← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 29

Sashe 16

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

ranar daya san tana da ciki ya yi nadamar fara zuwa wajenta sosai,ya rasa wanda zaiyi shawarar dashi,ranar muna falon Abiey sai ga yaya Zubair ya shigo,muka gaisa mu dukanmu amman da yake lokacin muna É—aukar karatu ne awajen Abiey É—inmu,ni da Baby sai kuma Rabia,Æ´ar gidan maka uwa gida don kaf cikin Æ´aÆ´anta ita kaÉ—ai ce muke É—inya sosai,ma ana munfi shiri da ita don ita ce tayo zyciyar Abiey a yaranta.

ina kallon Baby tana kallonsa tana hawaye,don har ga Allah tana sonsa sosai kuma shima yana sonta don dai anyi musu fin ƙarfine kawai.
bayan mun gama karatun ya gaida sauran matan Abiey sannan ya shigo ɗakin Ammi,alokacin tana kan injin saƙarta tana yi,ya samu waje ya zauna ni kuma na kawo masa zoɓo rodon da Ammi ke siyarwa don rufawa kai asiri,na haɗa masa har da fankasau ɗin da tayi.
ya yimin godiya,ina shiga ɗaki naji yana faɗa mata abinda ya sanyani firgita sosai,na sakko daga kan gadon Ammi gabana yana faɗuwa sosai,duk da ba nida wayo amman ai muna karanta komi a makaranta sannan tun ina shekara goma na fara haila,saboda haka Ammina ta sanar min da komi,na in kula da maxa kada na zama me wasa dana miji ko da kuwa wanda zan aura ne,hakan yasa na zama me taka tsantsan da kuma kula da kai,amman duk da haka ya Ahmad na ƙoƙarin taɓa jikina ni ce dai me kiyayewa ammanshi awajensa sai naga kamar wata wayewa ce.

sosai na tausayawa ya Zubair,Ammi ma ta tayasa jajan abin sosai ina juyota tana ce wa"sai haƙuri ɗana,nasan abin da zafi kuma da muni kuma ka cigaba da yiwa mahaifiyarka biyayya,in sha Allah zaka zama me nasara arayuwa,sannan kafin ka aureta ka ɗauketa kuje ayi muku gwaji,don gudun faɗawa cikin matsala hakan kuma zai zamar maka kariya don ita guguwa idan ta taso babu me iya kareta sai Allah,hannu ko waji mahuci ba zai taɓa yi maka garkuwa ba,sai dai ka nemi zaɓin Allah sannan ka dage da nafilfilu da kuma roƙon Allah shima wata madogara ce".

murmushi yake me haɗe da ƴar dariya,duk da ba wai zuciyarsa tayi 100%100 ba amman kuma yana jin kaso hamsin ya tafi,don tun da ya fara neman shawarar Ammi bata taɓa jefasa acikin matsala ba,sai dai ta fito dash dumu dumu aciki.

*** *** ***

Fulani ta kallesa cike da takaici,hawaye wasu na bin wasu ta nunasa da ƴatsanta ta ce"haƙiƙa Haidar da haihuwarka gwara ɓarinka,tabbas sa nasan zaka shigo cikin duniya ne don ka ruguzawa al'umma tarihi da kuma jin daɗi da na hanaka zuwa,sai dai ba nida wani ikon yin hakan baka taɓa faɗamin abinda ya zama na ƙarya ba,amman a wannan karon ka yimin ƙarya mafi muni arayuwa,bana son inyi maka mummunan fata,amman inason ka gaggauta barin garin nan don wallahi idan ina kallonka zan iya tsine maka kabi duniya".

sosai yake kallon mahaifiyarsa cikin mamaki,don gani yake tamkar de ba ita bace canja masa ita akayi,sai dai ganin Aamiru da yayi awajen ya tabbatar masa da cewa tabbas Aamiru ya sanar da mahaifiyarsa komi,takaici da kuma nadamar ɗaukar Aamiru amatsayin abokin sirri shiya ƙara haɓaka adadin ɓacin ransa,ya tako cikin takunsa me matuƙar sare zuciyar ƴammata,ya riƙe hannayenta duka biyu ya kalli cikin ƙwayar idonta waɗanda suka cika da hawaye sannan ya ce"Nisful hayat,me kuma nayi? waɗannan wasu zantuka ne suke fitowa ta bakinki me albarka? menene ya zafafa zuciyar da take cikin sanyi da sanyayawa? ki faɗamin Nisful .............."

