Sashe 7
Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 6 min read
  ta ce"Momma nasan kin gane fa? mamaki ne ya hanaki gasgata hakan,ko kuma so kike sai Bro yazo ya fuskantad dake komi,bakya buƙatar wannan a tsakaninku abinda yafi shine ki sanya masa ido sosai,sannan kuma idan da hali ki tayasa da addu'ah sosai don wallahi ɗan ƙwali yana shirin jawo hula idan ba a ɗauki mataki da wuri ba".
Momma ta zauna tana ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka ƙwaronyo mata,ta share hawayen na ta tana ce wa"ya Allah ga bawanka nan,wanda bai san komi ba sai kyautatawa iyayensa da kuma na sama dashi,ga taimakon marayuwa da jin ƙan talakawa,ya Allah ka kyautata masa kamar yadda ya ke taimaka mana,ya Allah ka kare min shi ka kare gabansa da bayansa ".
Murmushi auta tayi sannan ta ce"oh Momma irin waÉ—annan addu'o'i haka? sai kace shi kaÉ—ai ne É—anki? gaskiya Momma duk kin fi son waccen cikulallen mutumin me zubin samudawa".
wani duka Momma ta kai mata ta ce"eh nafi son shi É—in,kuma ai ko wani irjn zubi ne dashi a'i ya fiki kyau da komi".
dariya tayi ta ce"ato momma kin taɓa ganin inda namiji yafi mace kyau? a'i kinsan ma ba zai taɓa yiyuwa ba,kuma ma ai naga dake nake kama"?.
murmusawa kawai tayi ba tare da ta ƙara cewa komi ba,Auta ta tashi ta wuce ɗakinta don tasan wannan shirun da tayi ba ƙara magana za tayi ba,don wani miskilancin ma ita bro ɗinta ya gado ba wani ba.
  tana shiga ɗakinta ta cire dress ɗinta za ta shiga wanka,sai taga kiran wata ƙawarta wacce suke cewa Chuchu,tayi kamar kar ta ɗaga sai kuma ta daure ta ɗaga ɗin don tasan ta da shegwn surutu yanzu haka gulma zata kawo mata,ita kuma babu abinda ta tsana irin a kawo mata gulmar wani,kai baki ɗaya ma ta tsani me ɗabi'ar gulma don magulmaci wutarsa daban take.
 A'i kuwa tana ɗagawa ta ce"gimbiya wani labari nazo miki dashi da ɗumi ɗuminsa".
da sauri ta ce"kinga Chuchu ina da abin yi fa? bath zan shiga kika kirawo ni".
da sauri don kada ta katse ta ta ce"gimbiya don Allah ki saurare ni,wallahi wannan labarin da zan baki yana da kyau ki tsaya kiji saboda bana son daga baya Allah ya tambaye ni,wallahi akan bro É—inki ne ashe ya dawo ma ni ban sani ba,É—azu naje wajen birthday paty na abokina shine na gansa a club,nayi mamakin ganinsa wallahi don naga shi baya irin wannan rayuwar,duk dama mutum yana canjawa infact ma shi daya dawo daga turai kinga ai ba abin mamaki............."
"dalla malama tsaya,bana son sakalci da rashin sanin abinda zaki dinga faÉ—a mana,ta yaya zakice wai kinga bro É—ina a club? aka gaya miki shima irinki ne me yawon bin abokai da sakalci"?.
acan ɓangaren ta ce"ok baki yarda ba kenan? ai daman nasan ba zaki yarda ba,amman na faɗa miki ne don kusan matakin da zaku ɗauka,saboda wallahi ayanayin dana gansa ya ban tausayi sosai bayan buguwar da yayi da wata yarinya na gansa fa?".
  Sosai gabanta ya faɗi ta riƙe ƙirjinta dake wani irin luguden kai kawo ta fara magana bakinta yana karkarwa "Chuchu ta yaya kike tsammanin zan yarda,ta yaya xakice yayana fasiƙi ne? me shan giya me saɓawa mahakiccinsa? no no no wallahi ƙarya kike Chuchu".
chuchu tayi wani murmushin takaici ta ce"eh ni nasan ina da gulma amman fa duk gulmar da zanyi bana faÉ—ar abu idan har ba dai dai bane,ina faÉ—arsa yadda ya faru saboda haka ki buÉ—e whatsapp É—inku in turo miki hotonsa sai ki yarda".
 hannunta na rawa ta buɗe whatsapp ɗin,gabanta na faɗuwa hannayenta suna salƙewa tamkar suna taɓa wuƙa.
