← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 25

Sashe 7

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da murmushi a fuskarsa yake kallonta har ya ƙaraso inda take, zama ya yi kan kujerar dake facing wanda take kai ya ce" princess naji kinyi shiru lpy?" kallonsa tayi ta ce" yaya wai sai naga kowa yanada waya a school ɗinmu amma banda ni nima ka siyamin waya yau kuma" dariya ya yi yana kallonta ganin da gaske she's vert serious ya ce" toh Fattum zan siya maki idan kika yi graduation" wani irin kallo tayi masa sai kuma ta ɗauke kai tana kallon wani wajen daban, murmushi ya yi ya girgiza kai sannan ya ɗauko wata leda wacce take bayansa yana murmushi ya ce" kalli kiga" kin kallonsa tayi tana tura baki gaba, Jawaad ya ce" idan na mayar shikenan bazan baki ba shikenan kin rasa" satar kallon hannunsa tayi taga leda amma batace ga abinda yake cikin ledar ba, gyaɗa kansa ya yi sannan ya ɗauke ledar yana shirin mayarwa da sauri ta juyo ganin kamar waya ce cikin ledar tana washe baki ta tafi wajen tana zuwa ta karɓe ledar ta buɗe sakar baki Jawaad ya yi yana kallonta, tana gama ware wayar idanunta ya sauka kan iphone 11pro wata irin ihuuu ta saka tana ƙanƙameshi tana dariya ta ce" thank you so much Yaya nagode sosai Allah Ubangiji ya bikaya da gidan aljanna I'm so happy yayana" murmushi Jawaad ya yi yana kunshe idanunsa dan daman farin cikinta shine muradinsa ya ce" Ameen princess nima nagode" ledar kawai ta ɗauka ta fita daga garden ɗin da gudu da kallo ya bita sannan ya miƙe shima yabi bayanta

"Mommy kinga Yaya Jawaad ya siyamin" waro ido Mommy ta yi ta ce" enyeeee yarinya ƴar gidan yaya Jawaad to kince kin gode?" gyaɗa mata kai tayi tana washe baki daidai nan Jawaad ya yi sallama a parlon, gaisawa sukayi da Mommy ta ce" wato na fuskanci kaine kake shagwaɓata yasa take abinda taga dama ko Jawaad" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" A'a Mommy" murmushi Mommy tayi ta ce" kai da ita ni nan babu ruwana wlh" dariya ya yi ya ce"wai ina Footballer ne kwana biyu?" tsaki Mommy tayi ta ce" nima ina na ganshi sai ɗazu naji babansa ya ce wai ya tafi Spain shine amma ko ya sanar dani" murmushi Jawaad ya yi ya ce" kinsan halinsa sai shi watarana sai naji kamar dai yanada almutsutsai akansa" tuntsirewa tayi da dariya suka juya duka suna kallonta, saida tayi mai isarta sannan ta ce" yaya Jawaad ka bani dariya wai almutsutsai" sake tuntsirewa da dariya tayi Mommy ta ce" Allah Ubangiji ya shirya mana ke Fattum" tana dariyar ta ce" Ameen Mommy".

Haka Fattomah ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikin gidan General Ibrahim Baira babu abinda ta rasa arayuwarta komai suna yi mata abu biyu ne kawai yake damunta na ɗaya rashin Abbanta wanda har sannan bai saketa ba sai kuma rashin Amminta kusada ita dan bayan arba'in ɗin Abba ta koma garinsu Katsina saidai suyi waya da'ita lokaci zuwa lokaci, banda waɗannan abubuwa batada wata damuwa rayuwarta tana tafiya yanda ya kamata hakana ɓangaren karatunta wanda yanzu taƙi kaɗan ya rage mata dan gab suke da fara jarrabar kammala karatu matakin secondary. Bangaren Jawaad ma yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata mata duk da zuwa sannan Mommy ta gama fahimtar inda ya dosa saidai babu wanda ta sanarwa hakan ta bari har sanda suma zasu gano hakan da kansu, Ayrah kuwa da batasan wainar da ake soyawa ba ta ɗauki Fattomah tamkar ƙanwarta duk abinda ta samu tofa natane itada Fattum har kwana takeyi gidansa idan Daddy ya barta. Yauma suna cikin kitchen tare inda suke dafa jallof rice sai chips da zasuyi da kuma pineapple nd coconut drink, Banda ƙamshi babu abinda yake tashi dan indai girkine tofa Ayrah number ɗaya ce tanada kwarewa ta wannan fannin ba'a taɓa kada ita a girka haka itama Fattomah wacce yanzu take koyan duk wani abu wand da bata iya shiba. Sallama suka ji a parlon hakan yasa Fattomah ta miƙe daga kan stool ɗin tana kallon Ayrah dake ƙoƙarin wanke hannunta ta ce" aunty Ayrah bari na duba" ohk ta ce sannan ta cigaba da abinda take ita kuma ta fito dan ganin waye, da gudu ta tafi ta rungumeta tana dariya ta ce".

*Nanameera ce#*[5/13, 9:27 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

PAGE 13-14.

"Aunty Salma sannu da zuwa"

Murmushi Salma ta yi tana kallonta ta ce" Fattomah ya kike?" "Ina lpy muje ki zauna" okay Salma ta ce sannan tabi bayanta suka zauna kan kujera, Salma ta ce" Ayrah bata nan ne?" Tashi Fattum ta yi ta ce" muna aiki a kitchen ne bari na sanar da'ita" okay Salma ta ce sannan Fattomah ta juya ta shige kitchen ɗin, kallonta Ayrah ta yi ta ce" wace Fattum?" "Aunty Salma ce tazo" ok Ayrah ta ce sannan ta ce" ki ƙarasa haɗa drink ɗin please karki cika sugar Kinsan yayanki baya so" murmushi ta yi ta ce"toh in Sha Allah".

