← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin gumi ne yake keto masa tundaga kansa har ƙafafunsa ya gagara furta wata kalma ko guda ɗaya, Kamal ne yaja hannunsa ba tare da yace komai ba suka yi waje, office ɗinsa ya mayar dashi yana zuwa ya zaunar dashi kan kujerar dake office ɗin shuru Imad ya yi dan baida abun furtawa shi kaɗai ya dinga sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya sha dambe zagaye parlon Kamal ya hau yi kamar wani wanda ya yiwa sarki ƙarya afili ya shiga furta "inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun" kusan 5mins suna haka sannan Kamal ya dawo ya zauna yana kallon abokin nasa cikeda tausayawa ya ce"dan Allah karka saka wannan abun aranka friend wlh babu abinda yafi ƙarfin Allah in Sha Allah kanada rabon haihuwar ƴaƴa bila adadin, wannan ba wani abun bane" murmushi Imad ya yi wanda ya kasance na takaicine yana kallonsa ya ce"idan haka Allah ya tsara min babu yanda na iya da ƙaddara kuma kaima shaida ne tun inada 20yrs aka faɗi wannan maganar amma gashi har yau bata sake zani ba kuma gashi nan har yau Daddy bai sake haihuwa ba ni ɗaya da aka faɗa masa ni ne kawai ɗan da ya haifa, wlh Kamal yana ɗaya daga dalilin daya sanya mata basa gabana Saboda babu wacce zata jure zama dakai da irin wannan lalurar hatta Salma tausayi take bani tanada matuƙar ɗauke kai kuma ta nunamin ƙauna tsawon lokacin da muka ɗauka tare saboda haka kawai zan rabu da'ita taje tayi aurenta ko tanada rabon samun ɗa ita a duniya" girgiza masa kai Kamal ya yi ya ce"wannan fa wani abu ne daban dan ance daga ɗa ɗaya bazaka sake haihuwa ba saboda bakada wadataccen sperm sai kaga Allah ya yi ikonsa akanka ka haifi ƴaƴa masu tarin yawa sannan tunda har ta iya hakuri wannan lokaci zata iya zama dakai koda da ɗa ɗayan ne ai ba duka bane ba zaka haihu ba, yanzu shi Daddy daya haifi iya kai kaɗai ya kasa rayuwa?, ko akwai abinda ya rasa arayuwartasa?, Please Friend karka saka wannan aranka kaje kuma wani ciwon na daban ya sameka kayi haƙuri watarana sai labari in Sha Allah sai kaga ƴaƴanka da jikokinka" murmushi kawai Imad ya yi ya ce"toh Allah yasa thank you friend" dafa kafaɗarsa ya yi ya ce"karka damu dear".

Tana gama sanya kayanta ta zauna gefen gadon tana tunane-tunane, miƙewa tayi da sauri ta buɗe drawer, wayarta ta ɗauko ciki ta dawo ta zauna, data ta kunna tana shiga Whatsapp taga anyi mata magana da baƙuwar lamba amsa sallamar ta yi sannan ta cigaba da hira da ƙawayenta a group ɗin makaranta, murmushi ta yi bayan ganin reply ɗin da akayi dan ta ganeshi saboda pic ɗinsa ne kan dp nashi murmushi ta yi tana kallon abinda ya rubuta kamar haka

"Hyyy Fattomah ya gida ya Mommy yaushe zan zo na gaisheta?"

Dariya ta yi sannan ta mayar masa reply da imoji na mamaki, murmushi Kamal ya yi ya ce

"Please beauty wlh so nake na ganki ya za'ayi?"

Rasa abinda zata bashi amsa ta yi hakan yasa ta kashe datar tata ta kwanta tana kallon sama, sosai maganganun su Khaltum suka dinga dawowa fresh cikin kwakwalwarta tsaki ta yi ita kaɗai ta ce

"Haukama kenan"

Tana wannan tunane-tunane bacci ya yi awon gaba da'ita.

*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*

*Like nd share*
[5/13, 9:35 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.