 Mummunan gamon da tayi ya sanya ta kusan sandarewa awajen,ta shuɗe na wucin gadi awajen tana shesheƙar kuka ta ce afili"haba bro,me ka nema ka rasa aduniyar nan? idan auren ka keso ba sai ka faɗa ayi maka ba? amman wannan wacce irin rayuwa kake so ka jefa kanka? ka kuma jefa mu? innalillahi wa inna ilaihi raji'un,la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin,wallahi sai na kawo ƙarshen wannan al'amarin a satin nan zansa aɗaura maka aure kowa ya huta".
  ajje wayar tayi ta shiga banɗaki,tasha kukanta sosai kana ganin idonta kasan tasha kuka har ta godewa Allah ta sanya doguwar rigar abaya me ɗan sauƙin nauyi,ta yana veils ɗin kayan ko mai bata shafa ba ta sanya takalminta halp shoes wanda irin na ƴan gidan sarauta,don duk mafi yawancin takalmanta irinsu ne don arayuwarta tana masifar son irin kayan sarauta.
xama tayi afalonta,tana tunanin wanda zata haÉ—a baki dashi a yiwa bro É—inta aure ko a huta.
Can ta tashi da sauri ta ce"yes!.gun gwagwala zanje".
sashen kakar tasu ta nufa,tana cike da nishaɗi don tasan halin gwaggwala da son ayi maganar aure,caraf zata karɓe tace a haɗaku da wance da wane.
tuno wata shawarar yasa ta wuce part ɗinsu Amira ƙanwar ya Aamiru.
tana zuwa ta samu mamansu a babban falo,bayinta na gefen ta suna mata tausa ta gaisheta cikin fara'a ta ce"oh Auta me mukayi ƙwana biyu ba a shigo mana"?.
auta da baby ɓoye ɓoye ta ce"faɗa mukayi da Amira".
murmushi tayi ta ce"yo ai kun saba dama in dai kune,me shiga tsakaninku ai sai yaji kunya".
ta faɗi hakan tana murmushi,ni kuma na shige ɓangaren Amira wacce ba don tana son haɗa baki da ita ba,da babu abinda zai kawo ta saboda sunyi faɗa.
  Amira ƴa ce ga ƙanin mr martaba,tun suna yara tare muka taso har makaranta duk tare sukayi,idan sukayi faɗa sai ka ɗauka ba zasu tama shiryawa ba,sai kuma daga bisani kaga sun shirya ɗin.
tun daga nesa ta hango Amira tana gaban mudubi tana cancaɗa ado,cikin riga da siket na wani cancaɗeɗen leshi,wanda ya amsa sunansa kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba kasan anyi ɓarin dukiya awajen.
 tana ganinta tayi saurin ce wa"ƴar halak,wallahi dama kina raina yanzu zanje sashenku muyi wata magana".
Autar momma ta ce"ok nima magana nazo muyi".
on serious Amira ta juyo har da zama a bakin tamfatsetsen gadonta ta ce"ina jin ki aminiya".
Autar Momma ta ce"naƙi ɗin ke ki fara faɗamin maganar sannan nima in faɗa miki".
amira ta riƙo hannuwan Autar Momma ta damƙa acikin tsakiyar hannunta ta ce"don Allah hafsy ki taimakamin,wallahi wani abu ne yake damuna amman na rasa wanda zan faɗawa,ina kuma jin kunyar su Anti khalisat ba zan iya faɗa musu ba,ke aminiyata ce Hafsa ban saba da faɗawa kowa sirri na ba sai ke,shiyasa nake yanzu ma in faɗa miki wani babban sirrin zuciyata wanda na daɗe da binnesa sai dai ba zan iya binnewa ni kaɗai ba,dole ne in samu wanda zamu to no tare".
kallon ƙasa tayi mata sannan ta ce"kinga ni fa na gaji da wannan maganganun, ni ki faɗamun meye ke going? sai musan ta inda zamu ɓullowa abin".
a hankali ta tashi tsaye ta juya mata baya sannan ta ce"GALADIMAÂ na ke so"...............
da mugun sauri a É—ago tana kallon aminiyar ta.................
***Â Â Â Â Â Â Â ***Â Â Â Â Â Â Â ***
......bakina yana rawa na ce"a ,a,a, me kake nufi Ahmad? don Allah ka dinga yimin kyakkyawan zato mana? me zai shiga tsakanina da yayanka?".
sautin muryarsa taji yana ce wa"dalla malama rufemin baki,yau kika saba shagala? yau ne abin ya fara faruwa ko kuwa an daɗe ana yi? ki faɗamin gaskiya ko kuma wallahi in tona kundin sirrin da kika rufe agajimare yana yawo asama ba tare da kowa  yasan abinda ya faru ba".