← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 25

Sashe 16

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kee Fateemah ga Uncle dinkin can fa tunɗazu ya zo yana kallonmu" da sauri Fattomah ta juyo tana kallon inda take nuna matan, wani irin faɗuwa gabanta ya yi dan duk a zatonta yaya Jawaad ne ya zo ɗaukan nata, da sauri ta riƙe hannun Aysha ta ce"yaushe yazo?" ta ce"sanda kuke magana da wannan mutumin" shuru Fattomah ta yi na wasu sakwanni sannan ta ce"shikenan bye sai Monday" ok Aysha ta ce sannan tabar wajen. Kamar wacce akayi forcing nata haka Fattomah ke tafiya tana haɗa hanya har ta ƙaraso inda ya yi parking ɗin, buɗe motar ta yi ta shiga batace komai ba drivern yaja suka bar wajen, tunda taga irin kallon da ya yi mata ta sunkuyar da kanta har suka je gida bata ɗago ba.

Drivern na gama parking ya sakko daga motar without looking at her ya kama hannunta ya jata har cikin gidan yana zuwa parlon ya watsar da'ita yana mata wani mugun kallo ya ce cikin ɗaga murya

"Da ubanwa kike tsaye?"

Girgiza masa kai Fattum ta yi dan batasan amsar da zata bashi ba, wata uwar tsawa ya daka mata wacce tunda uwarta ta haifeta ba'a taba yi mata irin ta ba, jikinta ne ya fara rawa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, kallon rainin hankali Imad ya yi mata sannan ya fincikota ta miƙe tsaya haɗe hannayenta biyu ya yi a hannunsa ya wanketa da wasu maruwa ji kake

"Tassssssssss"

Tsabar yanda ta ji marin kusan shiɗewa tayi lokaci ɗaya gefen bakin ya fara fitarda jini, yana mata wani shegen kallo ya ce"zaki faɗa mini ko kuma sai na kakkaryaki anan wajen?" ƙoƙarin magana take amma ta gagara yi sai ajiyar zuciya da take saukewa dan ko kukanma batada zarafin yinsa. Ganin batada niyyar magana yasa ya ɗorata kafaɗarsa ya haye sama da'ita, cikin bedroom ɗinta ya direta yana mata wani kallo ya ce"yau zaki gane bakida wayo wallahi sai nayi maganinki nan gaba koda sunana kika ji an ambata zaki shiga taitayinki" yana gama faɗin hakan ya juya ya fita ta kwanta nan wajen tana wani irin kuka mai ban tausayi kusan 2mins sai gashi ya dawo hannunsa riƙeda wata irin bulala irinta dukan dokin nan, bai tsaya sake faɗar wata magana ba ya Fara sauke mata ita a gadon bayanta, tun tana ƙoƙarin karewa har saida ta gagara yin hakan saida dan kansa ya gaji sannan ya rabu da'ita ya ajiye bulalar yana kallonta cikin ɗaga murya ya ce"daga yau na sake ganin kin fita daga cikin gidan nan bare har kiji zaki iya tsayawa da wani" wayarta ya ɗauke kan drawer ya ce

"Wallahi daga nan har sanda zaki bar gidan nan babu ke babu ita ni bazaki raina min hankali na gyaleki ba shashasha kawai" yana gama faɗin hakan ya juya ya yi fitar yana huci kamar wani zaki.

Allah Sarki Fattum kasa koda motsi tayi daga inda take tunda tazo duniya babu wanda ya taɓa yi masa koda kasan abinda Imad ya yi mata ayau ba duk ya fasa mata jiki da duka ko'ina ta shafa jikinta sai taga jini na biyo wajen tasan ko kaɗan baya ƙaunarta amma bata taɓa tunanin har dukanta zai iya ba gashi ya kwace mata waya, wannan takaicin ya sanya ta sake fashewa da kuka tana kwanciya kan carpet ɗin dake wajen.

Murmushi Ameesha ta yi tana kallon Salma ta ce"Allah ya yi zamu haɗu yasa ban tafi ba yanzu nake shirin tafiya" Salma ta ce"dan Allah fa?, toh ya kike kwana ɗagawa kin ɓuya" dariya Ameesha ta yi ta ce"wallahi lafiya lao kema ai kin ɓuya ni kinga ina yawan zuna gidan nan" Salma ta ce"ina Ayrah?" "Ta shiga kitchen yanzu zaki ganta"okay Salma ta ce sannan suka ci-gaba da hirarsu.

Ganin har sannan ransa a ɓace yasa Jawaad ya ce"dan Allah kayi haƙuri Imad kasan yarinya ce ƙarama komai ma zata iya aikatawa amma bai dace ace kana fushi da'ita irin haka ba dan Allah ka dinga sassauta zuciyarka kaji" tsaki ya yi ya ce"saboda ba kaine wanda kake zaune da'ita ba shiyasa kake faɗin haka akanme Daddy zai haɗani da wannan kucakar yarinya wacce batasan kanta ba wlh ji nake inama na fita da'ita can daji na yarda ita ko nma samu na huta duk tabi ta isheni" dafa shi Kamal ya yi ya ce"calm down please komai zai shige abinda ba zama ne na har ƙarshen rayuwa ba, kayi haƙuri da wautarta please" shiru Imad ya yi bai ce masu komai ba amma shi kaɗai yasan abinda yake ji cikin zuciyarsa gamewa wannan yarinyar.

