← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 29

Sashe 19

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️27 & 28
........Alhaji Badamasi ya ce"wallahi Hajiya Khaltume ko kaÉ—an ba kida kirki, yanzu sai da kika sanya yaron nan ya saki wannan yarinyar? Saboda kin tsane ta? to wannan wacce irin tsana ce haka? kada ki manta fa kina da Æ´aÆ´a mata har guda biyu, É—aya agidan miji É—aya agabanki idan akayi musu haka za kiji daÉ—i?"...........

Da saurin gaske ta cafe tare da ce wa"a ah fa Alhaji, ka dena yiwa yarana fatan tsiya ta yaya ma za a haÉ—a yarana da waccan baragurbin yarinyar? ni Æ´aÆ´ana suna da tarbiyya, in sha Allahu babu abinda zai faru dasu sai alheri tunda alherin suka shirya kuwa".
GyaÉ—a kai ya yi cike da takaici sannan ya kalleta kallon yaro bai san wuta ba sai ya taka, sannan ya ce"to lokacin da hakan zai faru sai ki hana, sannan kuma gargaÉ—in da zanyi miki shi ne, ki tabbatar daga nan zuwa gobe yaron nan yaje gidan aminina don ya É—auki matarsa, idan ba haka ba wallahi kema hanyar naku gidan zaki yi, don ba zan zauna da baragurbi ba ina can ina wahala kan neman halak a kullum ke kuma abinda kika sani shi ne mugunta da son rai, to wallahi ba zai yiwu a agina gidana da haram ba, idan kunne yaji jiki ya tsira".

tunda ya fara maganar ta kafesa da fici ficin idanunta sannan ta kai bango asan sanin dalilin mijinta na wannan maganar? saboda haka ta fara magana cikin fushi.
"Alhaji kana cikin hankalinka kuwa? ni zaka saka akan waccan shegiyar yarinyar? mayya wacce tasha a nonon uwarta? shi ne tsabar mugunta akeson tazo tayi ta lashemu, kamar yadda uwarta ke lashe mutanen gidansu? to wallahi ba zata saɓuba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shekarata nawa da kai baka taɓa ce min ko da jeki zanzo ba, shekara 35 kenan da aurenmu amman shi ne yau akan wannan yarinyar kake min kuri da zaka sakeni saboda ita? to wallahi ga fili ga me doki saura sukuwa, ni kuma zanga ta inda Ahmad zai dawo da wannan mayyar yarinyar"...................

Cafka ya kaiwa bakinta, har sai da tayi ihu sannan ya saketa gefe ta faÉ—i tana kuka, ya nuna ta da manuniyarsa ya ce " inajin mantani kika yi ko? ko don bakya ganina da kayan soji shi ne duk maganar da tazo bakinki zaki dinga faÉ—amin? to wallahi yanzu da kuma baya duk É—aya ne awaje na, zan iya rufe É—akin nan inyi miki mugun duka sannan kuma in horaki irin horon sojin da yayi lefi, kuma dolenki kibi abinda nake so ko kina so ko bakya so".

yana faɗar hakan ya fice yana huci tamkar ƙububuwa, tana zaune zaman ƴan bori har ya ida ficewa baki ɗaya, wani kukan baƙin ciki ya turniƙe ta wato asirin da ta yiwa mijinta ya karye kenan? Ai da ko musu da ita bai isa yayi ba, amman yau gashi akan wata tsinanniyar yarinya yana zaginta da kuma ci mata mutunci.
a haukace ta tashi ta ɗakko wayarta, ta rasa wa ma zata kira? Sai ta danna lambar ƙanwarta Asabe.
kiran farko ta ɗaga tana mata kirari "kaga mata agidan tsohon soja mazan fama Allah dai ya ƴara miki lafiya da nisan ƙwana". ........
Tun kafin ta ƙarasa maganarta ta ce"ke! Asabe nifa ina cikin matsala ne, saboda haka bana son wani habaici ke ba matar sojan bace da zaki cikani da maganganu".

Asabe ta haɗiye dariyarta, domin tasan duk yadda akayi yau an ɓata da tsohon soja ne.

ta ce"yi haƙuri yaya, ba ni nakar zomon ba....."

tayi ƙwafa sannan ta ce"Asabe yau Alhaji ni ya kalla ya ce wai akan wannan mayyar yarinyar zai iya rabuwa dani? anya kuwa ba asiri suka yiwa Alhaji ba? to wallahi dama wajen da kika je ɗinnan nake son ki rakani, ayi abinda za a lalata rayuwarta kamar yadda ta lalata rayuwarmu".
Asabe ta ce" kinji ko yaya ? wallahi wannan yarinyar ba zata taɓa barinki ki zauna lafiya ba,yo ai daman Yaya tun tuni ke kika ƙi bada haɗin kai, amman yanzu tunda ke kika yi magana gobe da sassafe kizo mu tafi".
hajiya ta ce"Allah ya kaimu Asabe".
ta kashe wayar tana jin zuciyarta wasai, don ko babu komi yarinyar ta shigar mata hanci da ƙudundune, ta hanata gaba ta hanata baya.

