← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Imad ya yi ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita duk tabi ta dagula masa lissafi ranshi a ɓace ya ce"wai ba zaki yiwa mutane shuru ba?" ko kallonsa Fattomah batayi ba bare ya yi tunanin amsa ta ci-gaba da kukanta tana yarfe hannu, sai kusan ƙarfe 7am sannan ta samu ta yi bacci shi kuma ya fito dan komawa gida dan sai a asibitin ya yi sallah asuba. Tunda ya shiga parlon take kallonsa amma ta kasa yi masa magana har ya shige rai ɓace Salma ta miƙe daga kan kujerar wato saboda rainin hankali har wani fita suke abarta cikin gidan saboda batada amfani, goge hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tayi sannan ta shige bedroom ɗinta tayi kwanciyarta zuciya babu daɗi. Ƙarfe 12pm ya shiga asibitin yana sanye cikin wani yadi black colour ɗinkin babbar riga da jamfa sosai ya yi kyau abinsa ya sanya face mask a fuskarsa gudun kada attention ɗin mutane ya zo kansa yana shiga ɗakin ya tarar tana zaune sai wata nurse dake ƙoƙarin cire mata drip ahankali ya yi sallama wacce idan ba kasa kunne ka yiba bazaka ji abinda ya ce ba, tsayawa ya yi yana kallonta har ta ƙarasa cire mata sannan ta juya ta fita, sunkuyar da kai Fattum ta yi ya zauna kan kujerar dake gefen gadon ya ce"ya jikin naki?" ahankali ta ce"da sauƙi"miƙewa ya yi ya fita ta bisa da kallo. Murmushi Doctor ya yi ya ce"sir hakan dana faɗa shine solution kuma kai ma kasan haka tunda kasan field ɗin" ajiyar zuciya Imad ya sauke yana jin abun kamar ba mai yiwuwa ba lura da hakan yasa doctorn ya ce"sir kadai duba maganar coz haka ne kawai mafita wallahi komai na iya ka sancewa da rayuwarta kuma kullum ahaka zata kasance cikin ciwo tunda dai akwai halin taimakawa please ka taimaki rayuwarta kayi trying ko sau ɗaya ne" miƙewa Imad ya yi ya ce"zanyi tunani akai" okay Doctorn ya ce sannan ya juya ya fita.

Yanda ya barta haka ya tarar da'ita har sannan bata kwanta ba amma wannan karan ta haɗa uban gumi jikinta sai rawa yake ƙara sawa gabanta ya yi ya kama hannunta ya ce"keeee" kasa kallonsa ta yi tana kuka ahankali sosai yaji jikinta da zafi ta ɗora kanta kan cinyarsa koda wasa bai yi yunƙurin hanata ba yana jin yanda take fitarda zazzafan numfashi kan cinyarsa, kusan 5mins sannan ta fara sauke numfashi ahankali ya shafa kanta tana sauke ajiyar zuciya sallama Jawaad ya yi ya shigo aɗan rikice ya ce"ya jikin nata?" Imad ya ce" da sauƙi Alhamdulillah" kallonta Jawaad ya yi ya ce"sannu dear" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"yaushe za'a yi discharging naku?" Imad ya ce"har anyi gida zamu tafi yanzu"okay Jawaad ya ce sannan ya kalli Fattum wacce duk ta fice hayyacinta ya ce"tashi mu tafi gida" miƙewa Imad ya yi ya kama hannunta ta miƙe jikinta na rawa ta ce asanyaye"bazan iya tafiya ba ni"kallonta Imad ya yi kamar ya ce wani abu sai kuma ya yi shiru ya ɗauke ta kamar Baby suka fita daga ward ɗin.

