← Book details Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 34

Sashe 13

Fareedah Nabeel Complete Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

..D'auka ɗauka ɗauka maza maza kije ki ɗauko jakarki, kisan wani abu ɗaya! uzuri ɗaya zanmaki kishiga ki ɗauko wannan akwatin naki shi kaɗai zaki ɗauko baƙida wani abunda zaki d'auka awannan gidan de-de da tsinke da allurah bazaki fita dashi anan gidanba,jakar nan ma shima dalilin aure yabaƙi shi shiyasa zanbar maki akwatin, maza kije kishiga ki ɗauko jakar ki ,cikin daka mata tsawa ta cigaba da cewar"nace maza-maza ki tashi mana ki ɗauko, kizo ki fita kiba mutane waje
shashasha kawai bak'ar juya
"Hannun FAREEDAH dake tsananin rawa ta ƙarba takardan saki batare da ta buɗeba kai tsaye FAREEDAH ta nufi hanyar upstairs tare da haurawa saman upstairs
Kuka zuwa Wannan lokacin ya 'dauke mata zuciyarta bayan radadi da tsananin kunci babu abinda take mata
dan ahaka ta tattara kayanta da duka abubuwanta ta fito kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin d'akin tare da saukowa daga saman upstairs,tsayawa tayi tana mai kallon mijin cikin zubar da hawaye "kallo ta Mommah tayi kafin cikin daka mata tsawa Mommah tace"zaki wuce ko kuwa!
'Kai tsaye FAREEDAH tanufi hanyar fita daga cikin parlourn cikin sauri NABEEL mike tsaye da niyar zai bita ,"Ina zaka? inji cewar Mommah cikin fusata sannan cikin daka masa tsawa Mommah ta cigaba da cewar"ai ta gama fita daga hurumimka dan Allah my friend dawo kazo ka zauna fool shanyayye ka tashi zagwayzagway dakai zaka bita to me zakaje kai mata maza-maza fita ki ba mutane waje,kai kuma ka dawo nan ka zauna.kai kana ma bada kanka abanza to me zakayi mata kasake ta babu wani abinda yarage atsakaninku shi dai NABEEL ɗin shiru yayi ƙana kuma har izuwa yanzu kwata-kwata ƙasa cewa komai sai famar zubar
da hawayen dayake,,,,,,,,ɓangaren FAREEDAH ko tana mai ƙarasa fitowa tsakiyar compound din gidan kai tsaye ta nufi hanyar fita daga gidan gaba ɗaya ,tana fitowa bakin titi adai-adai sahu ta samu ta tare ba tare da ta sanar dashi inda zai kai taba ta shige,,,da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare NABEEL yafito compound din gidansa
NABEEL ne ya fito tsakiyar compound d'in yana k'arasawa bakin kofar motar ya buɗe mata motarsa ya shige sannan ya rufe murfin motar cikin sauri ya tada motar tunkan ya ƙaraso gate man ya wangale masa gate da wata aniyar gudu yafice daga gidan,daga ganin yanayin yanda yake tukar motartasa kasan yana
cikin yanayin tsananin damuwa da tashin hankali sai faman-sharara gudu
yaƙe asaman titi
haƙan yasa cikin minti Ashirin ya ISO babban katafaren Hotel wajene dayake ɗauke da yalwar mutane wasu zaka gansu atsakiyar compound din hotel din yayinda da kuma wasun su kuma zaka gansu a cikin babban parlourn Hotel d'in, duba da irin yanda dayawan mutane wajen keta had'a hadayansu kowa harkan gabansa yayinda Wanda kuma da yawansu samarine da yanmata sannan kuma daga ganin yanayin shigar jikinsu kadai zaka gane ko su ɗin suwaye ne domin kuwa babu wata ƴa mace ko daya awajen da take sanye da shigar mutunci yayinda da yawan mutane dake zaune a cikin babban parlourn wajen suke enjoying cool music d'in dake tashi awajen ta hanyar rawa tare da romancing din junarsu hakika daga ganin yanayin tsarin wajen kadai zai tabbatar maka da cewa ba wajen zuwa kowa da kowa bane sai dai wayanda suke jike acikin nairori musamma duba da irin