Ayrah ta ce"wallahi fa ni shiyasa nafison na dafa abinci da kaina bana wani tolerating ƴan aiki" murmushi Salma ta yi ta ce"nima abun yana burgeni amma kullum maids sune ke yi maka aiki cikin gida ai babu daɗi, ni Kinsan mene ne yake damuna?" girgiza mata kai Ayrah ta yi ta ce"sai kin faɗa" numfasawa Salma ta yi ta ce

"Wallahi abinda Imad yake yiwa Fattum baya dacewa kwata-kwata bana jindaɗi bakiga yau irin dukan da yayi mata ba wlh gwara ya mayar da'ita wajensu Daddy da wannan zaman doya da manja kwata-kwata baya sonta ya tsaneta bakiga yanda ta dawo ba sai ta baki tausayi wlh ina matuƙar tausayinta"

Tunda ta fara maganar suke kallonta baki buɗe har ta yi shiru sannan Ayrah ta ce"Allah ya kara daidai kenan maganin mai son auran mazajen wasu" da rashin fahimta Salma ta ce"mazajen wasu kuma?" Ameesha ta ce"kin bani haushi wallahi ke saboda mijinki na faɗa da kishiyarki shine Abinda zai dameki har ki dinga jin haushinsa tab" da mamaki Salma ta ce"bangane kishiya ba wace kishiyar?, Fattomah fa nace muku" dariya Ayrah ta yi ta ce"ashe baki nan baki san Abinda ya faru ba bakisan da kishiyarki kike zaune ba" labari Ayrah ta bata na abinda ya faru gidan Daddy tundaga farko har ƙarshe, miƙewa Salma ta yi tana huci ta ce"wai kina nufin Fattomah matar Imad ce yanzu?" miƙewa itama ta yi ta ce"Eh wlh matarsa ce ta sunna ma kuma" cize laɓɓe tayi ta ce"aikuwa saina nuna mata kuskurenta na bari ta auri mijina domin har abada Imam na wane ni kaɗai wlh, i must teach her a lesson" tana gama faɗin haka ta juya ta fita ko gyale bata samu zarafin yafawa ba.

*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*

*Like nd share*
[5/16, 9:55 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*

*Ameenatou I Ibrahim*
Nanameera

PAGE 29-30.

*I dedicated this page to yhu mabiyan FATTOMAH, Imad yana kallonku kuma duk yaji abinda kuka tattauna tawagar Nanameera's Library 😂ya ce a sanar daku yana nan babu gudu babu ja da baya he most teach her a lesson kuma babu yanda kuka iya 💪idan kunji haushi to kuce Daddy ya ɗauki abarsa mudai muna bayan Imadudden 🌝aikin hajjin bana damu team IMADUDDEN 😂😂much luv FATTOMAH na godiya wasu tashi sallar dare tana godiya da abin arziƙi 🙏*

Dakyar take tafiyar saboda wani irin ciwo da jikinta yake mata tunda take babu wanda ya taɓa yi mata irin wannan dukan da Imad ya yi mata jikinta duk ciwo yake, ahankali ta zauna gefen gadon nata tana duƙunƙune jikinta saboda wani irin sanyi da yake ratsata kamar mai jin zazzaɓi cikin mintuna kaɗan jikinta ya ɗauki wani zafi sai shivering take sosai zata baka tausayi saboda yanda ta koma gashi babu magani kusa kuma batasan wanda zata sanarwa ba babu waya a hannunta bare ta kira yaya Jawaad inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wannan wace irin rayuwace ta tsinci kanta wasu zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sauka kan kuncinta. Jiki asanyaye ta miƙe kamar zata haɗi ta fara tafiya azaba sosai take ji da tafiyar amma batada wani zaɓi wanda ya shige ta nemi magani domin batajin zata iya kaiwa gobe idan har tana cikin wannan yanayin, Kalle-Kalle ta shiga yi aparlon ganin kamar babu kowa ƙofar bedroom ɗin ta kalla taji sanyi aranta, without knocking ta shiga ɗakin tana rarraba idanu Salma ce zaune gefen gadon ta zuba wani uban tagumi kana ganinta kasan tabbas wani abun yana damunta ahankali Fattomah ta ƙarasa gabanta dan Salma batasan ta shigo ba tana can tunani

"Aunty Salma!"

Sai a sannan ta ɗago tana yi mata wani irin kallo cikeda tsana ta ce"lafiya?" tuni ruwa ya kawo idanun Fattomah ta ce"wallahi Aunty kullum jikina ciwo yake bana iya bacci dan Allah ki bani magani ko ki kaini asibiti kinji" afusace Salma ta miƙe tana riƙe da ƙugunta cikin wani irin ɓacin rai ta ce"uban asibiti zan kai ki ba asibiti ba keeee harni zaki rainawa hankali?, wallahi duk ranar dana sake ganin ƙafafuwanki cikin apartment ɗina wlh sai kin gwammace baki zo duniyar ba sannan ni ba abokiyar wasanki bace ke ko fuskarki banason na sake gani acikin gidan nan duk sanda muka haɗu to wlh sai ranki ya yi mugun ɓaci shashasha ƴar matsiyata kawai"

Tsabar shock Fattomah kasa magana tayi zazzaɓin jikinta na dawowa sabo kuma mai zafi fiye da na da, bakinta na rawa amma ta kasa furta koda kalma ɗaya infact ma batasan abinda zata ce ba

"Dallacan fita awajen nan!!"

Agigice Fattomah tayi waje har tana neman haɗuwa, tsaki Salma ta yi ta ce"gayyar tsiya wlh sai zaman gidan nan ya gagareki zaki san kin haɗa hanya dani"
Chapter 16 · 0% Book details