← Book details Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 25

Sashe 17

Fattomah Book Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin raunataccen kuka ta fashe dashi tana sake ƙanƙame pilon dake hannunta wace irin ƙaddarace wannan ke bibiyar rayuwarta?, meyasa Abba ya mutu ya barta, meyasa Ammi ta koma garinsu without second thought na makomarta?, meyasa Daddy yabar garin nan ba tare da ita ba?, meyasa ba'a ce ta zauna gidan yaya Jawaad ba sai gidan Imad?, waɗannan sune tambayoyin wanda ta gagara samun mai amsa mata tabbas akwai ƙalubale sosai a rayuwarta kamar yanda Abbanta ya faɗa mata cikin mafarki batasan laifin da ta yiwa Salma ba amma tana jin idan babu ita bazata iya cigaba da zama cikin gidan ba domin watarana zuciyarta sai ta fashe saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali tuna irin waɗannan abubuwan yasa ta sake rushewa da kuka iya ƙarfinta amma babu wanda yake sauraronta har bacci ya saceta. Wani kallo ya yiwa Jawaad sannan ya ce"banfa gane abinda kake nufi ba" murmushi Jawaad ya yi ya ce"zama ka fahimta ne Footballer tunda kana abinda kaga dama yanzu zuwa yaushe zaka tafi??" Imad ya ce"Ehh tohhh nan da one week in sha Allah" okay Jawaad ya ce, miƙewa ya yi ya ce"ni fa zan tafi coz inada meeting around 3pm zuwa 5pm zamu fito sai mu ƙarasa maganar ko kazo gida da daddare" okay ya ce masa sannan sukayi sallama ya fita..

Tsaki Aysha ta yi ta ce"kawai muje gidanmu kiyi zamanki wallahi tunda babu kowa gidan kuma kina jin tsoro" girgiza kai Fattum ta yi ta ce"A'a Aysha idan Uncle ya tarar bana gida dukana zai yi kawai zan tafi saina zauna wajen gatekeeper har su dawo kinga daman gobe bamuda paper sai next week" haɗe rai ta yi ta ce"ke wllh kin fiye tsoro ai shikenan kuma ke ba waya ba bare muyi magana ta chat" murmushi kawai Fattomah ta yi bata ce komai ba, can kuma ta ce"ina wayarki please?" "Me zaki yi da'ita?" tsaki ta yi ta ce"please ki bani da sauri zanyi amfani da'ita ne" miƙa mata tayi ta ce"hope akwai card?" gyaɗa mata kai ta yi sannan ta ci-gaba da kallonta. Ringing biyu ta ɗaga wayar ta sanya akunnenta daga ɗaya ɓangaren akayi sallama ji tayi kamar duk wata damuwarta ta gushe hawaye na taruwa akurmin idanunta ta ce asanyaye

"Ammina!"