tsala-tsalan hadaddun maza da kuma yan matan dake wajen saboda da sudin ba Irin gama garin Samari da yan mata nan bane tun shigowar NABEEL farfajiyan waje, da idanuwansa suka sauka akan tsirarun yan mata dake ta shawagi awajen da kuma wasu dake cikin tafkeken swimming pool din dake tsakiyar compound d'in,suna swimming acikin ruwan, Cikin sauri NABEEL yayi ƙasa da idanuwansa tare da kawar da kansa gefe, cikin wani Irin yanayin takun da yake yi ne, cikin kasaita da tabi jinin jikisa ya jawo hankalin mutane da yawa dake wajen ya dawo kansa kasancewa tun shigowarsa wajen hasken fata da Kuma kyawun fuska hadi da murdaddiyar sura jikinsa ya ɗauke hankalin mutane da yawa, shikuma duk da yasan da yawan mutane dake wajen kallonsa suka yi amma Sam bai damu ba, saboda idan da sabo yasaba da irin Haƙa
Kai tsaye gurin da ya zama kaman nanne babban parlourn cikin hotel din ya nufa daya daga cikin hadaddun kujerun dake wajen yaja yazauna asama tare da daura kansa anan kan. Dan table din dake gabansa ... NABEEL kuwa ya sunkuyar da kansa yayi a Samar table din gabansa...ya shiga cikin duniya tunanin da tsananin tashin hankalin da yake ciki, komai yayi masa zafi yarasa Ina zai sa kansa yaji daɗi ,wannan wane Irin masifa ce Haka!! Mommy wai wanne irin laifi FAREEDAH ta aikata maki ne wai kika tsaneta haka!!
ɗaya daga cikin masu aikin wajene ya ƙaraso inda NABEEL yake zaune,yana mai Kallon sa kafin cikin ɗan rusunawa haɗi da girmamawa ma'aikacin ya buɗe bakinsa yace"barka da zuwa ranka yadade maiza'a kawo maka? "Cikin nutsuwa NABEEL ya ɗan dago da kansa jin murya mutum akansa yakalli mutumin, yanayin fuskarsa ne ta chanja duk da kuwa bai taba zuwa wajen ba domikuwa wannan ne karonsa na farko, wani abun mamaki ma shi ne kwata-kwata baisan dalilin daya kawosa wajen nan ba, hakanan dai ya samu kansa da shigowa wajen, cikin damuwa gami da tashin hankali NABEEL ya buɗe baƙin sa yace"
Ka bani drinks
'yayin da shi kuwa mutumin dake tsaye kuwa jin NABEEL d'in ya ambaci drinks ne Haƙan yasa shi gane cewa kwata kwata NABEEL din bai taba shigowa wajen ba, domin kuwa duk Wanda ya shigo gurin nan giya yake saye yasha,idan kuma da budurwarsa ce yazo sai sun sha giyan sun shawu Sannan saurayin ya kama masu ɗaki dansu huta su jidadinsu ɗan rusunawa ya sakeyi tare da cewa "I'm am sorry Sir bamu da normal drinks saidai Wanda akayi mix ɗinsa sai kuma alcohol and wine non alcoholic 'NABEEL ko jin mutumin ya anbata masa alcohol ne yasa shi saurin dago kai ya kalleshi saboda shi tunda yake aduniya bai taba shan alcohol ba kai Allah ma yatsare shi dashan giya duniya da lahira cikin sauri ya girgiza kansa tare da kama labbansa a cikin bakinsa ya Ɗan ciza, cikin muryarsa da bata fita sosai ba cikin sanyi da kasa da murya NABEEL yace"kabani wine amma non alcoholic "okay sir inji cewar ma'aikacin yana mai juyawa
cikin sauri ya tafi Dan kawowa NABEEL ɗin wine kamar yadda ya bukatar bajimawa kuwa mutumin ya dawo hannunsa ɗauke da kwalbar wine da kuma Wani glass cup ajiye kwalbarn yayi agaban NABEEL d'in 'tare da juyawa yakoma bakin aikinsa, NABEEL kuwa ɗaukan kwalbar wine din yayi batare kuma da ya duba ko wine din neko non alcoholic bane, yaballe murfin ya zuba wine d'in a cikin cup bai ku ma damu da yawan wine d'in da ya zuba acikin cup din ba sai da ya cika cup din dam sannan ya kafa kofin a bakinsa ya fara sha bai kuma cire cup din daga baƙinsa ba har saida yaga ya shanye gaba daya win din dake cikin kofin, Ahankali ya ɗauki wayarsa dake aje a Saman table din tare da kunnata kifa kansa akan table din dake gabansa yayi, hade da turawa hoton FAREEDAH dake mamaye akan screen d'in wayar idanu, idanuwansa da suka sauka a kan kyawawan lips d'inta yadan lumshe, tare da fesar da wani irin numfashi me sanyi FAREEDAH