A'i bai ƙarasa faɗar abinda zai faɗa ba,ta turesa gefe har sai daya kusa haɗuwa da tibin bangon da ta kusa cika tamkeken falon,Aamiru ya taho da sauri zai taimaka masa,ai kuwa shima da sauri ya cakumo sa ya shaƙesa sosai,asalin kalar Galadima ta fito ya ce"Aamiru ayau ne nasan dawa nake xaune? ayau ne nasan kai munafuki ne wanda ba a sirri dashi,lallai ka cika maha'inci kuma mayaudari,amman abinda nake son ka sani ni nawa sirrin daka bayyana cike take da securities da kuma ikon Allah,kai kuma naka sirrim a hannuna yake ko yanzu nayi niyya zan tona maka asiri za kuma kayi dana sanin wannan abin da kayi min".

yana faÉ—ar hakan ya fice fu,don yasan halin mahaifiyarsa indai tayi fushi alokacin babu me rarrashinta sai me martaba,zai je ya tonawa kansa asiri awajen mahaifinsa,ya kuma buÉ—e masa cikinsa wanda dama acan baya damar hakan yarasa ko Allah zai sa ya samu me jin tausayinsa.

yana fita Aamiru ya rasa yadda ze yi,don kamar yadda Galadima ya faÉ—a nasa sirrin yana tafin hannunsa wanda kuma ya tabbatar da nasa yafi na galadiman,amman ya ze yi da rayuwarsa? wani mataki zai É—auka don kada hakan ya tabbata? idan kuwa ya tona masa asiri ya gama dashi.

*** *** ***

uwar gidan sarki,ta miƙe tsaye asanda take kallon wani bidiyo awayarta,ta tuntsire da dariyar cikakkiyar ƙeta tana ce wa"good! tabbas yanzu ne na samu wani makami da zan fito yaƙi dashi,ba tare dana ji wani ɗarr ko tunanin komi ba kyauta, inason ki ɓoye wannan bidiyon kamar yadda zan ɓoyesa,nayi hakanne don ki zamar min shaida don kuwa me martaba baya komi sai da shaida".

wacce aka kira da kyauta,ta É—an murmusa gami da tsugunnawa ta ce"an gama ranki shi daÉ—e duk yadda kika ce haka za ayi,kuma ina yi miki albishir da zan dinga bankaÉ—o miki wasu sirrikan da suka fi waÉ—annan,ke de kawai ki zama me bani goyon baya É—ari bisa É—ari".

Murmushin gefen baki tayi,irin na cikakkun sarakai sannan ta ce"kyauta,kina yi mana gandarki ne akan bama baki goyon baya? nada ma da kika saba bincikomin basu yimin bane sai yanzu ne kika ganomin wanda nake so".

ta É—akko bandir É—in kuÉ—i masu yawan gaske,ta sanya mata akan mayafinta sannan tayi mata nuni da hannu alamar ta fita,babu musu kuwa ta amsa ta fice da sauri har tana haÉ—awa da É—an gudu don yau bokanyarta zata samu kyakkyawan labari.

tana fita ta kyalkyale da dariya tana ce wa"Fulani ke da ɗanki kun shigo hannuna,sai na tarwatsa muku dariya kun zamo tamkar baku wanzu ba a doron duniya,sai na shayar dake baƙin cikin da kika shayar dani ni da ƴaƴa na"...........soon➡️

07068606171
ga masu son joining ɗin grp faccala,zasu iya bin wannan link ɗin na ƙasa bana son maza a grp sannan bana son ƴan masu turo ba tsa.

https://chat.whatsapp.com/L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA

*MRS GREEN CE✅*
[1/9, 13:21] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*_Wattpad profile✅_*
Rabiatu333
*_𝘼rewabooks profile✅_*
Rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
yawaita azumin lafiya, yana karemu daga barin aikata ɓarna.

