaima Fattum wato ke zama zakiyi babu wanda zaki kula?" murmushi Fattum tayi ta ce" Allah ya kiyaye wlh babu ruwana da kula wani mutum bayan nasan ba aurensa zanyi ba kuma ba aurenma za'ayi min yanzu ba kinga kuwa babu amfani" harararta Abla tayi ta ce"ai sai kiyita zama hajiyata" tuntsirewa tayi da dariya tana kallonsu ta ce"Allah ya kaimu lokaci musha biki" "Ameen Ameen" suka amsa mata atare.
Washegari tana tashi bayan sun gama shiryawa ta fito tana gyara mayafinta, kallonta Khaltum ta yi ta ce" wai ina zaki ne?" murmushi ta yi ta ce"gida mana" sakar baki tayi ta ce" ke kuma sai kace ana korarki zaki tafi ƙarfe nawa yanzu?" Mama ce ta shigo tana kallonsu ganin yanda sukayi curko-curko a tsaye ta ce" lafiya dai?" Khaltum ce ta ce"wai tafiya zatayi da wannan safiyar sai kace muna korarta" murmushi Mama tayi ta ce" haba Fattomah sai kace baki sanmu ba?, kibari anjima zai ki tafi" shuru Fattomah tayi amma har cikin ranta bataji daɗi ba domin tafi son tafiya gida fiye da zama anan kuma taji hankalinta bai kwanta da zaman ba. Misalin ƙarfe 2pm ta shigo cikin layin nasu da mamaki sosai take ƙarewa motocin data gani a bakin layin kallo domin kana gani kasan masu tsada ne bata ƙara tsorata ba saida taga wasu mutane masu kamada samudawa tsaye ƙofar gidansu kowanensu da bindiga atare dashi duk sun sanya wasu baƙaƙen kaya da glasses, da sauri ta shige gidan nasu tana waiwayon mutanen ta gani ko biyota suka yi.
Da mamaki ta tsaya daga bakin ƙofar shiga tsakar gidan nasu tana kallon mutanen da suke zaune kan tabarmar sai kuma Abbanta wanda yake kwance daga gefe shima, kasa ƙwaƙwƙwaran motsi tayi daga inda take dan ita bata ganewa wannan abun ba bata taɓa ganin mutane irin haka ba kuma bata taɓa ganin Abbanta a kwance irin haka ba
"Fattum"
Kallon Ammi tayi wacce ta faɗi maganar ganinta da tayi kamar a tsorace da hannu tayi mata alama da tazo ta tafi cikin tafiyarta ta sanyi kamar kowane lokaci, zama tayi gefen Ammi tana kallon Abbanta wanda idanunsa suke a lumshe juyawa tayi kuma tana kallon manyan mutanen da suke zaune kan tabarmar suma kana ganinsu kasan masu arziƙine kuma jinin sarauta kowanne sun yana ji da kansa kuma ba yara bane domin Zasu iya girman Abbanta dukda kasancewarsa mai yawan shekaru, sunkuyar da kanta ƙasa tayi dan ita bata gane mene ne abinda yake faruwa ba kuma batasan wnada zai mata bayani game da hakan ba, tsinkaya tayi yana cewa
"Wannan ita ce yarinyar taka?"
Gyaɗa masa kai Abba ya yi har sannan kuma idanunsa a rufe suke ita kuwa Fattomah kallo kawai take binsu dashi ya ce" ya sunanki?" "Fattomah" ta bashi amsa a taƙaice"Masha Allah nice name dear" shuru tayi ta juya ta kalli Abbanta sai a sannan ta ce
"Abbana mene ne ya sameka?"
Riƙe hannunta ya yi cikin nasa yana magana da kyar ya ce" Faɗimatoh ki kula da kanki kinji ki riƙe tarbiyarki ki zama mai jin magana ga kowa ki daina rashin jin magana dan Allah Faɗimatoh" bakinta na rawa ta ce" Abbana bazan sake ba kaji kayi haƙuri wlh Adda ce tace saina kwana amma ban ƙarawa" tallafo fuskarta ya yi ya ce ahankali kuma cikin rauni" bakiyimin laifin komai ba Fattomah Abbanki yana matuƙar ƙaunarki kuma yana son ki kula da rayuwarki kinji" gyaɗa masa kai kawai ta iya dan duk ta rikice ganin haka yasa ɗaya daga cikin mutanen wanda ba shine ya yi mata magana ba ya ce"inaga zamu tafi da ita sai ta zauna a gidana" da sauri ta kalleshi amma ta kasa magana dukda tanajin babu inda zata iya tafiya tabar Abbanta a wannan halin duk inda yake toh itama nan zata zauna.