← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 29

Sashe 22

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

MTN
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
3GB. 900
_____
GLO
500MB. 150
1GB. 300
2GB. 5,50
3GB. 850
_________
AIRTEL
500MB 150
1GB. 300
2GB. 600
5GB 1,200
__________
9MOBILE
500MB
500MB 150
1GB. 250
2GB. 450
3GB. 600

Via:-
5458227606
Nabiyyah Aminu
Moniepoint

my no
08103807998

*MRS GREEN CE*
[1/15, 17:30] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_AREWA WRITER'S ASSOCIATION✍️_*

*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444

Whatsapp:https://wa.me/7068606171

*Ummu maher collection👛👠*
https://chat.whatsapp.com/EBmNeSHdAl9EgqmlWo3Z3C

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️31 & 32
.........fashewa na yi da wani irin kuka me mugun cin rai, na tsugunna a ƙasa na dafa ƙafar Ammi na ce" Ammi don Allah ki daure ki yafemin, wallahi fushinki tamkar ƙara tafasar wutar da take tafarfasamin rayuwata ne, duk abinda nayi ba don komi na yi ba Ammi saboda ke da kuma Abiey, tunda nake arayuwata ban taɓa ganin kun samu saɓani me girma har haka ba, duk akaina ne komi ya faru bana son wata ɓaraka ta shigo tsakaninki dashi duk ta sabadiyya ta, don Allah ki yafemin sannan inason ki dage da yimin addu'ah saboda rayuwar aure na ta gyaru kamar kowacce mace da take zaman farin ciki da walwala agidanta". na faɗi hakan ina me fashewa da kukan tausayin kai na.

sosai na hango tausayina ƙarara akan fuskar Ammi na, ta riƙo hannuwana na tashi zaune ta ce"Adawiyya ba tsanarki nayi ba, Ahmad ne ahalin yanzu bana so ko jin sunansa, musamman ma a bakin ki sannan kuma ayau nr na yarda da son da kikewa Ahmad, saboda haka na baki goyon baya ɗari bisa ɗari ki koma gidansa, amman zan nemi alfarmar akan ya barki har sai zuwa jibi ma, don aƙwai abubuwan da na ke son kiyi kafin ki koma, sannan shima da kanshi aƙwai abubuwan da zan sanya Malam ya bashi, don na lura abin naku aƙwai lauje cikin naɗi".
Ɗan murmushi nayi wanda ya sanya wushiryata fitowa fara tas tas tamkar madarar ruwa, dimples ɗina suka samu damar lotsawa gwanin ban sha'awa, na ce"na gode Ammi Allah ya barki da Abiey". ta murmusa tana ranƙwashina na ƙwanata kan cinyarta, tana kallon kitson zara zaran kalba akaina, wanda ya ɗan jima kusan wata ɗaya akaina, ta ce"Amman yaushe kika zama ƙazama kuma?".

Cike da shagwaɓa na ce"Ammi to wanda zanyi kitson ya gani be damu dani ba, ko nayi ma bai san nayu ba abinda ya sani yayi ta kallon mata awayarsa ba tare dani ya sanyani agaba ya kalla ba".
"wannan dai duk ba hujja bace, ta yaya za'ace mace me aure ta zauna da kitso, kitson ma na kalba akanta har tsawon wata ɗaya? haba Adawiyya, bafa haka na koya miki ba ni ɗinnan da kike ganina sati bibbiyu nake kitso na, sannan kuma aduk sati biyun nan ina wankeshi kafin inyi sabo, adawiyya ƙazanta tana sanya namiji yaji ka fice aransa, duk kuwa da tsananin son da ya ke miki, balle yazo inda kike ya jiyo kina wari ko ƙarni ko hamami, kinga gobe ba zaki ƙara ganinsa kusa dake ba, sannan sai abu na biyu ki zama me yawan ɗauke kai aduk abinda mijinki zai miki, sai kiga kin zauna dashi lafiya duk da aƙwai abinda ba'a ɗauke kai akansa a aure shi ne idan namiji yayi dare, dole ne ka tambayeshi ko lafiya? shima ba ta hanyar rashim kunya ko fitsara ba, ta hanyar lallami da lumana idan da hali ma sai kin haɗa masa ruwan wanka ya yi bayan hakan ma kin bashi abinci yaci, aƙwai matan da babu ruwansu da yadda mijinsu ya dawo, abinda suka sani shi ne kawai a basu sai faɗa sai masifa, kuma waɗannan matan ba fa basa son mazajen na su bane, suna sonsu sosai amman kuma basu san yadda zasu zauna dasu bane, Adawiyya idan nace miki ke kika bawa mijinki ƙofar neman mata banyi ƙarya ba, don kuwa ke kike hanashi kanki, don har gidan nan ya kawo min ƙararki, wai akan facalar ki na cewa ke mayyar miji ce, to ke kuma kina tsoronta sai kika fara ƙaurace masa a shimfiɗarsa, haka nayi ta fama dake akan ki dena amman daga baya sai kika ɗauki hakan a banza, daga baya kuma yazo ya dame ki ko ayanzu abinda yasa na dake sai ya rabu dake saboda tsoron kada ya sanya miki wani ciwon, tunda ke kin kasa dena abinda kike masa na hana mishi kanki, nasihar da zan miki itace tunda har kinji kin gani zaki koma kina son mijinki, to ki dage ki kula da miji salo salo ki ƙara tabbatar da abinda ya keso da kuma wanda baya so, sannan duk yadda za kiyi ki hanashi yawon dare, don duk macen da mijinta ke dawowa gida da wuri to tabbas ba tada rabin matsalar aure, don a wannan yawon ne zai je ya ɗakko miki wacce zata sanya ki acikin mummunar matsalar da zaki kasa fita, ƙarshe mijin ya yanka miki red card ita kuma ta zauna agidan da kika kafa ɗan ƙaramin tarihinki aciki, don duk macen da ta bari ta fita gidan mijinta wata ta shigo to tabbas wannan kishiyar zata shafe babin tarihinki agidan sai na ta, duk irin tashen da kika yi saboda haka ki kula sosai sannan an jima zanyi magana da Mlm, aƙwai abinda za'ayi da kuma addu'o'i da kuma saukar alƙur'ani me girma".

