← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 29

Sashe 9

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama uwar gida ce ta fara ganinsu sun fito,ta kafe su da mayun idanuwanta wutar kishi na cin zuciyarta,yadda kasan ta shaƙesu haka take ji,tun ba yau ba idan ta kalli Zulaiha sai taga duk tafi dacewa da mijin na su,ita farar fata ce sol sol shi kuma baƙi ne cikakken bahaushe ita kuma cikakkiyar shuwa arab,wacce kallom farko zaka tabbatar da hakan saboda kyaun fuska da kuma na jiki,ga gashin nan yala yala tamkar ita ta dasa abinta cif cif gwanin ban sha'awa.
har suka iso gabanta bata sani ba,sai turaren Zulaiha ne ya sanar da ita sun iso gab da ita koma sun wuce,turaren na ta ba wai me masifar ƙamshi bane,a a turare ne irin na su na shuwa arab wanda ake turara kaya dashi,sai kuma taje gab da kai zakaji hakan ko kuma wanda ya santa dashi ne zai iya jiyowa.

da sauri Mama Uwar gida ta ce"a'a Alhaji ina zuwa kuma? ka manta fa yau masu kawo lefen Zahra za suzo".

bai tsaya da tafiyar da yake ba ya ce"eh inda zamuje yafi kawo lefen ne,Mamana ce babu lafiya za muje asibiti duba ta".
wani banzan kallo da harara ta bankawa Zulaiha,ita kuwa bata ma san tana yi ba don bata juyo ba,burinta kawai taje wajen ruhinta jinin jikinta wato Æ´arta.
bata samu damar ƙara yin magana ba saboda ya fita daga gidan baki ɗaya.
Mama Zaliha na jinta daga falonta tana mata ƴar dariya,tare da yiwa Rabiatu fatan samun lafiya don haifar Rabiatu ne kawai bata yi ba amman itace uwar ɗakinta,don komi da ita take shawara bata taɓa ɗaukarta amatsayin ƴar kishiya ba,abinda ta ɗauka shine ƴaƴan mijinta ƴaƴanta ne don ko ba komi aure ya bata su,ko tana so ko bata so kuma daɗa da dukiya ba a musu mugunta,bakasan wanda zaiji ƙanƙa ba.
daman ranar unguwa zata fita itama,bayan ta gama shirinta ta kalli Æ´ammatan É—akinta ta ce"to ni zan tafi gidab yaya Jummai,ku tabbatar kun gama girkin dare da wuri kuma sannan bana son ko nan da soro É—ayanku yaje".

Dukkansu suka amsa mata da to umma adawo lafiya.ta amsa musu ta fito tsakar gida har lokacin Mama Uwar gida na zaune tana hararar tsakar gida,ita kuwa murmushi tayi ta ce"to Yaya ni zan wuce gidan yaya jummai,saboda kinga daga gidan yayata ne za a kawo lefen nan gwara inje in zauna zuwa dare sai na dawo".

    aciki ciki ta amsa mata,ita kuwa tayi wucewarta ko ƙara waigenta bata yi ba,in banda ƙaddara me zai sa ɗan yayarta ya auri ƴarta ai sai dole,har azuciyarta bata san wannan auren don yaranta duk ba suda tarbiyya,mazan ne kawai masu ɗan sauƙin kai amman suma uwarsu kawai suka sani ko wani abin arziƙinne ya samu basa bi takan kowa sai abinda ta ɗora su akai.

tafiyar da zata kai ta unguwar malali,da nisa wacce ke kaduna su kuma suna a Rigasa ne,saboda haka sanda taje har ƴan kawo lefen sun fito da aƙwatuna guda 12 reras dasu gwanin ban sha'awa.bata ji baƙin ciki ko ɗaya ba sai ma murna da tayi don   a wannan lokacin ɗanka ya wuce siraɗin lefe ai ka ji daɗi.
tana shiga gidan ta samu yayarta a tafkeken falonta,da yake mijinta me kuÉ—i ne sosai itama kuma ta tara abin duniya babu laifi.
kana ganin fuskarta kasan tana cikin matsala sosai,ta ƙaraso kusa da yayarta ta ce"yaya Jummai lafiya kuwa? Na ganki kamar kina cikin matsala? A'i ni aganina kamata yayu kiyi murna ba wai ɓacin rai ba".
kallon ƙanwarta tayi ta ce"Zaliha wallahi sam bana son wannan auren,don anfi ƙarfina ne shiyasa nayi shiru amman wai har ni yaron nan zai dinga gaba dani don na ce kada ya auri wannan yarinyar? ni wallahi abin ma mamaki yake bani,yaron da da yake son wannan yarinyar kirkin aminiyar Rabiatu wato Salimat,amman lokaci ɗaya ya burkice wai shi sai wannan lukutar yarinyar me kama da samudawa? Allah ƴar uwa abinnan yana damuna,don kowacce uwa tana son ɗanta ko ƴarta ya samu abokin rayuwa nagari."
shiru tayi sannan ta ce"haka ne yaya,amman babu yadda zamuyi fa bamu isa mu sauya abinda Allah ya tsara ba,abinda zamuyi yanzu shi ne mu maida komi ba komi ba,mu fauwalawa Allah dukkanin lamuran mi miƙa masa komi sannan mu taya Sagir da Addu'ah Allah ya basu zaman lafiya".
yayar ta amsa da "amin Xaliha shiyasa akaf cikin ƙanne na nake jinki acikin zuciyata,don ke ɗin haske ce acikin al'umma baki ɗaya,kina da tsarkakkiyar zuciya kin san abinda ki ke yi,kuma aduk abinda za kiyi kina sanya shi ne cikin mizani bisa hukuncin ubangiji idan akabi shawararki sai aga komi ya tafi dai dai".
taguminta ta cire ta ce"wallahi yaya ni babban abinda ke damuna yanzu bai wuce matsalar da Adawiyya take ciki ba,kinga na farko shima mijin bata jin daɗinsa,sannan Faccalarta wacce itace uwa uba wajen haɗa dukkanin wani tashin hankali,sai kuma surukarta wadda ko don muna muƙwaftaka da juna ta dinga raga mata,amman wallahi idan kinji zagin da take aikowa da Zulaiha maman Adawiyya sai kinsha mamaki wallahi".

