← Book details Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 34

Sashe 27

Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Agurguje*
*bayan wata uku*
AHMED ne na hango yana Zaune a Saman lumtsumemiyar two-seater d'insa a cikin parlour sa ,tare da Abdul, "kallon sa Abdul yayi kafin cikin kulawa Abdul yace " AHMED wannan matsala bafa karama bace ,babba'ce,
Mudin idan aka sake nan da wasu yan kwanaki dolene MOMMAH ta gane, kasan halinsu na mata . Abdul ya karasa maganar sa idonsa akan sa ,Dan runtse idanunshi AHMED yayi cikeda ciwo zuciyanshi namai zafi yanamai radadi sanan gently ya buɗe idanunshi ya daura su akan Abdul kafin cikin tsantsan damuwa AHMED yace"Abdullah nikai na abun nan yana damuna, wallahy ALLAH Jiya ban iya bacci ba,duk da dai da na yanke shawaran cewa zan bar garin nan. Inya so idan na tafi idan abun yafaso zan dawo daga baya, amma tasirin da NABEELAH take dashi agare ni acikin zuciyarta ya sa bazan iya ketarewa ba ko nan da can , cikin sauri Abdul ya furta
"AHMED Ina da wata shawara mezai sa bazakaje wajen likitan gidanku ba.. doctor Adam's,ka fad'a masa komai kada ka boye masa, lokacin da kake gabansa kazama tamkar maraya,,,cikin tsantsan damuwa AHMED yace"wannan ba shawara bane ,dan idan nayi haƙa kamar naɗauki asiri nane nayi tallah ,,,,girgiza kansa Abdul ya yi kafin cikin bashi shawara da kwarin gwiwa Abdul ya ce"amma halin maza dana mata ya babbanta,insha Allahu doctor Adam's zaisamar mana mafita ,idan bazaka damuba muna iya zuwa gurinsa yanzu nan,ba sai gobe ba Please ka tashi muje mu sameshi da batun wata kila asamu mafita agunsa tashi sukayi kai tsaye suka nufin hanyar fita daga falon tare da ficewa daga
gidan gaba ɗaya

