← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 29

Sashe 23

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ƙer ya buɗe ƙasaitaccen bakin na sa ya ce" eh ina ciki,ba kuma za ka iya yimin maganinta ba, saboda haka you have to be carefull, bana son surutu nuna min bathroom zanyi wanka".
shiru ya yi gamida tashi ya nuna masa sannan ya dawo ya zauna, yana mamakin abinda ke faruwa? sai dai ba shida ikon sanin meke faruwa ɗin, amman duk abinda zai sa kaga Yarima cikin damuwa ba abune ƙanƙani ba, don tun yana yaransa iyayensu ke yi mishi misali da yarima, yadda ko acikin yara ne babu me sanya sa kuka, sai dai ma kai ya sanya ka.

sosai ya saki ruwan ajikinsa, ruwa me xafi ya daÉ—e acikin wannan halin ya fara wanke ko ina na jikinsa tamkar mace, don sai yayi awa É—aya zuwa biyu a banÉ—aki, har sai da Shamaki ya fara tunanin buga ban É—akin ko lafiya? sai gashi ya motsa handle É—im banÉ—akin ya fito, sanye da tawul a jikinsa yana tsane kansa da wani.

yana fitowa ya hango kiran mardiyya, ƙanwarsa da kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga, shiru tayi ta kasa magana shima bai ce komi ba ya barta amman ya sanyata a handsfree, duk sanda ta tashi magana tayi idan kuma tayi shiru har kuɗinta ya ƙare a banza.
Shamaki dai bai daina kallonsa ba, don ashe abin nasa har ƙannensa bai bari ba? sai kuwa ya ce"Yarima mardiyya ke kiranka fa? ni aganina ka ɗaga kaji ko menene"?.

bai ce masa ƙala ba, sai ma lumshe idanuwansa da yayi, yana tuno wani mashahurin lamari, wanda aduk sanda ya rufe idonsa abinda yake gani kenan, indai ba ƙwayarsu ta soji yasha ba baya jin daɗin rayuwarsa.

can Mardiyya tayi ta maza ta ce"bro Allah ya taimakeki ya ƙara maka lafiya, daman wata magana ce nake son muyi da kai, abinda Ammi ta faɗamin ɗazu gaskiya ne? wai ka yiwa wata yarinya ciki har ta haihu? i can do that, nasan hakan ba zai taɓa faruwa ba, ɗan uwana ba shida wannan halin don Allah ka faɗamin ko zuciyata zata samu salama".

sosai gaban Shamaki ya buga, ya tsorata sosai daman abinda ya sanya yarima cikin damuwa kenan? gaskiya wannan ba ƙaramin mummunan lamari bane, kuma abin yana da ɗaure kai da kuma shiga ruɗu.

kamar babu wani abinda ke damunsa ya ce" eh haka ne, meye matsalarki akan hakan? saboda haka kisan da wanda kike magana, ni ba sa an wasanki bane".
Yana faÉ—ar hakan ya datse kiran wayar.

Shamaki ya kallesa da kuma ƙarfin halinsa, don shi koda ya aikata ba zai iya cewa shi bane, amman shi cikin dakiya har ya iya buɗe bakinsa yace shi ya aikata hakan, gaskiya ba kowa ne zai iya wannan sadaukarwar ba.

*** *** ***
....... Amrat ta ce"Hamida kinsan kuwa yadda nake masifar son yarima? kinsan daɗewar danayi da sonsa a zuciyata? amman shi bai ma san na damu dashi ba? kullum burinsa bai wuce ya ƙuntatamin ba? idan har da ace zan iya cire soyayyarsa arai na to da tuni na cire shi araina, amman bazan iya hakan ba ya xama dole in auresa idan ba haka ba mutuwa zanyi".

Hamida ta ce"come down besty, kiyi haƙuri mu zauna mu tattauna ta yadda ya kamata ace yarima ya kulaki har ya aure ki, ni aganina me zai hana muje wajen Dad muyi magana dashi, tunda Dad abokin me martaba ne wataƙila za a samu sauƙin lamarin, har ma ya aure ki ko yana so ko baya so".
Amrat ta juyo da sauri ta ce"yes yes shawara me kyau"..........soon➡️

FACCALA NOVELS FANS
https://chat.whatsapp.com/L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA

*NABIHA DATA SERVICE*
kuzo siyan data me rahusa da kuma auki.

MTN
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
3GB. 900
_____
GLO
500MB. 150
1GB. 300
2GB. 5,50
3GB. 850
_________
AIRTEL
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
5GB 1,200
__________
9MOBILE
500MB
500MB 150
1GB. 250
2GB. 450
3GB. 600

Via:-
5458227606
Nabiyyah Aminu
Moniepoint

my no
08103807998

*MRS GREEN CE*
[1/17, 12:31] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444

Whatsapp:https://wa.me/7068606171

*Ummu maher collection👛👠*
https://chat.whatsapp.com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️33 & 34
..........Amrat mawashi, ƴa ce ga Alhaji mawashi shi ɗan asalin jahar katsinane, shararran me kuɗine wanda yasan menene kasuwanci kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suke faɗa aji acikin Nigeria bama iya katsina ba, yana matuƙar son yin mu'amala da masu kuɗi sannan ya tsana talaka ko sunan talaka ma bai son ji, shiyasa ko taimakonsu ma bayayi kuma babu wanda ya ke cin kuɗinsa sama da matansa da ƴaƴansa, sai kuma waɗanda suke musu aiki a ɓoye, wanda babu wanda yasan irin ta'asar da ya ke sai shi kaɗai, sai kuma wani mutum wanda yasan komi nasa, sai dai ya yi shiru ne ba don tsoro ba kowani abu yayi ne saboda talala da yake shirin yi masa.

