← Book details Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 34

Sashe 18

Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Happy Friday masoya na Allah ya sada mu da ALKHAIRI da ke cikin wannan rannan Allah ya gafarta mana kura kuran mu yasa mu cika da kyau da imani fatan ALKHAIRI fan's
[7/4, 4:43 PM] Fulani Gal✍🏻: 💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

*FAREEDAH NABEEL*

🌹
💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

By
*A'ISHA FULANI GAL*

*🌺 CHAPTER 19-20🌺*

*DEDICATED TO :- ƘAWATA XAYYNEB💤💤💤(XEXEN FASAHA*) *ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKI A DUK INDA KIKE INA MAKI SON FISSABILLILLAHI XAYYNEB 💤 XEXEN FASAHA*

*ƘAWATA UMMU ADIYYAH*
*FATAN ALKHAIRI NAKE MAKI A DUKKAN RAYUWAR KI,UBANGIJI YA KAREKI DAGA SHARRIN MAKIYA DA MASU YI MAKI HASSADA*

❗❗ *GARGADI* ❗❗
*BAN YARDA WANI KO WATA YAYI MIN AMFANI DA WANI BANGARE DAGA CIKIN LITTAFINA BA SANNAN KUMA BANYARDA WANI KO WATA SU SAUYA'MIN LABARI BA SAI DA IZZINI NA IDAN AKA SAMU AKASIN HAKA BANYAFE BA SO A KIYAYE*

*🌺 CHAPTER 19-20🌺*

GIDAN NABEEL
Zaune FAREEDAH take a saman kujera a cikin falon su tayi tagumi da ka ganta kasan tana cikin tsananin tashin hankali da damuwa yayinda ta nutsu cikin duniyar tunani can sai ga wani kyakkyawan matashin saurayi mai matukar kama da FAREEDAH ya shigo cikin falon su FAREEDAH ,Abbacar kanin FAREEDAH ne yashigo cikin falonsu FAREEDAH tare da furta sallama.....
Abbacar ne ya shigo cikin falonsu FAREEDAH
tare da furta

"ASSALAMU ALAIKUM!!!

Kai tsaye cikin sauri ya ƙaraso inda FAREEDAH take zaune ta zabga wata uwar tagumi ,cikin tashin hankali Abbacar ya kalli yayarsa FAREEDAH kafin cikin kulawa da tashin hankali ABBACAR ya bude baƙin sa
ya shiga kiran sunanta"Aunty FAREEDAH! Aunty FAREEDAH !! Tunanin me kike yi haƙa?yana ganki acikin yanayin tashin hankali da damuwa? tunanin
me kikeyi haƙa ????.ya karasa tambayarta cike tashin hankali da tausayawa
Firgigit FAREEDAH tayi ta dawo cikin hayyacin ta tasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, yaushe Abbacar yazo bata sani ba? cikin salon basarwa tare da murmushi mai ciwo FAREEDAH tayi kafin cikin kulawar FAREEDAH ta buɗe baƙin ta tace" ABBACAR
daga gida kake? ya su Mama da Baba? ta ƙarasa maganar ta tana mai kallon sa """""""'''cikin kulawa Abbacar ya bude baƙin sa yace"hmmm Aunty FAREEDAH babban abunda ke damunki shi kawai nakeso ki faɗa min, kinga ko da zanzo gidanki,sai da Mama tace in faɗa miki cewa ki daina tunani ,amma yanzu nakara zuwa na taddake a cikin tunani ABBACAR ya ƙare maganar cikin wata irin murya mai cike da tsananin tausayawa yar Uwar tasa

"ABBACAR abune mai matuƙar wahala in cire tunani atattare ni alokaci ɗaya ,ga NABEEL zai yi doguwar tafiya, zai fita ƙasan waje dan ya ƙaro couse akan har kokinsa magana aure kuma babu shi, yayin Haƙa ne dan yasamu damar da zai dawo dani, FAREEDAH ta kare maganar ta cike da tarin damuwa ,,,,,,cikin farin ciki ABBACAR ya furta "Aunty FAREEDAH ba gashi anci nasara ba kin dawo dakin mijin ki ba,ko kina tunanin cewa zata fitar da ke?? Abbacar ya karasa maganar sa idanunsa akan ta.