Wani irin yanayi ta jita ciki itama hawaye na cikowa idanunta ta ce"Fattum kina nan klao?" girgiza kanta ta yi amma ta ce"ina lafiya Ammi, kin tafi kin barni ko Ammi?" ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan ta ce"ban barki ba Fattum babu yanda zanyi ne shiyasa na barki karki damu nasan zaki zo ko kuma ni nazo inda kike Faɗemah" kuka Fattum ta saka tana jin wata sabuwar kaunar mahaifiyarta na shiga jikinta tabbas baka gane amfanin abu sai sanda ya yi nesa dakai ayau ji take inama Amminta na gefenta da bata dinga yi mata rashin jin magana ba, da ta zaunar da'ita tana yi mata hira mai daɗi har bacci ya ɗauketa. Jin tayi shuru yasa Ammi ta ce"Kina kan layi Fattomah?" gyaɗa mata kai tayi kamar tana gabanta ta ce"Eh Ammi yaushe zaki zo?" murmushi Ammi ta yi ta ce"in Sha Allah zan zo nan bada daɗewa ba, kina karatu dai?" ta ce"Eh Ammi ina yi yanzuma exams muke ta Waec mun kusa gamawa" Ammi ta ce"toh Masha Allah, Allah ya taimaka ya bada sa'a Faɗeemah ki cigaba da haƙuri" Ameen ta ce jiki asanyaye sannan sukai sallama, ajiyar wayar tayi kawai ta kifa kanta ta fashe da kuka sosai taka kewar iyayennata, dafata Aysha ta yi ta ce"kiyi haƙuri kinji Fateema dan Allah ki daina wannan kukan duk kin rame kinyi baƙi fa" dakyar Fattomah ta yi shiru sannan ta tashi tana kallon Aysha ta ce"zan tafi ni dai" "ke kaɗai zaki zauna?" gyaɗa mata kai ta yi dan bata yanayin da zata iya doguwar magana gaba tayi kaiwa Aysha ta bita da kallo cikeda tausayawa koda Fattomah bata faɗa mata halinda take ciki ba tasan tabbas akwai abinda yake damunta domin yanda duk ta fice hayyacinta cikin ƴan sattitika ƙalilan.

Da mamaki Fattomah ke kallon motar tasa dan tama gagara ƙarasawa kar taje ba ita yazo ɗauka ba, tsaki Imad ya yi ganin ta tsaya tana kallonsa fitowa ya yi daga motar yana sanye cikin wata jallabiya blue colour ya tufke gashinsa ya zubo har gadon bayansa dukda yanda ransa yake a haɗa hakan bai hana ainihin kyansa fitowa ba kana ganinsa kasan yesssss akwai kyau babu ƙarya. Da kallo ɗaliban makarantar suka bishi ganin mutum mai kamada Larabawa yana tafiya toward direction na makarantar, duk yanda zuciyarta ke lugude haka ta danne ta cigaba da kallonsa har ya ƙaraso, wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"kin bar kallona ko saina tsiyaye idon" sauke idanunta ƙasa tayi bata ce komai ba ya juya ya koma motar itama tana biye dashi.

Kwafa Salma ta yi sannan tabar wajen tana jin baƙin ciki kamar ya kasheta wato daman son yarinyar yake shine dalilin daya sanya yake raina mata hankali kuma baya bata lokacinsa ko kaɗan, suna shigowa parlon ta yi sauri ta haye sama gudun kada ya yi mata magana ko kuma ya yi mata tsawa, da kallo ya bita sannan ya taɓe baki ya zauna kan kujerar yana kallon tv inda al-jazeera ke haska labarai. Tana fitowa daga wanka ta shige kitchen ɗinta, tsaki ta saka tunawa da tayi babu komai cikin kitchen ɗin sai indomie kuma ta gaji da cinta, juyowa ta yi zata fito suka yi karo da sauri ta koma baya tana ɗan yarfe hannu haɗe rai ya yi ba tare da ya yi magana ba ya miƙa mata wayar hannunsa karɓa ta yi tana sanya kunnenta tana ɗan satar kallonsa juyawa Imad ya yi yabar ɗakin tana murmushi ta ce

"Mommy nayi missing naki sosai inason na ganku please"

Murmushin itama ta yi ta ce"Fattomah rigima ki bari da zarar kin ƙarasa exams Imad zai dawo dake shikenan mu cigaba da rayuwarmu kamar da" sosai Fattum ta ji daɗin haka ta ce"toh Mommy daman mun kusa gamawa ai"okay ta ce sannan suka ci-gaba da hirarsu cikeda so da ƙauna kai ka ɗauka da gaske ita ce wacce ta haifeta.