*Ameena I Ibrahim*
Nanameera

PAGE 27-28.

Kallonsa Salma ta yi ganin kamar yana cikin damuwa amma batada ikon yi masa magana dan basu saba haka dashi ba, zama Imad ya yi kan ɗaya daga cikin royal cusion ɗin dake zagaye da parlon kusan 3mins sannan ya kalleta asanyaye ya ce

"Salma!"

Juyowa ta yi dan tabbatar da ita ce wacce yake kiran amma sai taga yana kallon wani abu daban, ahankali ta ƙaraso wajen ta zauna kujerar dake facing ɗinsa ta ce"gani" numfasawa ya yi sannan ya ce"please ki dafamana abinci banason na maids ɗin nan yau" Okay Salma ta ce sannan ta miƙe dan shiga kitchen zuciyarta fal farin ciki, cikin mintuna ƙalilan tagama dafa abincin banda ƙamshi babu abinda ke tashi dan Masha Allah Salma ta iya girki babu ƙarya musamman yanzu daya kasance Imad ne yakeson ya ci abincin nata hakan yasa ta ƙara baje basirarta. Tana kammala ta jera komai kan dinning table sannan ta haye sama dan shiryawa dan ta tabbatar yau zata kwana ɗakin mijinta, da mamaki Salma ta tsaya ganinsa tsaye jikin mirror ɗin ɗakin daga gani kasan wanka ya fito dan har sannan jikinsa na ɗigar ruwa shagala Salma ta yi da kallon mijin nata dan ganinsa take kamar wani sabon halitta tabbas Imadudden asalin kyakkyawane irin first class ɗin yanada wani irin hallitar jiki wanda ba kowa Allah ke horewa irinta ba sai kaɗan daga cikin mutane kallon gashin kansa ta yi ta ganshi luf ya kwanta gadon bayansa kamar na mace itama mai gashi sosai a Hausawa sai sheƙi kan nasa yake dukda ruwan dake jikinsa, kallon suffar jikinsa tayi wacce saida ta tsorata dan bata taɓa lura haka yake ba dukda wasu lokutan tana ganinsa babu kaya amma ba kamar yanzu ba da ya kasance bathrobe ce kawai jikinsa duk ƙirjinsa a buɗe yake wanda ya sha tatu wanda aka rubuta Imadudden amma sai ka ƙura idanu sosai sannan zaka gane sunan mutum aka rubuta tabbas da ace Imad ɗan dambene to fa babu wanda ya'isa ya kada shi dan kana ganinsa kaga asalin namiji mai ji da mazantaka

"Salmehhhhhhh"

Da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta saboda kunya dan har ga Allah batasan sanda ya zo gabanta ba, ganin taƙi ɗagowa yasa shi ya tallafi fuskarta da hannayensa masu matuƙar laushi cikin yanayi na gajiya ya ce"mene?" a hankali ta girgiza masa kai ta ce"babu komai kayi haƙuri" harararta ya yi ya ce"da aka yi me?" murmushi ta sakar masa shima ya tsinci kansa da mayar mata da murmushi ya ce"je kiyi wankan sallah I'm coming" toh ta ce masa sannan ta shige toilet ɗin tana sake waiwayonsa. Kai tsaye master bedroom ɗinsa ya nufa yana zuwa ya buɗe wata drawer bayan ya saka pin wani ɗan sachet na magani ne ya fito dashi, zama ya yi gefen gadon shi kaɗai ya dinga juya maganin kusan 3mins kafin ya mike ya isa wajen da freezer ɗin ɗakin take buɗewa ya yi ya ɗauko ruwa ya ɓalli maganin guda ɗaya ya saka abaki sannan ya kora da ruwan.