*** *** ***
"Malam don Allah ina neman gafararka, abisa son zuciyar da ɗana Ahmad ya aikata akanku, na ɗaukar maka alƙawari in sha Allah komi zai zo ƙarshe daga yanzu zansan ta yadda zan ɓullowa shi Ahmad ɗin"....

tun kafin ya ƙarasa Malam ya tare shi da ce wa"haba Badamasi, wani kuma bada haƙuri? ai ni aganina duk mun riga da mun zama ɗaya, ko da babu wata alaƙa tsakanina da kai ai kai maƙocina ne, saboda haka ka daina ce wa komi kan wannan maganar, ita kuma mamana ya zama dole ta koma gidan Ahmad, tunda dai haryanzun da muke maganar nan ba ce wa yayi ya sake taba, saboda haka ka faɗa masa an jima yazo ya ɗauke ta su tafi".

da sauri ya ce"a ah haba aminina, ya yaya zakace haka? bayan duk Zubairu ya faɗamin cin kashin da yake mata? sai kuma ace ta koma tun yanzu? Ai kaga ba a nuna masa yayi laifi ba kenan? saboda haka yanzu inason a kiramun ita ta faɗamin duk abinda ke faruwa, shima yanzu zan kirasa duk ayi ta ta ƙare idan ma ya gaji da zama da itane sai ya sake ta, don bazan yarda da wulaƙanci ba".

Malam ya murmusa cike da taƙaicin abinda ke faruwa, yadda yake jin Adawiyya aransa abin babu abin ƙwatance aciki, yana son yarinyar ne sosai saboda kaf yaransa babu wacce tayi kama da mahaifiyarsa sai ita, kai hatta maganarsu ma iri ɗaya ce, yana roƙon ubangiji ya fidda ta acikin wannan matsalar.

da kansa ya shigo muna zaune a falon Ammi, tana kallon series É—in labarina a sabuwar tv É—in da Abba ya siyo musu, ni kuma ina cin abinci alokacin.yana shigowa na tashi da sauri ina gaidashi, ya amsa min cikin fara'a sannan ya ce"yauwa mamana, ni da babanki Alhaji Badamasi muna son ganinki a babban falo na".

sosai gabana ya yanke ya faɗi, ya fara bugawa da ƙarfi har sai dana sanya hannuna dai dau saitin zuciyata ina kiran sunan Allah. hankulan iyayena ya dawo kai na, Ammi ta girgiza kai cikin tausayawa ta ce" wai ni malam ana aure dole ne? yaron nan ya saki yarinyar nan mana? ko maƙiyana ba zanso ya auri miji irin Ahmad ba, amman tsakani da Allah an hana yarinya sakat, gaskiya ni dai ba zata koma gidansa ba, yaje can ya nemi wata yarinyara ɗaya tilo an sanya min ita agaba , kalli yadda ta zuƙe ta rame ta fita a hayyacinta duk da tana cikin rayuwar ƙuruciyarta ne, shekara 17 ko ashirin ma bata kai ba, a kyale ta haka mana ba sai ya kashemin ita ya bugo yace azo a ɗauke ta ba".
ta faɗi hakan tana furzar da huci, tausayinta ya kamani sosai don tunda nake da ita ban taɓa jinta tayi sa'insa da Mahaifina ba, sai yau da ta gaza ɓoye kunyarta akaina don ba ƙaramin kunyar ƴar fari take dani ba.

Malam ya kalle ta cikin ƙwantar da murya da damuwa ya ce"kiyi haƙuri Zulaiha, ki kuma sanyawa zuciyarki salama akan wannan batun, shi fa aure rai ne dashi sai kiga ke kina nan kina huci da tada jijiyar wuya, ita kuma yarinyar ta ce xata komawa mijinta, to kinga kinji kunya anan ko? saboda haka ina me baku haƙuri da ki cire bakinki cikin wannan maganar".

Da sauri ta ce" in bar maganar ko? tunda bata shafe ni ba ko me? ai wallahi idan kaga na cire bakina a maganar Æ´ata sai dai idan mutuwa na yi".
Malam ya fara harzuƙa, abinda bai taɓayi ba kula mace idan tana huci sai naga yana ta bala'i har yana maganar indai taƙi yarda na koma to ta shirya bar masa gidansa don ba zai zauna da marajin magana ba.

da sauri na tashi na shiga tsakaninsu, don har mutanen gidanmu sun fara jin komi, don tuni har mama uwar gida ta hallara awajen, tana wani mugun murmushi me cike da fassarori da dama.

na ce"don Allah kuyi haƙuri ku bar maganar nan, duk akai nane iyaye na ke faɗa? duk akan aure na ne kuka samu wannan gagarumar matsalar? don Allah ku yafemin iyaye na ku sasanta kanku, indai kiranka ne Abba zanje amman bana son ganinku cikin wani hali".
Na faÉ—i hakan ina me fashewa da tausayin kaina dana iyayena.
Malam ya fita cikin matsanancin fushi, har yana tuntuɓe Mama uwar gida ta gama shigowa ɗakinmu, ta ce"Zulaiha wai me ya ke faruwa ne? amman sai naji kamar magana kuke akan komawar ta gidan wannan banzan yaron Ahmad ko? to wallahi kada ki bari ƴarki ta koma masa, don ba dena halinsa zaiyi ba don naji ance ma abin gaba yake don har neman mata ya ke.........."

wata tsawa Ammi ta daka mata, har sai da na tsorata itama maman ta tsorata sosai.

"ke! Jamila, kar nake ganinki munafuka me fuska biyu, wato kinzo kima dariya kina murna nayi faɗa da Malam, to ai ni kinsan a tarihin rayuwata ban taɓa yi ba, ke kuwa wani irin rashin arziƙine bakya masa agidan nan, saboda haka kada ki ƙara sanyamin baki akan auren ƴata, kije kiji da matsalar taki yaran da suka yi miki ƙwantai a ɗaki".

Sosai mama tayi mamakin jin wannan furucin daga bakin Ammi, ta kama kukan munafurci tana ce wa"yanzu ni Zulaiha kika zaga agidan nan? don kina ganin yanzu kin dafa ƙasa da hannayenki? to wallah sai kinsan kin faɗamin magana".
Chapter 19 · 0% Book details