Wani irin sanyi taji ya daki hancinta ta lumshe idanunta dan daman tana matuƙar ƙaunar yanayi irin wannan shiru parlon yake babu alamar mutum ciki hakan yasa kai tsaye ta shige bedroom ɗin mamaki ta yi ganin yanda ɗakin yake da wani irin kyau kaf ɗakunan gidan ba taga wanda ya kai shi kyau da kuma tsaruwa ba, tsayawa ta yi tana kallonshi ganin yanda yake bacci hankalinsa ya kwance ya duƙunƙune cikin lallausan duvet ɗin harararsa ta yi ta ce can ƙasa"mugu shi gashi ya zo yana ta baccinsa ni kuwa kullum bayana ya yi ta yimin ciwo" tsaki ta yi sannan ta ajiye masa wayar gefen bedside drawer juyawa ta yi zata fita sai kuma ta dawo ta ce"nima bari na ɗan kwanta na huta anan kafin ya tashi"tana gama faɗin hakan ta haye kan gadon ahankali kamar wata ɓarauniya haka har ta samu ta kwanta daga can gefe guda ta ja bargon ta rufa wata irin ni'ima taji tana saukar mata ta lumshe idanunta nan da nan bacci mai daɗi ya ɗauketa.

Wani irin azababben ciwo taji mararta na yi mata tun tana dauriya har ta miƙe daga kwancen duk ta haɗa gumi kamar wata wace take naƙudar haihuwa kuka ne ya kwace mata dan tasan irin azabar da zata sha nan gaba dan ita duk sanda zata yi period tofah sai duniya ta sani dukda Allah ya taimaka mata tana kaiwa wajen 4 to 5months bata yiba amma duk randa yazo mata tofah sai tasha baƙar wahala arayuwarta sau biyu ta taɓa yi sai kuma wannan karo na uku, ahankali ya buɗe idanunsa jin kamar sautin kuka ware idanunsa ya yi tass akanta ya miƙe yana kallonta da mugun mamaki amma ya kasa magana ganin yanda jikinta ke rawa sai zufa take yasa ya ƙara sa wajenta yana zuwa ya kalleta da sauri ta riƙe masa hannu bakinta na rawa tama kasa faɗa masa abinda take so ya sani ɗin, hannunsa ya ɗora kan goshinta yaji babu zafi kwata-kwata mamaki ya yi dan ya ɗauka zazzaɓin dare take, ahankali ya ce

"What wrong?"

Hannunsa ta kama ta ɗora daidai saitin mararta dan batajin zata iya yi masa bayani, kallon wajen ya yi sai kuma ya yi tsaki ya ce"toh ubanme zan miki nd me kika shigo yi ɗakin nan?" kuka kawai Fattomah ta sanya tana riƙe da hannunsa dan gani take kamar idan ta saki zata mutu ne, sauka ya yi daga kan gadon ya fita a ɗakin, bai wani daɗe ba ya dawo hannunsa riƙe da injection sai drip. Tana nan zaune inda ya barta ya gama haɗa allurar ya yima amma hankalinta baya wajen, yana sanya mata drip ɗin ya fice daga ɗakin ya koma parlon ya yi kwanciyarsa dan wani irin mugun bacci yake ji.

Kiraye-Kirayen sallar asubar da aka fara shine ya farkar dashi da sauri ya miƙe ya shige toilet dan ɗauro alwala dan ko sallar dare bai samu damar yiba, yana fitowa ya tarar da ita zaune kan gadon sai nuƙurƙusu take kamar wacce zata haihu, tsaki ya yi sannan ya ƙara so gabanta yana kallonta ya ce"keeeee" dakyar ta ɗago ta kalleshi idanunta duk sun sauya kala sun kumbura, taɓa jikinta ya yi yaji zafi zau saɓanin ɗazu, ganin kamar tana neman sumewa azaune ya sanya ya ɗaukota tamkar Baby ya sakko da'ita yana fita ya sanya driver ya taso ya shiga mota shikuma ya shiga baya yana riƙe da'ita ajikinsa.

*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*

*Like nd share*[5/17, 9:24 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.

*Ameenatou I Ibrahim*
Nanameera

PAGE 31-35.
Chapter 17 · 0% Book details