← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Fattum ta gaji da tafiyar ganin kamar ma ba tafiyar suke ba, saida suka je daga bayan gidan inda babu haske sosai ya ce"yawwa zauna anan bari na ɗauko miki acan"toh kawai ta ce sannan ya juya ya bar wajen gajiya tayi da tsaiwar ganin kusan 5mins bai dawo ba, zama tayi awajen saboda ba zata iya cigaba da kasancewa a tsaye ba

"Keeeee!!"

Aɗan firgice Fattomah ta ɗago kanta tana kallonsa ya ƙaraso yace"me kike yi anan?" ta ce"dama..daman wannan ne ya ce zai ɗauko mini magani anan na jira shi shine na zauna cikina yana min ciwo" tsaki ya yi ya ce"ke wace irin shashasha ce?, bakida hankali ko ko ya ya?, mene ne ma abinda kika fito yi a wannan daren?" hawayene ya kawo idanunta ta ce"cikina ne yake ciwo kuma na kasa Bacci shine nake neman magani" girgiza kai ya yi aransa yana cin babu daɗi tabbas abinda Imad ya aikata ba daidai bane bai dace barin yarinya budurwa cikin gida ita kaɗai ba tareda wani wanda zai kula da'ita ba, ganin tana neman faɗuwa yasa ya ce"shige ki koma gida da safe sai kije asibiti a dubaki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya ce"yi gaba" gaba tayi yana binta abaya daga yanda take tafiyar zaka gane tana matuƙar jin jiki dan dakyar take ɗaga ƙafarta a haka har suka fito compound na gidan, saida yaga ta shiga ciki sannan ya girgiza kansa ya koma wajen gate ɗin aransa yana tausayawa rayuwarta.Fattomah kuwa na shiga ta zauna a parlon nan tana kuka saboda wani irin zafi da cikinta ke mata ita kaɗai tasan masifar da take ji da wannan ciwon ciki, haka ta ƙarasa wannan daren ba tareda tayi bacci ba sai wajejen asuba sannan ta samu ya ɗauketa

ABUJA

Rai ɓace Daddy ya ce"when zaka dawo malam?" ya ce"in sha Allah ranar Thursday Daddy zanfara biyowa nan maybe" Daddy ya ce"Imad karka ce zaka rainami hankali"murmushi ya yi ya ce"Daddyyyy calm down wlh zan zo ko ban biyo ba ina komawa gida zan tawo" yace"nadai faɗa maka" kashe wayarsa ya yi yana kallon Mommy ya ce"ya kusa dawowa ai" Mommy ta ce"toh Allah ya dawo dashi lafiya amma dan Allah idan zai tawo ya tawo mini da Fattomah naganta" Daddy ya ce"why?, bai fi ba sauran 5weeks ta dawo nan duka ba please ki bar wannan maganar kawai"murmushi kawai tayi dan tasan saboda ransa aɓace yake ne ta ce"toh na bari yallaɓai" tashi ya yi bai sake cewa komai ba ya shige bedroom.

KANO

Tashi tayi wajen karfe 10am kalle-kallen inda ta kwanta ta shiga yi dafa cikinta tayi wanda har sannan yana mata ciwon amma ba kamar ɗazu ba, freezer ta buɗe da ɗauki ruwa ta sha sannan ta haye sama dan kintsawa. Kallonta gateman ɗin ya yi ya ce"yanzu ke dawa zaki je asibitin?" ta ce"nida ƴar uwarmu ka kaini gidanta please" girgiza kansa ya yi ya ce"bari akira yallaɓai dan ya ce kar a kuskura a barki ki fita wani waje idan ba makaranta ba" turo baki Fattum tayi bata ce komai ba ya ce"bari naje wajen oga" tafiya ya yi ta bisa da kallo. Saida taga ya shige sannan ta yi sauri ta kalli ƙofar, ahankali kamar wata mara gaskiya haka ta buɗe gate ɗin ta fice da gudu.