Waro ido Salma ta yi hankali atashe ta ce"kamarya Ameesha?" murmushi Ameesha ta yi ta ce"naga kin wani firgita ko daman baki shirya ba?" girgiza kai Salma ta yi ta ce"bawai haka bane Ameesha kawai banason zuwa wajen wani malami ne shiyasa kawai gwara Imad ya sakeni na kama gabana ni bazan iya kunsar baƙin ciki ba wlh" tsaki Ameesha ta yi ta ce"aikin banza ashema ke ƙaramar ƴar iska ce kenan kin haƙura da duk tarin dukiyarsa wacce zaki mallaka idan yana ƙarƙashin ikon ki har kike tunanin fita daga cikin gidansa" Salma ta ce cikeda damuwa"wai to Ameesha mene ne abinda zan yi kusan 5yrs muke tare dashi kuma Alhamdulillah na samu abinda na samu wajensa dan Imad bashida rowa ko kaɗan ni gaskiya bazan taɓa iya cutarda shiba lemme tell you" dariya Ameesha ta yi ta ce"da ni nace miki ki cutar dashi ne?, ko kuwa kina ganin zaki iya cutar dashi ɗin ne?, ai daman ba shine target ɗinmu ba ya kamata ace kina saurin fahimta Salma" da mamaki Salma ta ce"bangane abinda kike nufi ba, waye target ɗin toh?" murmushi kawai ta yi sannan ta ce"yarinyar dake gidan nan Fattomah da'ita zamu yi amfani wajen aiwatar da abinda muka yi niyya batareda kowa ya zarge muba idan har zaki iya yin abu yanda na tsara wlh zamu samu nasara kawai ki cire tsoro malama" numfasawa Salma ta yi ta ce"zanyi tunani akai Ameesha dan bazanyi abinda zai dawo kai na ba wlh nasan halin Imadudden bashida mutunci idan yaso kome zai iya aikatawa saboda haka bazanyi Abinda zan jawo a ɗaureni ba gwara na rabu dashi cikin mutuntawa" miƙewa ta yi daidai lokacin suka shigo cikin parlon bakinsu ɗauke da sallama, da kallo suka bisu har suka zauna sannan suka gaisa Jawaad ya ce"Ameesha ke ce anan?" murmushi ta yi ta ce"wallahi fa Doctor na ɗan shigo sada zumunci ne ya Ayrah?" "tana nan klao Alhamdulillah" "Masha Allah". Satar kallon Imad ta yi taga ko inuwarta bai kalla ba hakan yasa ta ce"yallaɓai ina yini"

"Lafiya"

Abinda kawai Imad ya ce kenan ya ɗauke kansa yana cigaba da danna wayarsa, shuru Ameesha ta yi dan daman tasan haka zata iya faruwa dan tun ba yau ba Imadudden baya wani ƙaunarta dan murmushin yaƙe ta yi ta ce"toh Salma sai anjima" miƙewa ta yi ta ce"muje na raka ki" okay ta ce sannan sukai waje. Kallon Fattomah ya yi wacce take kwance kan kujera 3seater ya ce"tashi ki tafi " ahankali ta miƙe daga kwancen ta fara hawa stairs ɗin kamar ta waɗo har Allah ya taimaka takai ɗakin nata, saida ta shige sannan Jawaad ya ce"wai what wrong with her?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wai menstrual pain ke damunta shine fa harda kwanciyar asibiti" Jawaad ya ce"ayyah to Allah ya ƙara sauƙi ya rabata dashi kuma" Ameen Imad ya ce sannan ya cigaba da abinda yake.

"Kin gani ko Ameesha ke daga ganin irin kallon da Imad ke miki kinsan akwai wani abun a ƙasa nidai ki rufamin asiri ki rufawa iyayena idan zamuyi magana dake mu haɗu gidan Ayrah ko muyi chat idan ya zama worth akwai buƙatar na ganki ko park ne sai muje please" taɓe baki Ameesha ta yi ta ce"ke kam Allah ya yaye miki ai shikenan mayi wayar" okay ta ce sannan ta shiga mota ta fita ita kuma ta koma ciki, zaunar ta tarar dasu da alama wani abun suke tattaunawa hakan yasa tana yin sallama ta tafi zata hau sama

"Salma!"