*BAYAN MINTI TALATIN*
*GIDAN DOCTOR ADAMS*
Zaune DR ADAM yaƙe acikin parlournsa tare da AHMED da abokin AHMED wato Abdul kallon AHMED doctor Adams yayi tare da"AHMED yayadai ,meke tafe daku ,ko wanine ba lafiya,? Doctor ya tambaye AHMED cike da kulawa ,dago kansa yayi tare da sauke idanuwansa akan doctor Adams ƙafin
cikin faɗuwar gaba
da girmamawa AHMED ya buɗe baƙin sa yace "eh doctor nine banda lafiya Kuma ina sa rai Insha ALLAHU indai muzo wajenka zan samu magani cutar dake damu na "to amma kuma Ikon ALLAH, haƙa ba wanda zai ganka yace kanada wani lalura ,koda yaƙe wani cutar zaka ga ba ganin ta ake ba, meke damuka?? Doctor ya jefo masa tambaya kai
tsaye idonsa akan su
Gyara zamansa Abdul yayi haɗe da cewa " doctor babu abunda zamu boye maka.mu tasone.tun daga gida.da niyar farke maka sirin da ke tare da mu, dan girman ALLAH ,muna nemar mafita Abu biyu. Abu na farko karike mana sirin mu, nabiyu muna nemar mafita a gareka Abdul yaƙare maganar yana mai
kallon doctor Adams,
cikin kulawa doctor Adams yace"wannan bazai zamana da damuwaba INSHA ALLAHU.zanyi iya kok'arina inga na taimaka maku, in har taimakon baifi karfi naba, kuma INSHA ALLAHU zaku sameni mutum mai siri.Wanda ta gefena sirinku bazai fitaba insha Allah doctor Adams yaƙare
maganar sa
idonsa akan su
,Cikin zubar da hawaye Abdul yace"doctor kuruciya .dason zuciya ita tahaifar dawata ƙaddara,akwai wata yarinya nasan zaka santa, kanwace gunsu AHMED,NABEELAH yanzu haƙa maganarda mukeyi dakai tana ɗauke da cikinsa,wato cikin AHMED, sannan kuma,
Duk likitan da akaje wajensa domin fitarda cikin kafin zuwa wannan Lokacing sai ace da akwai matsala atare da mahaifanta, mudin akace za'a cire cikin zata iya rasa ranta Abdul ya ƙare maganar yana mai dukar da kai ƙasa shima AHMED ɗin dukai da kansa yayi yana mai zubar da hawayen danasani da nadamar abun da yakaitawa kanwansa "kai kai kai haba doctor Adams yafaɗi maganar ataƙaice, sannan cikin ɓacin rai doctor Adams ya cigaba da cewar "AHMED kayi kuskure ,kayi kuskure, kayi kuskure babba , AHMED banji daɗin jin wannan labari ba,kayi kuskure, toyanzu menene mafita, mekake son ayi, ?? doctor Adams ya tambaye AHMED
idonsa akan AHMED
Cikin zubar da hawayen danasani AHMED ya d'ago 'kansa haɗe da cewa "duk wani taimakon da ya dace ayi mana, shi nake roko ayi mana doctor. dan. Banason MOMMAH tasan halinda ake.ciki AHMED yaƙare maganar sa yana mai zubar da hawaye tsoro damuwa da tashin hankali
da yaƙe ciki ,
Cikin tsantsan bacin rai doctor Adams yace"yanzu ita NABEELAH tafara yin laulayine?"
,,,,,,Cikin sauri AHMED ya furta"Eh, takan dan kwanciya amma nakan matsa mata ta tashi,,
, Doctor Adams yace "
to yanzu abunda nakeso dakai idan ka koma gida, kajeka same ita NABEELAH kace mata takwanta sai ta gayawa MOMMAH bata da lafiya, nasan ni ace inzo in dubata, to in nazo nasan dame zan ɗaura ,koya ? "hakane suka haɗa baƙin gurin faɗin haƙa,,,, doctor Adams yace "ku kwantar da hankalin ku ,zan taimakeku in ALLAH ya yarda, "Allah yasa Inji cewar Abdul "AMIN inji cewar doctor Adams sannan ya cigaba da cewar "to gashi kunzo gidan goro dasai ahaɗa maku abun breakfast ko ba zaku sha ba ??"aa munagodiya Allah ya saka da Alkhairi ba matsala "haha haha haha doctor Adams ya kwashe da dariya tare da faɗin"to Allah yasa mu dace "Amin ya rabbil izzati suka haɗa baƙin gurin faɗin haƙa zalika suna mai mik'ewa
tsaye atare
,Kallon su doctor Adams yayi kafin cikin kulawa doctor Adams yace"zaku tafi ne? "eh suka furta
"to shikenan
Thank you. so much, Inji cewar doctor"cikin sauri suka haɗa baƙin gurin faɗin"doctor Adams muke da godiya Allah ya ƙara girma "amin doctor Adams ya furta,kana sukuma suka nufin hanyar fita daga cikin falon tare da ficewa daga gidan gabaki ɗaya