sosai naji daÉ—in abinda Ammi ta faÉ—a, ko daman abinda ya hanata yin komi wai don ni Æ´ar fari ce, har mamaki Ammi nake da take kunyar Æ´ar fari dani don ni dai Allah ya sani bana jin kunyar Æ´ar fari da ita.

tana tsefemin kai Malam da ya Ahmad suka shigo, na tashi da sauri ina gaida ya Ahmad ɗin amman fuskata ahaɗe take, sai kallona yake yana ƙara kalleni tsaf, sai naga yana wani mayen murmushi ya ce azuciyarsa, wai me yasa ma nake kula matan banza ne? alhali matata babu abinda bata haɗa ba, ƴar shekara 17 yarinya ɗanya sharaf ga komi na cikar halitta amman na tsaya a matan banza?. shi kaɗai yake saƙa komi aransa , amman ni ina fuskantar duk abinda ya ke ce wa, na tashi da sauri zuwa ƙuryar ɗaki.

Ammi ta ce" Ahmad ina roƙo idan da hali ka barta zuwa jibi, don kuwa aƙwai abubu da yawan gaske dana ke so ayi, ciki kuwa harda addu'o'i da kuma saukar kur ani me girma."

Malam ya gyaɗa kansa don ya aminta da hakan, ya ce"tabbas haka ne Zulaiha kinyi tunani me kyau,sannan kai ma Ahmad ka dage da azkhar na safe da maraice, yawancin mutane muna wasa da wannan babban azkhar ɗin, wanda shi ne Manxon Allah S.A.W ya keyi sannan kaima aƙwai tofin da zan maka na ƙwana uku, idan da hali kada ka faɗawa kowa wannan lamarin, don mugu ba shida fuska amman kayi haƙuri idan mun tirsasaka".

da sauri ya tari numfashin malam ya ce" ba komi Malam, nima ina toƙon gafara awajenku don Allah ku yafemin akan abinda ya faru tsakanina da Rabiatu".
Malam ya ce"ba komi Ahmad, tun É—azu kake neman yafiyarmu Allah ya yafe mana baki É—aya".

Dukkanmu muka amsa da amin, har ni dana ke cikin ƙuryar ɗaki ina jiyosa yana musu sallama, sai dai sallamar tashi cike take da manufofi don yana son yaga na fito, ni kuma na yi ƙulewa ta amman kewarsa cike take a ƙoƙon zuciyata, don inasom mijina shima yana sona na dai rasa dalilin canjawar komi, wanda ni na ɗaukesa ƙaddararmu ce haka.

*** *** ***
shigarsa ɓangarensu sha maki yayi dai dai da shigowar dalleliyar motarsa cikin gidan, yana fitowa ya ƙaraso da sauri inda ya ke ya ce"Yarima yau kai ne a sashenmu? sannu da zuwa".

ya ɗanyi murmushin gefen fuskar daya saba yi, sannan ya bashi hannu suka gaisa ya ce"muje ɓangaren mama mu gaisheta sai muje sashenmu ka huta ko?"…
saurin dakatar dashi yayi, ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce a taƙaice" muje sashenka kafin".

Babu yadda shamaki ya iya dashi, dolensa ya yi biyayya don ko ba komi ya É—an girmesa sannan kuma matsayinsa dana sa ba É—aya bane, shi yana É—an sarkin fada shi kuma É—an sarki? ai matsayin ma ba É—aya bane, kuma sannan yasan halin Yarima da rashin son magana, saboda haka ya yi abinda yace don azauna lafiya.

suna shiga ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon shamaki, ya ce"miƙomin ruwa me ɗumi insha".
da sauri ya tashi ya ɗebo masa ruwa a na'urar xafafa ruwa, sannan ya kawo masa a glass cup, da yake shamaki irin matasannanne masu tsaftar gaske, sannan komi nasu a tsaftace ya ke don har kitchen ne ƙato me matsaikacin kyau a ɗakinsa.

tunda ya kafa kansa bai ajje ba har sai daya shanye, duk da yasan illar da take cikin hakan amman ajje ruwan tamkar ƙara tafarfasa zuciyarsa ne, shiyasa ya kwankwaɗesa tsaf sannan ya ajje yana ajiyar zuciya.
Shamaki na lura dashi, duk da yana É—an danna wayarsa don aikin banki yake yi kunsan aikin yadda yake da sanya mutum a busy.

azuciyarsa kuws ce wa yake, Yarima ikon Allah wannan matarsa za tayi fama ba kaɗan ba, don mutunne shi mai masifar mskilanci, magana ma sai yayi niyyar yinta yake yi idan kuwa ya yita da yawa har haki za kaga yana yi, kyau tamkar shi yayi kansa musamman jan bakinsa dake matuƙar ɗaukar hankalin mutane da dama, ciki kuwa har da maza bama mata ba, gashi dogo ne samɓal irin mazan nanne masu tsayi sosai kuma yana da ɗan kauri amman ba can ja, idanuwansa sleeping eyes kullum alumshe suke tamkar me jin barci.

Shamaki ya ce"Allah ya taimaki yarima, sai naga kamar kana cikin damuwa ko"?.
Chapter 22 · 0% Book details