Cikin wayar Imad ya ce"A'a kar wanda ya barta ta fita indai ba school ba kuma koda school ne idan an kaita kar a tawo abarta tare da'ita zaku dawo" toh kawai sukace sannan ya katse wayar, da mamaki gateman ɗin yake kallon wajen da yabar Fattomah tsaye dan yanzu bai ganta wajen ba, sosai ya duba bai ganta ba kuma babu alamun ta koma cikin gidan buɗe ƙofar ya yi yay waje ya fara tafiya cikin unguwar kwata-kwata babu mutane a titin kowane gida kuma arufe yake wani ƙofar gida ya gani da gateman zaune kan kujera da sauri ya ƙarasa bayan sun gaisa ya ce"dan Allah kaga wata yarinya ta shige tanan?" gateman ɗin ya ce"ai kuwa wata ta sanya abaya blue ko?" da sauri ya ce"Eh ita ce" ya ce"wallahi naganta ɗazu ta shige tana tafiya da sauri kamar tayi gudu ma, amma lafiya" cikin tashin hankali ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun meyasa yarinyar nan zatayi haka?' magana gateman ɗin yake masa amma ko juyowa bai yiba shi kaɗai yasan tashin hankalin da zasu fuskanta wajen Imad idan har ya dawo ya tarar bata nan fatan shi ɗaya Allah ya bata ikon dawowa da wuri duk inda taje,koda ya shiga gidan babu wanda ya sanarwa cewa bata nan ya koma ya yi zamansa dukda zuciyarsa fal take da tunani kala-kala.

Da gudu Khaltum ta zo ta rugumeta tana sake kallonta cikeda murna ta ce"Fattomah ke ce dagaske?" murmushi ta yi ta ce"to dafa?" dariya suka yi tare ta ce"ina Adda?" "yanzu ta fita taje wajen biki yanzu zasu dawo" okay ta ce Sannan ta zauna kan katifar

"Washhhh wlh nagaji sosai"

Kallonta Khaltum ta yi ta ce"wai daga ina kike?" "daga gida mana, ina yaya Aslam?" ta ce"wallahi ya tafi Katsina mukaje gidan da kika koma muka tarar arufe shine ma ya tafi" miƙewa daga kwanciyar da tayi ta ce"dan Allah fa meyasa baku bugamin waya ba nag ...." shiru ta yi tunawa da tayi babu waya a hannunta Khaltum ta ce"wallahi mun kira ki amma wayar akashe shiyasa kawai muka haƙura muka dawo gida, kina waya da Ammi?" hawayene ya kawo idanunta amma ta ɓoye ta ce"rannan na kirata please kina credit wayarki kimin kiranta?" okay ta ce sannan ta ɗauko wayarta, ringing ɗaya Ammi ta ɗaga wayar tana yin sallama Fattomah ta ce

"Ammina!!Ammina!!Amminaaa".

Kukane yaci ƙarfinta tama kasa magana ita kanta Ammi kuka take domin tana matukar kewar ɗiyarta saida ta daidaita muryarta sannan ta ce"mene ne haka Faɗeematoh?" sake rushewa tayi da wani kukan saboda tunawa da tayi da Abbanta da yake yawan ce mata Faɗeematoh, cikin sheshsheƙar kuka ta ce"Amma.Amm...Ammina dan Allah ki dawo Kano kinji banason zama gidan uncle ki dawo mu zauna agidanmu kinji yafi daɗi Ammi" cikin raunin zuciya Ammi ta ce"kiyi haƙuri Fattum ina nan zan zo wajen ki in sha Allah karki damu ki daina kuka kinji ki daina rigima" Fattomah ta ce"Ammina inason naganki dan Allah" murmushi tayi wanda yake zuba da hawaye ta ce"Nima haka Fattum inason naganki amma in sha Allah zan zo nan kusa" "Ammi amma bazaki koma ba?" ta ce"ai nadawo gida Fattum nida rayuwa cikin Kano saidai hukuncin Ubangiji" sake fashewa ta yi da kuka Ammi ta ce"ya isa kiyi shiru banason kukan zan zo shikenan?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"to sai kin zo Ammi kuma so nake ki dafamin dambun shinkafa da zogale da gyaɗa Ammina" dariyar da bata shirya ba ta yi tanajin zallar rigimar ɗiyar tata ta ce"in sha Allah randa nazo Kano duk zan dafa miki wannan abubuwan Fattum" murmushi ta yi ta ce"toh Ammina sai kin zo" ta ce"toh Faɗeema" murmushi ta sake yi ta ce"ina sonki Ammina" dariya ta yi ta ce"nima inasonki Fatyy na", sallama sukayi sannan ta miƙawa Khaltum wayarta.