Amrat ita ce ƴa ɗaya tilo daya mallaka aduniya, itama sai da suka shafe wasu shekaru kamar shekara 15 sannan suka haifeta, shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗora mata duk abinda takeso shi take samu, shiyasa take taka duk wanda take so babu wanda ya isa ya taka mata burki, sannan babu ta inda ta baro mahaifinta awajen tsanar talaka, shiyasa ma kaf ƙawayenta babu talaka sai ƴaƴan masu kuɗi waɗanda iyayensu suka shahara aduniya ma ba iya nigeria ba.

Amrat ta fara sanin Aliyu ne a ƙasar America, inda taje party ɗin wani abokinta bature, alokacin shi kuma ya fito daga barrek ɗinsu na sojoji, yana training kan hanya ta tsaya har da ɗaukarsa hoto shi bai ma san tana yi ba, sai daga baya sannan yasan tana ɗaukarsa, ya ƙaraso inda take fuskarnan a matuƙar murtuke ya warce camerar ya nunata da ƴar manuniyarsa ya ce" na yi miki kama da mara aikin yi kamar ki? na yi miki kama da wanda yazo shan iska? wannan shi ne warning ɗin da zanyi miki kada ki ƙara zuwa wajen nan don ɗaukana hoto".

har ya gama maganarsa bata tanka masa ba, kallonsa kawai take ko kyafta ido babu don har ga Allah ya tafi da ita sosai don tunda take bata taɓa ganin mijin da ya ƙwanta mata irin Aliyu ba, tayi yawo sosai cikin ƙasashen da taje babu irin mazan da bata gani ba, amman sai yau Allah yayi ta haɗu dana mijin daya zamar mata gamda katar.

har ya wuce bata san ma ya wuce ba, sai da ta juyo taga babu shi babu alamarsa, sai ƙamshin turarensa perform me matuƙar tsayawa arai, tun daga ranar ta dinga bibiyarsa har Allah yasa ta gano komi nasa da ƙasarsa da asalinsa har ma da sunansa, ko da ta dawo nigeria sai hankalinta da tunaninta suka fara gushewa, saboda tunanin farin cikinta Abban sojoji malamin soyayyarta wato Aliyu, ko barci ta ƙwanta sai tayi mafarkinsa wai gata ga shi a wani babban falo tana maƙale a kusa dashi suna ta tsinkar fure, idan mahaifiyarta ta shigo tashinta sai kaga har kuka take saboda tsabar azabar da take ciki na son kasancewa da Aliyu.
Mahaifiyarta bata taɓa bata damar wulaƙanci agabanta ba, macece mai matuƙar taka tsantsan da addini sannan tana matuƙar taimakon talakawa, don har sadaka ma take yi duk ranar jumma'ah sannan bata tsaya iya nan ba har gidan marayu tana zuwa ta basu taimako sosai, tun Amrah bata son zuwa har ta koya, domin Hajiya Rabi na tsaye akanta sosai saboda haka duk ƙarshen wata tana janta suje gdan marayu su kai musu goma ta arziƙi, da yawan mutane sun ɗauka Alhaji Kabir mawashi shi ne me wannan taimakon, shiyasa zakaga duk inda ya shiga ana matuƙar girmamasa da ɗaukar komi nasa amatsayar girma da kuma mutuntawa, mutane sun ɗaukesa tamkar wani waliyyi saboda yadda ake ganin matarsa na taimako sosai, don ayanzu haka ma tana da gifan marayu da kuma gajiyayyu na ta nakan ta, itace shugaban ƙungiyar OPHANAGE FOUNDATION GROUP, bama a iya nan ta tsaya ba tana ɗaya daga cikin mata masu matuƙar gyara fannin aure, don duk ranar laraba ana zuwa har gida wajenta don tana da ofishin da ta gina acikin gidanta, na taimakawa mata da kuma matasa zawarawa, da ƴammata har ma da gauraye, kuma tana haɗa aure sosai ƴammata da zawarawa duk tana haɗawa ta bawa miji jari ta bawa matar ma, Hajiya Rabi giwar mata hasken matan arewa, kinga jiya kinga yau zakin mata gagara badau, wannan itace waƙar da alan waƙa yayi mata, da sauran mawaƙan gargajiya da kuma na zamani.

Amrah mawashi irin yaran nanne marasa jin magana sosai, don duk irin ƙoƙarin da Hj Rabi take yi a banza, don duk abinda zata ɗorasa akai mahaifinta zai canja mata layi, idan ma bata yi wasa ba sai kiga abin ya dawo kanta don aƙwai lokacin da Amrah ta fita partyn dare bata dawo ba sai washe gari, ko da ta dawo a buge ta dawo tayi shaye shaye har ta gaji, ranar haɗiyar zuciya ne kawai bata yi ba don ji tayi awannan karon zata iya fito na fito da mawashi, don ko sakinta zai yi sai dai ya saketa amman ita baxa ta yarda rayuwar ƴarta ta salwance ba, aranar ta yiwa Amrah mugun dukan daya sanya ta farfaɗowa daga wannan mayen da take ciki, sannan ta kulle ta a ɗaki ta gargaɗi me aikinta akan kada ta sake ta buɗe mata zataje wajen aiki ne, da yake ƙwararriyar likitan mata ce wacce tasan abinda take, likita me lasisi a jihar katsina har ma da sauran jahohi a ƙasar tamu ta nigeria.

tana fita Alhaji mawashi ya shigo, ko da ya shigo yaga ba kowa sai ya tambayi me aikinsa ina Lulu?, bakinta yana rawa ta shaida masa komi.
Chapter 23 · 0% Book details