Da sauri ta juyo jin ya kira sunanta, gani tayi ba ita ce wacce ya ke kallo ba amma tabbas da'ita yake hakan yasa ta dawo wajen ta zauna kan kujera

"Gani"

Ɗago dara-daran idanuwansa ya yi ya saukesu akanta, da sauri ta yi ƙasa da nata idanun haka kawai taji gabanta na faɗuwa tabbas akwai abinda ya sanya ya yi mata wannan kiran, kusan 2mins sannan ya ce"karna sake ganin wannan yarinyar cikin gidan nan okay?" gyaɗa masa kai ta yi ta ce"in sha Allah" kallon Jawaad ya yi ya ce"as i said before" ganin sun cigaba da maganarsu yasa ta miƙe ta haye sama tana dafe ƙirji.

Cikin kwanaki uku data ɗauka tana period tayi matukar shan wahala duk ta rame kamar ba itaba dukda yanda Imad ya yi ƙoƙari wajen ganin ta samu duk wani abu da take da buƙata har ta kammala sannan ta cigaba da zuwa makaranta zuwa yanzu kuma sun kusa fara yin Neco, murmushi ta yi tana kallon Fa'eeza ta ce"ke kam ki dinga jin tsoron Allah wallahi duk irin amsar da kika kwafa" dariya Fa'eeza ta yi ta ce"wallahi ƙarya kike Banason sharri ayaushe ai wallahi sai na faɗawa Daddyna dama ya sani bai biyamin anan makarantar ba" dariya suka hau yi mata Aysha ta ce"abanza dai tunda har kin fara zanawa" Shuru Fattomah ta yi ganin motarsa tsaye bakin gate ɗinsu sai na guards ɗinsa kusan guda biyar, kallonsu Aysha ta yi ta ce"sai anjima anzo ɗaukana" bye bye suka yi mata sannan ta tafi.

Zaune ta sameshi cikin motar yana danna system da alama wani abu mai muhimmanci yake gabatar dan duk attention ɗinsa yana can, shiru Fattomah ta yi bayan ta shiga tana jin wani sanyi na ratsata ga ƙamshin turarensa wanda ya haɗe da sanyi A.C ya bata wani irin sanyi mai ban sha'awa, lumshe idanunta ta yi tanajin duk wata gajiyarta na sauka kallonta kawai Imad ya yi ganin yanda ta fara bacci jikin motar ajiye system ɗin hannunsa ya yi ya ɗauko wata leda ƙarama a hannunsa buɗewa ya yi ya ɗauki wata injection saida ya gama haɗawa sannan ya matsa kusa da'ita ahankali cikin dabara ya yi mata allurar motsawa ta yi amma Saboda yanda baccin yake kanta ya sanya ta cigaba da abinta.

Fitowa ya yi daga toilet ɗin yana tsane jikinsa, wayarsa ce ta fara ringing ya ɗauka cikeda ladabi ya ce"ina yini Daddy?" Daddy ya ce"lafiya Imad kuna lafiya?" ya ce"Alhamdulillah Daddy ina Mommy?" "Tana nan, ka bawa Fateemah zan yi magana da'ita" kallon Fattomah ya yi wacce take ta faman bacci ya ce"Daddy bacci take wallahi saidai zuwa anjima ko gobe" okay Daddy ya yi Sannan ya yi hangup na kiran. Ajiye wayar ya yi sannan ya cigaba da gyara jikinsa saida ya gama shiryawa sannan ya ɗauko wani tablet sosai ya dinga tunani kusan 5mins sai kuma ya zaro wayarsa dialing number Doctor ya yi ring biyu ya ɗauka bayan sun gaisa ya ce
Chapter 18 · 0% Book details