← Book details Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 34

Sashe 8

Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare AMATUƘAR razane NABEELAH ta farka daga nannauyan bacci take sakamakon mumunar mafarkin da tayi , lokacin ɗaya taji duk jikinta ya soma Bari sai wani kaduwa sassan jikin ta yake sai kace wacce aka tsamo daga ruwan sanyi hannayenta dake rawa tasa ta dafe de-de saitin zuciyarta dake bugawa da karfi, yanayin yanda jikinta ke rawane yasata cije labbanta, tare da lumshe sexy eye's d'inta kam-kam, tabbas ta yi matuƙar tsorata da wannan munannan mafarkin da tayi akan su Mommah da yaya AHMED ,Ahankali tadan soma jujjuya kanta da taji yayi mata nauyi sosai, da sosai, mafarking da tayi ya tada mata hankali matuƙa ya Kuma hautsuna duk wani tunaninta, yayinda wani irin tsoro me ɗauke da zallah fargaba ya lullubeta, kwata-kwata bata jin zata iya jurewa, domin kuwa zuciyarta ta karya sosai, tsoro take ji kada dreaming ɗin ta ya zamanto Gaskiya, hakan yasa Ahankali ta zuro da kafafunta ƙasa tare da saukowa daga kan bed ɗin ta kallon agogon dake sakale ajikin bango dakin tayi, duk da cewar cikin tsakiyar dare ne sosai bata tunanin akwai wani Abu da zai hanata zuwa garesa, fitowa tayi daga cikin bed room d'inta, Ahankali take tafiya, yayinda kuma zuciyarta ke cike da tarin tsoro, domin kuwa babu wani Abu dake motsi a cikin Gidan ko Ina ta dau shiru..
Kasancewa a wannan lokacin da yawan mutane sunyi Nisa a cikin baccinsu. Sam bata damu da duhun da ya mamaye parlourn ba kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn,tana fita, Kai tsaye ta nufi kofar da zata Sada ta da part ɗin AHMEDh ,duk da cewa a yanzu zuciyarta ta Fara kawo mata wani Abu me Kama da tsananin tsoro Sai dai Sam bata jin akwai Abun da zai hanata zuwa garesa a wannan dare, dan ita bata kan Mommah take ba dan ita ma Allah yasa Yan fashin su kashe Mommah ita meye ruwanta , babban burin ta kawai ta isa garesa domin kuwa zuciyarta cike take da son ganinsa, saboda ba kadan ba mafarkin da tayi akansu ya daga mata hankali. Tana isa daidai part d'insa, d'aura hannunta akan handle d'in kofar parlour tayi tare da tura kofar cikin Ahankali ,ta shiga cikin parlournsa,sassanyar kamshi da kuma sanyi A/C ne suka daki kan fuskarta. Wanda hakan ya tilasta mata lumshe beautiful eyes d'inta, tare Kuma da buɗe su alokaci guda , ayanzu kam ta fahince cewa shi ɗin mutum ne me mutukar son kamshi. Ahankali ta shiga dan sai yau take Kare parlour nasa kallo, Wanda komai dake cikin sa yake nit babu alamar datti ko akasin Haka, duk da cewar babu yalwatacce light a cikin parlourn ,,,Dan blue light ne kadai ke kunne, amma hakan baisa ta daina ganin tsarin parlourn sa ba,
Gaba daya zuciyarta ta Riga da ta karye da tunaninsa, hakan yasa kaitsaye ta nufi daya daga cikin kofar dake cikin parlourn ,Wanda Kuma anan bed room d'insa yake,
Bata ko tashi jin fargaba da matsanancin faduwa gaba ba, Sai da ta k'araso jikin kofar bed room d'insa ta tsaya, dan lumshe idanuwanta tayi Tana me sauraran yanda zuciyarta take bugawa da sauri-sauri, nan take wani irin tsoro ya lullubeta, Abu guda biyune aranta Wanda na farkon shike Kara karya mata zuciya, domin kwata-kwata batason ace mafarkin da tayi akansu ya tabbata musamman shi..
Chapter 8 · 0% Book details