Da sauri ta farka tana kallon agogon wayarta mamaki tayi ganin yanda tayi bacci har haka batareda ta sani ba, tsaki ta yi sannan ta miƙe tana murza idanunta ta shige toilet ɗin, tana idar da sallah ta fito dan yunwa take ji kitchen ɗinta ta shiga ta duba store ɗin ciki tsaki ta yi ganin babu komai ciki sai indomie da kwai wato kallon Baby ma suke mata??, turo bakinta ta yi sannan ta kunna gas ɗin ta ɗora ruwan dafa indomie ɗin.

Tsaye ya tarar da'ita tana shafa mai ajikinta ba tare da tasan ya shigo ba ya ƙarasa gabanta yana kallonta from head to toe, juyowa ta yi da niyyar ɗaukan rigarta idanunta ya sauka cikin nasa da sauri ta juya masa baya tana murmushi dariya shima ya yi sannan ya dafa kafaɗarta ya juyo da'ita gabansa, ahankali kamar wanda ake forcing nasa haka ya dinga shafa jikinta kamar kwai ya fashe masa ajiki, ji tayi wani abu na tsirga mata tundaga kanta har ƙafarta da sauri ta riƙe hannayensa bakinta sai rawa yake amma ta gagara furta wani abu dan daman Indai Imad ne tofah ba daga nan ba yasan takan biyar da mace yanda ya kamata ganin tana ƙoƙarin kaiwa ƙasa yasa ya jata ahankali suka kwanta kan gadon yana cigaba da abinda yake, ahankali cikin salo ya fara zare towel ɗin jikinta ta lumshe idanunta dan ko kaɗan batayi ƙoƙarin hanasa ba dan itama a matuƙar buƙace take.

Sai kusan 12pm sannan suka dawo hayyacinsu musamman Salma wacce takejin so da ƙaunar mijin nata na nunkuwa cikin zuciyarta Imad ya iya soyayya kawai baya nunawa ne ko kuma akwai abinda yake nufi, saida sukayi wanka sannan ta kalleshi murya can ƙasa ta ce" abincin fa?" kallonta ya yi da idanunsa wanda har sannan basu gama dawowa daidai ba ya ce" I'm full" shuru Salma ta yi dan bazata iya musu dashi ba ta koma ta kwanta, addu'a ya yi mata sannan shima ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesu.

Kusan 2weeks kenan da dawowar Fattomah gidan Imad wanda ko kaɗan batajin dadin zaman gidan muradin zuciyarta shine lokacin makaranta ya yi ta tafi dan anan ne kawai take samun hutu amma da zarar lokacin tashi ya yi tofah idan hankalin Fattomah ya yi dubu toya tashi tana samun sauƙine idan ya kasance Jawaad ya zo gidan sau tari tana yin kuka akan zata bisa amma koda wasa Imad bai basu wannan damar ba baya taɓa barinta ko gidan taje dan kwata-kwata ma idan ba school bata fita ko'ina kullum tana zaune cikin gidan, yau ya kasance Friday yasa suna tsaye da Aysha bayan an tashi daga makaranta, har ya yi gaba sai kuma yaga kamar Fattomah hakan yasa ya dawo baya dan tabbatar da ita ɗin ya gani. Fitowa ya yi daga motar tasa yana sanye cikin ƙananun kaya wanda suka amshi jikinsa ba karya ya yi kyau fuskarsa asake kamar koda yaushe ya ce"Fattomah!" kallonsa ta yi da mamaki sai kuma ta ce"kai ne??" gyaɗa mata kai ya yi ta ce"me kake yi anan kuma?"murmushi ya yi ya ce"zan wuce sai naga wata kamar ke shine na dawo ashe kuwa kece" dariya ta yi ta ce"naji toh shige ka tafi" yanda ta yi maganar serious yasa ya tuntsire da dariya saida ya yi mai isarsa sannan ya ce"toh Hajiya Fattomah" kwaɓe fuskarta ta yi ya ce"shikenan zamuyi magana a waya ko?" gyaɗa masa kai ta yi ya ɗaga mata hannu itama ta mayar masa sannan ya shige motarsa yabar wajen, da kallo tabi bayan motar. Aysha ce ta taɓota ahankali ta ce
Chapter 15 · 0% Book details