Murmushi ɗauke a fuskarta suka gaisa ta ce"sannu da zuwa sai yau?" Murmushin itama ta mayar mata sannan ta ce" wallahi kinsan halin mutumin ban samu saƙafar faɗa masa ba sai yau shiyasa ma kikaga ganni yanzu da yamma ya ce anjima zai zo mu tafi" Ayrah ta ce "wallahi yaya Imad halinsa sai shi rannar fa dakyar ya tsaya ya ci abinci wai tafiya zai yi bayan ya gama saka ni aiki" dariya Salma ta yi ta ce"Allah dai ya kyauta" Ameen Ayrah ta amsa sannan ta ce" let me get you something".

Harararsa Jawaad ya yi ya ce" bangane ba?"kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wannan abinda kake shirin yi isn't proper matarka ta ɗauki yarinyar nan matsayin ƙanwarta bata nuna mata wani banbanci da ƴan uwanta shine zaka ɓata alaƙar tasu kuma sannan ma ka rasa wa zaka aura sai ƙaramar yarinya ubanme zata yi maka idan zakayi aure ka ɗauko babbar mace shine Malam ba wacce zaka zauna raino ba" tuntsirewa ya yi da dariya yana kallon ɗan uwan nasa ya ce" a naka tunanin kenan amma ni kam babu abinda zai hanani auran Fattum sai ikon Allah naji zanyi rainon nata kai bakasan sunfi daɗi ba yaran" taɓe baki Imad ya yi ya ce" bakada hankali ne shiyasa sai ka ƙara girma" wani shegen kallo Jawaad ya watsa masa ya ce" lailaima wato kaine ka girma ko Abba" haɗe rai Imad ya yi ya ce" E, kasan ai daman ni ba sa'anka bane" fitowar Fattum ya sanya sukayi shuru da maganar tana zuwa ta kalli Jawaad tana haɗe rai ta ce" yaya muje ka mayar dani gida" da mamaki ya ce" lafiya princess?" turo baki ta yi ta ce" kawai nidai ka mayar dani mana"

"Fattum!!! Fattum!!"

Ƙin juyawa tayi Ayrah tazo tana murmushi ta rungumeta ta baya ta ce" I'm so sorry dear ban ƙarawa" ƙin kallonta Fattomah tayi dan ita daman riƙo gareta, murmushi Jawaad ya yi ya ce"me kika yimata?" murmushin itama tayi ta ce" wai dear daga nace mata ta cika sugar cikin drink shine fa wai gida zata tafi" dariya ya yi ya ce" rigima dai Fattum?" zumɓura baki ta yi ta ce" ni bazan sake zuwa gidan nan ba" Jawaad ya ce" dan Allah kiyi haƙuri Fattomah Kinga yanzu dare ya fara yi ki bari gobe in Sha Allah da kai na zan mayar dake gida okay?" girgiza kanta tayi bata ce komai ba, babu yanda basu yi da'ita ba amma Fattomah taƙi haƙuta ita a lallai sai ta tafi gida. Ji tayi an fizgota ta juya kafin tayi aune har ya kaita compound ɗin gidan, cikeda ɓacin rai yake cewa

"Idan kika sake two minutes cikin gidan nan sai ranki ya ɓaci shashasha kawai"

Da sauri Jawaad ya ƙaraso wajen yana kallonsa ya ce" haba Imad mene ne haka yarinya ce fa?"

Afusace Imad ya juyo ya ɗaga masa hannu ya ce" enough!!, banason jin komai nd idan baki bar gidan nan ba I'll show you the other side of me" banda rawa babu abinda jikin Fattomah keyi Allah sarki duk tabi ta tsorata bata saba da irin wannan masifar ba domin kwata-kwata ba'a yi mata faɗa idan ka cire Ammi wanda shima a hankali take faɗa mata koda kuwa laifi tayi shiyasa duk tabi ta ɗimauce, ganin har sannan batada niyyar fita yasa yace da ƙarfi" ubanme kike jira ne?" jikinta na kyarma tayi hanyar fita daga cikin gidan veil ɗin nata ma ya waɗi saboda tashin hankali. Ganin ta kusa kai wai bakin gate yasa Jawaad ya bi bayanta ba tare da ya kalli Imad ba har zata fita dan gateman ɗin bai yi ƙoƙarin hanata ba ganin abinda ya faru, da sauri ya fice daga gidan yana bin bayanta ya ce

"Fattomah!!"

Ko juyowa bata yi ta cigaba da tafiya da sauri da sauri gudun kada ya cimma ta, kasancewar tafiyarta da tashi ba ɗaya ba yasa ya yi saurin shan gabanta yana kallon fuskarta wacce duk ta jiƙe da hawaye ya ce" Fattum!" kasa kallonsa tayi sai kawai ta rungumeshi tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ba ƙaramin tsorata tayi ba har jikinta ya fara ɗaukan zafi, tsam ya rungumeta a ƙirjinsa yana jin yanda take kuka a hankali shafa kanta kawai ya iya yi dan bashida zarafin ce mata tayi shuru tabbas akwai buƙatar tayi kukan ko ta samu sauƙi cikin ranta.
Chapter 7 · 0% Book details