INA MATUƘAR SONKI! BA ZAN IYA KWATANTA MAKI IRIN MATUƘAR KAUNAR DA SONKI DA NAKE MAKI A CIKIN ZUCIYA TABA KAUNAR KIDA SONKI YANA YAWO A JIJIYOYIN JININ JIKINA,I CAN DO WITHOUT YOU ,YOU ARE MY HAPPINESS Ahankali NABEEL ya fad'a ta hanyar motsa pink lips ɗinsa
Kwanta da kansa akan table din yayi saide Kuma wani abu mamaki ko mintuna 20 ba acikin da shan wine d'in nasa ba ya ji kansa
Na dan juyawa yayin da idanuwansa ke sake marairaicewa, tamkar Wanda yake jin bacci Haƙa yanayinsa ya dawo musamma ma idanuwansa da suka soma juyewa, haɗi da chanja launi, take kuma cikin mintuna kadan yasake jin duniya tana nema juya masa ganin da yayi cewa da gaske yana neman fita acikin hayyacinsa ne haƙanyasa shi mik'ewa tsaye, tare da ɗauka wayarsa, wallet d'insa dake cikin aljihunsa ya ciro tare da budewa batare da kuma ya dubaba yaciro fararen yan one one thousand ya ajiye musu asaman table d'in,
Ahankali cikin yanayin da yake jin kansa ya fice daga cikin babban parlourn,koda ya fito tsakiyar compound d'in, kansa yadan buga, saboda yanda yake wani jin jiri na nema kai shi ƙasa, a cikin zuciyarsa yake tambayar kansa shin ma Meye kawosa wajen nan? ,gashi sanadiyyar tashin hankali da yake ciki haƙan yasa shi zuwa nan wajen sannan kuma yasa shi shan abunda yake nemar dagula masa lissafi duk laifin kine Mommy kece sila Allah ya isa tsakanin na dake Mommah, cikin dan cijewa ya nufa inda ya ajiye motarsa yana zuwa kuwa ya bude murfin motar nasa ya shiga, ya tada motar sa, da wani irin mugun speed kuwa ya cillah motar kan titi gudu yake yi sosai akan titi
Kai tsaye ya nufi gidan sa, yana isowa gaban makeken Gate din Gidan sa ne haƙan yasa Shi soma Danna wani irin uban horn, yayinda kuma karar horn d'insa kadai zaka ji ka fahinci cewa baya cikin hayyacinsa, da gudu gate man ya fito daga dakinsa ya k'araso, tare da zuwa jikin kofar gate d'in cikin sauri ya wangle masa gate d'in NABEEL kuwa da yakejin kansa asama da wani irin gudu ya shiga cikin tsakiyar compound d'in direct ko Gama de-de ta parking din nasa da kyau kuwa baiyiba ,ya bude murfin motar nasa ya fito, kallo daya zaka masa kasan cewa baya cikin hayyacinsa, maida murfin motar nasa yayi ya rufe,Cikin wani irin taku dake nuna zallah kwarjininsa ya nufi hanyar da zai Sada sa da babban parlour gidansa ahankali ya shige cikin tsakiyar parlour din sa,a Saman two-seater ya zauna hanuwansa biyu yasa ya Kama kansa dake wani irin ciwo, hakanan yake jin kunci da damuwa acikin ransa, lokcin ɗaya. yatambaye kansa, wai ma shin meyasa Ma'aikacin hotel din ya yaudaresa ta hanyar basa wine me alcohol acikin??? Shima bai saniba a
Ahankali ya dago idanuwansa da suka yi jajur ya saukesu akan hadadden Zane photon FAREEDAH wada ya manna ajikin bangon parloursu ,tashi tsaye yayi tare da karasawa wajen da zanen photo Nata yake like Ahankali ya daura hanuwansa akan picture tare da sakin smillig batare da ya yashirye ba"sugar baby
I love you ya furta ba adadi,Zanci gaba da sonki har bada,You are My Everything,My life,my soul mate,My...my....my....my....You are mine Dear I cant do without you My lovely wife....