   Yaya jummai ta ce"ikom Allah,au haryanzu Ramatu bata san annabi ya faku ba? bata dena muzgunawa wannan yarinyar ba? to ta barta da ƙaddarar da tasa me ta mana? kuma naga duk akan wa ƙaddarar ta faɗa mata? idan ba akan Ahmad ba? amman sun bi sun tsani yarinya sun dame ta akan mi? ni wallahi ma ahalin yanzu babu wacce nake gani da lefi sai Zulaiha,banda sakarya ce ita ta yaya za a dinga musgunawa ƴarki ki zauna ki sanya ido? yo haƙuri hauka ne? yarinya duk ta fita a hayyacinta? duk sanda kika ganta a zabure take? dalili dami duk akan abinda ya sameta wanda ya zama ƙaddara ce za a dinga hillatar yarinya?".
Zaliha ta ce"me kike son Zulaiha ta ce ya ya? kin san fa halin Alhaji? ba zai taɓa yarda ba ko? Yanzu sai kiji ya ce mata ai za a ɓata musu amintakarsu ta tun suna ƙanana? kinga kuwa ai dole abi abin da addu'ah."
haka suka yi ta hirar su ita da yayarta,sai dare ta dawo gida don yau ita ce da megidan baki É—aya wato Alhaji Bawa.

*****
ina ganin Ammi na fashe da kuka na faÉ—a jikinta,sosai nake kukan tamkar bazan dena ba Ammi ma da ba tada dauriyar ganin hawaye na,ai sai ta fashe da kuka tana ce wa"luf luf luf Adawiyya,ana asif".
aduk sanda take lallashina abinda take faÉ—amin kenan,don da larabci muka fiya magana ni da ita.
Abbana yana tsaye yana kallonmu,sosai yake jin babu daɗi agame da abinda ke bibiyar rayuwar ƴarsa wacce yafi so aduniyarsa,bai san me yasa ba duk yawan tarin ƴaƴansa,baya jin kowa kamar yadda yake jin Adawiyya baya son ɓacin ranta ko kaɗan,yanzu ma haka dole ce yasa yake yin shiru,don da babansu Ahmad dashi aminan juna ne,don tun suna yara suke tare kuma da suka tashi aure ma rana ɗaya aka ɗaura musu,uwar gidajensu suma aminai ne wato mama uwar gida da kuma mahaifiyarsu Ahmad,kamar yadda matayen na su ke komi tare haka suma suke yi,babu me jin kansu baya son yanzu kuma aji kansu akan autayyar yaran na su.

sai da mukayi kuka me isarmu sannan Abbana ya ƙaraso ya ce"yi shiru mamana ki faɗamin abinda ke faruwa ko?".

ina ganinsa na ce"Abiey".
da sauri ya ƙaraso kusa dani,na sanya hannuwana acikin lallausan hannunsa ina kuka na ce"Abiey wai akan ƴar yaya Zubair ba tada lafiya na tafi bada jini,sannan shi kuma ya Ahmad yana barci na tafi shine dana je aka ɗibi jinin adaren na taho gida don gudun kada ya yi faɗa,to shine fa wannan ya bugeni a mota ya kawoni asibiti,to kafin inkira Ammi shi na fara kira,shi ne shi ne ya ce wai kada in dawo masa gidansa".

  sai na fashe da kuka me dukan zuciyar me sauraro.

Sosai kowannensu ya girgiza da al'amarin Ammi ta rungumeni tsam ajikinta ta ce",yi haƙuri goge hawayen ki wallahi ba zaki koma gidansa ba...........Soon➡️
SHARE FISABILILLAH🙏🏻

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

MRS GREEN CE✍🏽
[1/9, 08:44] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
        {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

             _BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
Ya ku Æ´an uwana mu yawaita addu'ar fita daga gida don neman kariya daga sharrin shaiÉ—anu.

Addu'ar fita daga gida.

"Bismillahi alaihi tawakkaltu alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billahi".

addu'ar shiga gida.

"Bismillahi walajna wa bismillahi karajna wa alallahi rabina tawakkalna".

➡️13 & 14

…………………Abbana ma kasa tsaida ƙwallarsa yayi sannan ya ƙaraso inda nake,ya dafa kafaɗata sannan ya ce"Mamana inason ki faɗamin gaskiya,kin tabbatar ya cs miki haka"?.
ɗaga kaina na yi ina kuka,Ammi ta ce"tunda nake da ƴata tun tana budurwa har zuwa yanzu bata taɓa yimin ƙarya ba,to me zai sa ta yiwa Ahmad ƙarya? ni ina ganin Baban yara mu tafi da ita gida,idan yaso daga baya a yi duk maganar da za'ayi ammab idan aka komar da ita gidansa kamar ba asan darajarta bane,yarinyar nan fa ita kaɗai na mallaka arayuwata,to sabida me za a dinga son arabani da ita? duj kawai cin dana ke sai an kai ni ƙarshe"?.
Chapter 9 · 0% Book details