"hmmm injin cewar FAREEDAH sannan cikin sanyin murya FAREEDAH ta cigaba da cewar"NABEEL ba zai yi kwana goma da tafiya ba zan bar gidandan nan, Abbacar Ina son miji na bazan iya kwatanta maka irin kishin mijina da nike ba,, cikin sauri ABBACAR ya bude baƙin sa tare da faɗin "Aunty FAREEDAH akwai wata shawara da nake so in baki , amma bansaniba ko zaki amince da ita,
Asma'u dai kawar ki ce kuma aminiyarkice, kuma likita ce , zan so ace tashigo cikin shawara nan da zan ba Yar, ..cikin sauri FAREEDAH ta furta"wata irin shawara ce? Tabbas nasan Asma'u zata iya biya min bukata ta ko wace iri ce "samu guri yayi ya zauna yana mai sauke ajiyar zuciya tare da furta barin in huta tukkun kafin in faɗa maki shawara da na yake" okay to barin in kawo maka ruwa da ɗan wani abun tabawa FAREEDAH ta ƙare maganar ta sannan cikin sauri ta faɗa kitchen

*GIDAN HAJIA NAFISAT*

Kwance AHMED suke saman Bed yayinda da Nabilah take kwance a gefensa sai famar sauke ajiyar zuciya take zuwa can kuma sai NABEELAH ta furta ban gaji ba tana mai hayewa saman AHMED cikin natsuwa NABEELAH Ta rankwafa a kansa ta sanya masa ... d'inta a bakinsa ya cafka da sauri tare da Kama dayar ....d'inta da Dayan hannunsa yana Jan kan.
sun jima kafin suka gajiyar da junarsu ta hanya gamsar da junna su ,daukarta yayi cak suka shiga cikin bathroom sukayi wanka tare sannan suka fito,suka shirya, bayan sun gama shirin "sannan FAREEDAH ta tuna da cewa dare yayi ,duban AHMAD NABEELAH tayi kafin cikin sanyin Murya NABEELAH ta furta "yanzu karfe sha biyu! "kallon agogon da yake manne ajikin bangon dakin AHMED yayi tare da faɗin"ai duk ke kikaja mana injin cewar AHMED sannan cikin faɗa Ahmad ya cigaba da cewar" sai danace maki ki tafi amma kika ki kika ce wai ke baki gaji ba "hmm uhmm injin cewar NABEELAH sannan ta cigaba da cewar"badam wani Abu ba da bacci na kawai zan yi anan cikin bed room dinka,dan so nike na kwana a cikin jikin ka yayinda nake shashakar daddadar kamshin turaranka jikinka ,sai dai ina gudun kar Mommy tashigo dakina bata ganni ba NABEELAH ta ƙarasa maganar ta cikin shagwaba haɗi da turo baki"cikin daure fuska AHMED ya buɗe baƙin sa yace" a gaskiya ni tsoro nake ji kinga irin abunda yaso ya faru kenan jiya,ɗauko littafin da yake ajiye asaman gado AHMED yayi yana mai mika ma NABEELAH kafin cikin natsuwa AHMED ya buɗe baƙin sa yace"ki tashi ki tafi kanki tsaye idan Mommy ta tareki kice wannan littafin kike son kiyi nazarinshi cikin dare kuma dakyar muka same shii "amsar littafi NABEELAH tayi haka zalika tana mai faɗin,"AHMED kenan sarkin tsoro da wayau ,haha haha ta fashe da dariya sannan cikin dariya tana mai cigaba da fadin" bara in je good night sugar baby ,kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin dakin,sauke ajiyar zuciya AHMED yayi yana mai faɗin Allah ka rufa mana
asiri duniya da lahira