TABBAS Ni NABEEL ina masifar tausaya wa kaina acikin halin damuwa da tashin hankalin da nike ciki Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawarka lafiya, lallai hakika Allah ka aiko min da babban jarabawa rayuwa Allah Kasa in cinye wannan jarabawa rayuwa lafiya Allah ya kawo min mafita cikin lamuran ka,,,
________*FAREEDAHH*______
_____*Bayan sati biyu*_______
BANGAREN GIDAN SU FAREEDAH kuwa
Gida ne mai d'auke da d'akuna uku sai kitchen dake daga bangaren dama sai kewaye dake daga can karshen gidan sai tsakar gida mai dan yalwa, gidan dai kallo daya zakamashi kasan na masu ɗan rufin asiri ne
azahar suna zaune atsakar gida cikin yar qaramar rumfarsu
Zaune mahaifin FAREEDAH da mahaifiyar ta suke a samar tabarma
Kallon mahaifiyar FAREEDAH mahaifin FAREEDAH yayi Kafin cikin kulawa ya buɗe baƙin sa yace "
Wai Rabi
"Na'am Malam Maman FAREEDAH ta amsa tana mai kallon mijin nata"cikin sanyin Muryar mahaifin FAREEDAH Yace" wai wace irin tafiya ne wannan NABEEL ɗin yayi wanda bazai bar FAREEDAH agidan ba sai ya turo ta nan Gidan ? "cikin sanyin Muryar da mamakin abun mahaifiyar FAREEDAH ta buɗe bakinta tace"nima haka nagani kuma ni kasan abunda ke bani mamaki ,FAREEDAH tunda tazo Gidan nan bata wani kazar-kazar shine nace ko dai akwai wani abun ne?
"hakane inji cewar Malam sannan ya cigaba da cewar" to amma kuma ai in baki manta ba yaran nan sun shaku da junarsu kuma suna zaman lafiya da junarsu "amma duk da Haka dai yakamata dai a sake tambayan ta ,inji cewar Mama"yanzu Ina take? "Tana cikin kitchen "kira min ita "cikin daga murya Rabi ta shiga kwalawa yarta FAREEDAH kira "FAREEDAH! FAREEDAHh!!"Na'am FAREEDAH ta amsa kiran da Mamanta tai mata "cikin kulawa Mama ta furta"kizo ana kiranki "
Cikin sauri FAREEDAH ta fito daga cikin kitchen kai tsaye inda suke zaune ta nufa cikin sauri ta ƙaraso gurin su a inda suke zaune tare da rusunawa kallon su tayi kafin cikin sanyin Muryar FAREEDAH ta buɗe bakinta tace"gani Baba "Cikin kulawa Malam ya buɗe baƙin sa yace"FAREEDAHh wai me ke faruwa ne bana son ki boye min komai ki gaya abunda yake faruwa? , Malam ya ƙarasa tambayarta yana mai dubanta "Baba abunda na fad'a maka dazun shine babu abunda ya yafaru,tana cikin magana kenan sai kawai kukan tsananin tashin hankali da damuwa ya subce mata ,..... cikin sheshekar kuka FAREEDAH ta cigaba da cewar "Baba babu abunda ya faru Tana gama magana ta Mike cikin kuka ta nufi hanyar d'akin ta Tare Da shigewa cikin d'akin ta"kallon Malam Mama tayi tare da faɗin
"ka gani ko Malam! in harda akwai wani bakon Abu gameda FAREEDAH ni Ina ganewa " sauke ajiyar zuciya Malam yayi Tare Da faɗin"hakane To kyale ta bari zanzo in kira ta mu keɓance dani da ita insha Allah zata gayamin koma menene ke faruwa"Allah yasa "AMIN YAH Rabbill IZZATI Wai Ina kanin nata ?"Abubakar? "eh "Ina ji yana dakinsa "to maza kirawomin shi yazo ya tayanin rubuta wannan rubutu a jikin allo ",OKAY To inji cewar Mama tana mai mike wa tsaye kana ta nufi
hanyar zaure gidan
Chapter 13 · 0% Book details