Dariya ta yi ta ce"naga randa zaki daina shagwaɓa arayuwarki" harararta ta yi ta ce"babu rana kuwa wollah" dariya Khaltum ta yi ta ce"ai shikenan" kwanciya Fattomah tayi gefen katifar nan da nan bacci wanda baya mata wahala ya sake ɗauketa. Murmushi Adda ta yi ta ce"aikuwa kin kyauta Faɗeematoh amma dai kwana zaki yi?" gyaɗa mata kai Fattum tayi tana murmushi dan daman haka ta shirya, Abla ta ce"kinyi kyau abunki amma duk kin rame Fattu"harararta Adda ta yi ta ce"ke kam da gulma Allah ya shirya" dariya suka yi duka sannan suka cigaba hira gwanin ban sha'awa, tun bayan rasuwar Abba sai yau ta sake samun farin ciki irin wanda ake kira farin ciki domin ji take kamar zata koma gidansu ta tarar da Abbanta da Amminta zaune suna jiranta

"Fattomah kuka?"

Da sauri ta taɓa fuskarta taji hawayene yake zuba, Adda ta ce"faɗa min lafiya kuwa?" murmushi ta yi ta ce"lafiya klao Adda kawai Abbana na tuna shiyasa" cikeda tausayawa Adda ta ce"ayyah Allah ubangiji ya jiƙan Ahmad" cikin asanyaye ta ce"Ameen ya Allah".

Har wajen ƙarfe 12am ba suyi bacci ba suna hira idan wannan ta faɗa sai wannan ta ɗauke a haka har baccin ya ɗaukesu banda Fattum wacce take jinta cikin wata duniya tabbas rashin iyaye babu daɗi duk irin abinda zaka samu idan har babu iyayenka tofah bashida amfani haka ba kowane zai ƙaunaceka saboda Allah ba dukda ƙanƙantar shekarunta amma ta naɗe wannan cikin kwakwalwarta, ba ita tayi bacci ba sai wajen 2am a haka ma ɓarawone ya saceta. Da safe bayan sun idar da sallar asuba suka fito tsakar gida Abla ce ta shimfiɗa musu tabarma suka zauna suna cigaba daga inda suka tsaya jiya, Adda ce ta fito jin hayaniyarsu ta ce"tunda kun tashi sai ku nemi abun dafawa, Faɗeema me kike so?" sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ta ce"Adda kunu nakeso da ƙosai please" murmushi irinna manya Adda ta yi ta ce"tom shikenan Khaltum ki tashi ki kunna wuta bari nima na fito"toh ta ce mata sannan ta koma ɗakin. Suna gama karyawa suka haɗa kwanukan wanke-wanke suka fara yanda suke yi da nishaɗi yasa basu wani ji wahalar aikin ba har suka gama gyara gidan wajejen 10am sannan suka koma bacci, da rana Adda ta dafa musu dambun shinkafa wanda yaji zogale Masha Allah Khaltum ce ta daka musu yaji mai daɗi suka zauna yanda suke cin dambun shinkafar ni kaina saida yawuna ya tsinke musamman Fattomah dan ba ƙaramin ci tayi masa ba dan saida ya fice kanta tsabar irin cin da tayi masa ni kuwa na ce ko dan saboda harta sammin ne☹️babu komai Imad namu zai bani nasan 😂.
Chapter 21 · 0% Book details