*GIDAN GIDAN HAJIYA NAFISAT*
Da misalin ƙarfe biyar
Zaune HAJIYA NAFISAT taƙe acikin parlournta tare da AHMED da NABEELAH da doctor Adams
Gyaran zamansa doctor Adams yayi kafin cikin nutsuwa haɗi fara mata bayanin rashin lafiyar yaƙe damu NABEELAH doctor Adams ya buɗe baƙin sa yace "wato Hajiya ciwon da yaƙe tare da NABEELAH, girgiza kansa yayi tare da cigaba da cewar" Kai Allah dai ya kyauta , Cikin faɗuwar gaba Mommy ta furta"Amin ya Rabbi izzati idonta akan doctor Adams,,cikin nutsuwa doctor Adams ya kalli Mommah kafin cikin kulawa doctor Adams ya buɗe baƙin sa yace"wato da NABEELAH ta sanar daku dawuri ,
ciwon da yaƙe tare
da NABEELAH
,Wato ciwon yana shiga ne lokaci guda ,sannan shi ciwon baya nunawa. kuma yana haifar da abubuwa biyu zuwa uku. na farko yana haifarda ƙasala, kuma zakiga 'kafafun mutum sun kumbura, kai in ciwo yayi karfi ma yakan sa ,kiga har cikin mutum ma yana kumbura, cikin sauri Mommy ta furta"doctor to yanzu meye mafita, cikin wannar Al'amarin,??
,,,,cikin nutsuwa doctor Adams yace"to Hajiya a nan dai bamu da asibity, da yaƙe kula da irin wannan lalurar. sai a American,amma akwai
wani asibity a Abuja Wanda abokina ma yaƙe kulada asibity ,su suke kula da irin masu wannan laluran kuma suke ɗaukarsu zuwa
American d'in,to Ina ganin zaiyi kyau idan mukayi gaggawar yi mata biza sai mu ɗauke ta ni da AHMED mukai ta Can Abuja sai su. wuce ƙasan wajen
"kuka ne ya subcewa MOMMAH cikin shesheskar kuka Mommy tace "doctor ba damuwa nagode Allah yasaka da Alkhairi, anjima zan turo maka AHMED sai yazo duk wani abunda ya dace da za'ayi cikin gaggawa sai ayi "cikin smiling doctor yace "ok to Allah ya kaimu,maida kallon yayi inda AHMED yaƙe zaune Tare Da cigaba da cewar"AHMED muje waje akwai karin bayani da zan maka Allah ya sauwake,"Amin ya rabbil izzati Inji cewar Mommy,mik'ewa suka yi tsaye sannan suka nufin hanyar fita daga cikin falon duban NABEELAH Mommy ta yi tare da faɗin"Sannu ko ƴata ALLAH ya baki lafiya inji cewar Mommy
Batare da NABEELAH ta tanka ba ta lumshe ido tana jin yanda gaban ta ke fad'uwa, ALLAH ka rufa mana asiri duniya da lahira NABEELAH ta faɗa acikin zuciyarta,wai meyasa NABEELAH kika biyewa son zuciya har ta kai ki ga aikata zina NABEELAH ta tambaye kanta bayan kuma tasan bata da amsa ALLAH ka gafarta min zunubai na Wanda nasani da wanda ban sani ba Insha ALLAHU daga yau na tuba. *Alhamdu'lillahy Allah Nagode maka da kaba mahaifiya ta lafiya Allah ka ƙara mana lafiya Tare Da tsawon rai mai albarka fans*
*Thanks for uzurin ku agare Ni Dan Allah kucigaba da min uzuri watatan sai labari wayan da suke kirana da masu turo min sako Alhamdu'lillah jikin mama da sauki ina matuƙar godiya Allah ya saka da aljanna*💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

*FAREEDAH NABEEL*

🌹
💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

_STORY,WRITTEN_.

BY
*A'ISHA FULANI GAL*

*🌺 CHAPTER 29-30🌺*

MY DEAR DADDY
MAY YOUR SOUL REST IN PERFECT PEACE
DAD ALLAH YAJI KAN KA DA RAHAMA Daddy ALLAH YASA CAN TAFI MAKA NAN,,,,,,, ALLAH YASA ALJANNA FIRDAUSI MAKOMACE AGAREKA

DEDICATED TO :- ƘAWATA XAYYNEB💤💤💤(XEXEN FASAHA)

*WANNAN PAGE ƊIN NA SADAUKAR DASHI GARE KU* Kawata Ummu addiyah ,Dr adamarhh,,Matan rabiu
Queen beauty,,Nice girl
Me suna da Arabic
Maman zee,, Tah Annabi
Mar'atussaliha ,Sahiba
*Ina matuƙar jin daɗin ZAZZAFAR COMMENTS NAKU ALLAH YA SAKA DA ALJANNA*

*SAKON GAISUWA GA MY BRODA SAPWAN DA ƘAWATA UMMU ADIYYAH*
*FATAN ALKHAIRI NAKE MAKU A DUKKAN RAYUWAR KU,UBANGIJI YA ƘARE KU DAGA SHARRIN MAKIYA DA MASU YI MAKU HASSADA*

*🌺 CHAPTER 29-30🌺*

*YAU Ma NO🤦🏻‍♀️ EDITING 🤦🏻‍♀️*
*_BALOKACI EDITING_*
Chapter 27 · 0% Book details