NABEELAH kuwa direct ta nufi hanya da zai Sada ta da part dinsu,ahankali ta murda handle din kofar parlour,tare da shiga cikin parlour ,tana gama k'arasa shigowa cikin parlourn, haka zalika yayi de-de da kai dubanta zuwa ga kan kujeran ,a daidai lokacin ne kuma narkakkun idanuwanta suka sauka a kan Mommy wacce take zaune a saman lumtsumemiyar kujeran parlour su,tayi facing d'in TV tana kallon film, ita kuwa Mommy tana ganin shigowa NABEELAH tayi saurin furta "NABEELAH me kike har yanzu baki je kin kwanta ba? Mommy ta k'arasa tambayarta idanunta akanta "duban Mommy NABEELAH tayi Kafin cikin sauri NABEELAH ta buɗe baƙin ta tace"wallhy Allah Mommy mu tsaya duba wannan littafin ne saboda in son zan yi karatu anjima NABEELAH takarasa maganar ta haka zalika tana mai nuna ma Mommy littafin hannunta "sauke ajiyar zuciya Mommy tayi ta kafin cikin sanyin Murya Mommy ta buɗe baƙin ta tace"kingani nima nan wani film nake kallo na kasa tashi maza kije ki kwanta maza maza kije ki kwanta good night sleep well "alright to sweet night and lovely dreams
dear Mommy
*WASHE GARI*
Zaune AHMED yake acikin parlourn shi tare da NABEELAH daga ganin Alamun hiran soyayyar su suke cikin nishadi had'i da farinciki,
zuwa can kuma sai NABEELAH ta ji kamar zuciya ta yana tashi, tana jin kamar zatayi amai amai, kakarin Amai ta Fara yi,ai kuwa da gudu ta tashige cikin bathroom,tana ta kwara amai,tana aman tana nishi sama sama haƙa zalika tana mai faɗin"wayyo Allah na haka dai tayi ta kwara amai kamar zata amayo ƴaƴan hanjin cikinta,tana kammala amai, ta had'a ruwan dimi ya cika bath sannan ta cire kayan jikinta ,ta shiga cikin ruwan bath 🛀d'in, sosai gasa jikinta da ruwan dimin, Tana gama wankan ,ta fito daga bayin daure da towel d'inta, AHMED kuwa yana ganin fitowar ta daga bayi yayi saurin ƙaraso gun ta kallon ta yayi kafin cikin kulawa da tashin hankali AHMED ya buɗe baƙin sa yace"ko NABEELAH meye yake damu ki .kike amai haƙa? "sauke ajiyar zuciya NABEELAH tayi kafin cikin natsuwa NABEELAH ta buɗe baƙin ta ce" wallhy AHMED yau kusan wata na ɗaya da yan kwana ki banga al'adana ba,ta karashe Maganar ta idanunta akansa"
Cikin sauri Ahmed ya furta

"Ban fahince ki ba ??

Cikin sauri NABEELAH ta furta"AHMAD ina ganin kamar ciki ne dani

"Ciki! ciki!! Cikiiiiii AHMED ya furta cikin tarin mamaki haƙa zalika yana mai kallon ta from a to z sannan cikin mamaki AHMED ya cigaba
da cewar
"Keko a Ina kika samu ciki ??

"Kamarya inji cewar NABEELAH sannan cikin bacin rai NABEELAH ta cigaba da cewar" akwai wani da namiji da nake bine bayan Kai,girgiza kanta NABEELAH tayi sannan cikin zubar da hawaye NABEELAH ta cigaba da cewar" kaga ni koh dama ni irin abunda nake gudu kenan ta karashe maganar ta cikin dan daga murya.

"Cikin daka mata wata uwar tsawa AHMED yace "ke NABEELAH bari kiji abunda zai fito daga cikin bakina kame baki agareki ya zamo wajibi idan kuma ba Haƙa ba zakiyi rub'i da rubabb'iyar azara AHMED ya k'arasa maganar sa cikin tsananin zafin da bacin rai "ita ma NABEELAH cikin fusata da daka masa wata uwar tsawa NABEELAH ta buɗe baƙin ta tace "Kai AHMED ya kake Furta min wannan mugum kalman naka,me kak'e nufi da wanyan mugayen kalaman naka?? "cikin tsawa Ahmed yace "Ina nufin wannan cikin da yake jikin ki kije ki nemi meshi d.....cikin fusata NABEELAH ta katse shi ta hanyar faɗin"karya kake yi AHMED, wallhy shaye shaye da ake yiwa kanwah ba'a isa ayiwa barkonoshi ba """"""""""""""cikin mugun faɗa AHMED yace"me kike nufi da wannan kalmar taki ??inji cewar AHMED cikin sauri"""""""""""""cikin tsantsan ɓacin rai da masifa NABEELAH tace "Ina nufin abubuwa da maza suke yiwa mata wallhy ni sai dai mu kwashi kashin mu a hannu..

Cikin fusata AHMED ya buga mata wata uwar tsawa tare da faɗin "zako mu zuba mu gani za'a ga na Wanda zai ......*wash nagaji fan's mu haɗu a next page masu zazzafar Comment ina matuƙar godiya Allah ya saka da ALKHAIRI ALLAH ya ƙara mana lafiya Tare Da tsawon rai Mai albarka Allah ya gafarta mana kura kuran mu*

💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

*FAREEDAH NABEEL*

🌹
💖💖💖💖💖💖💖💖
💗💗💗💗
💖💖
🌹

_STORY,WRITTEN &EDITED_.
Chapter 18 · 0% Book details