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️23& 24
…………………dariya Fulani take sosai,har sai da ta zauna daram akan lallausan kafet ɗin dake shimfiɗe ababban falon, sai taga wannan dariya da murnar ba zata yi ta ita kaɗai ba,har sai da ta danna ƙerarriyar wayarta ta dannawa faccalarsu kira,don duk wani tuggu da ita ake haɗawa.

kiran farko ta ɗaga tana mata kirari,katseta tayi da ce wa"ke nifa bana son wannan kirarin, don haryanzu bai yi dai dai da kirarin da nake so a dinga yimini ba,uwar gida awajen sarkin Babbar masarauta,uwar yarima me jiran gado to wannan kirarin shi nake so ki dinga yimin, ba wani uwar gida sarautar mata ba a ina na zama sarautar matan? bayan waɗanda basu kaini matsayi ko sarauta ba,har ana iƙirarin sune gida tunda sun haifi yarima?.dama albishir na bugo inyi miki wannan buɗaɗɗiyar wasiƙar dana daɗe inason ta warware kowa ya santa yay dai ta fashe,don kuwa ashe Yarima wata ya yiwa ciki ta haihu ƙarshe ya kai yaron gidan marayu,kai abin fa babu daɗi awajen fulani, amman ni awaje na tamkar hasken farin wata musamman tauraro me suna Zahra".
da sauri Fulanin soro ta miƙe tana kyakkyaɓa dariya,tamkar tsohuwar da ta daɗe batayi dariya ba ta ce"hhhhh wato daɗina da gobe saurin zuwa,yanzu kinga sai muyi abinda muka ga dama babu wani ɗan iskan da zai sanya mana baƙin kyalle,tunda shima abin kunyar a gabansa ya ƙare,kuma ina me tabbatar miki zuciyar Fulani yau bindiga xa tayi kowa ya huta,shegiyar da ta saka akayimin kishiya? saboda tsanar da take mini? ita ba uwa ta ba,ba komi na ba sunanta Faccala tauraruwa me wutsiya,ai dole ne innuna mata zaren ba kalar yadin bane".

Dariya Fulani mazugal tayi sannan ta ce"uhm ai duk ba ma wannan ba,yadda mutanen gari zasu ɗauki al'amarin shine abinda ke ƙara sanya zuciyata cikin farin ciki da kuma walwala,yau kam sai nayi kyautar dawakai ɗari biyar,tare da haɗa kyakkyawar kilisa acikin babbar masarauta".HHHHH ta kyalkyale da dariya tana ajje awayar,ta ce"Fulani rayuwarki tana tafin hannuna".

*** *** ***
yaya zubair ya yarda da shawarar Ammi ɗari bisa ɗari,bai sanar da hajiya komi ba ya tafi gidansu Balaraba,abin takaicin bai wuce ganinta da wani ƙaton alhaji ba yana ƙofar gidansu suna bakin mota,itan kuwa kamar zata shige jikinsa tsabar takan sanin barikanci, ita ko tunanin wani ya gansu ma bata yi,abinda ta sani kawai ita bata shayin kowa ya ganta dana miji,takaicinsa bai wuce auren wannan gantafalalliyar matar ba wacce ta gama bawa maza jikinta tayi ƙwantai tayi saura.sannan ne shi za a ɗauko masa ita ace ya aura? banda uwa uwa ce wa ya isa ya kawo masa wannan juyayyiyar shawarar,wacce da ita da babu duk ɗaya? shi kaɗai ya ke ta bayanansa har ya ƙaraso wajen da suke,bata gansa da farko ba har sai daya ƙaraso sosai.yana hango tsoro fal a fuskarta don shi bai ma ɗauka tana da wani abu tsoro ba,amman bai san me yasa take tsoronsa haka ba tuni jikinta ya yi sanyi,ta kalli alhajin ta ce"kaga nayi baƙo ka dawo gobe ko"?.
gyaÉ—a kai ya yi sannan ya ce"ok an jima dai kinsan ina da time dake,saboda haka a guest house É—ina zaki sameni".
yana faÉ—ar hakan yabar wajen.
Chapter 16 · 0% Book details