← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta kalleni cikin É—an jin haushina, sannan ta ce" wai mi yasa kike da zurfin ciki ne? kinsan kuwa hakan zai iya janyo miki ciwo? saboda haka ina umartarki daki nutsu ki haÉ—a zuciyarki waje É—aya ki faÉ—amin abinda ya ke faruwa"?.

Tayi ƙuri tana kallona babu alamar wasa akan fuskarta, na ɗanji shakkat ɓoye mata don nasan tunda na furta dole sai na ƙarasa wannan maudu'in dana ɗakko, don Ammi babu abinda ta tsana irin ka ha'ince ta a magana ko kuma ka ɓoye mata wani abu, musamman ma akan duk abinda ya shafeni ba ta wasa dashi. baki yana kakkarwa na fara maganar da ta kusa tarwatsa zuciyar Ammi, tuni hawayenta suka ƙame sai idanuwanta da sukayi jawur tamkar gauta.

"Ammi mama uwar gida da kuma Hajiyarsu Ahmad naji suna hira, wai zasu sanya a haukatani inbi duniya, wai Balaraba Facala ta ita ce zata je wajen boka a basu magani su haukata nabi duniy.........."

Kasa ƙarasa maganar nayi wacce ta tsaya a maƙogwaro na, saboda wani mugun wahalallan kukan daya ci ƙarfina, samnan Ammi ta dakamin wata gigitacciyar ƙara da ta kusa firgitani tun kafin asirin furgicin haukan ya kamani ta ce"me kike ce Adawiyya? su haukata ki kuma? mi yayi zafi haka? saboda kina auren ɗanta shi ne suke son su salwantar min dake, ke ɗaya tilo dana malakka arayuwata, tun bayan haɗarin jirgin daya mueƙushemin ahalina, mamana baba na, ƙanne na biyu, yayyi na biyu, wa nake dashi yanzu sai kakata da ƴan uwa kuma na dangi, shi ne ake son kema sai an rabani dake to wallahi ina musu albishir da sun taro mach ɗin da bazu su iya buga ƙwallo dasu ba, don kuwa sai na firgita rayuwarsu ta yadda ba zasu ƙara tunanin sanya wani ma ba wata ba a matsala". tana faɗar hakan taja hannuna na muka fita da sauri ni da ita, ni kuwa sai kallonta nake don ganin inda zata kai ni, sai dai babu damat tambaya? Domin fuskarta a matuƙar haɗe take babu ko alamar giftawar wasa a kyakkyawan fuskarta me cike da sirrin kyau irin na su na shuwa arab.

bata tsaya dani a ko ina ba sai a tsakiyar falon mama uwar gida, tana ganin mun shigo tayi saurin kashe wayar da take, ta bimu da wani irin mugun kallo na tsantsar tsana ta ce"ke kuma meye zaki shigomin É—aki ki tsayamin akai na tamkar wata sanda"?.

Ammi ta kalle ta kallon kin rainawa kanki wayo sannan ta harɗe hannunwanta a ƙirjinta sannan ta ƙara wurga mata wani kallo ta ce"ke kina tunanin wannan borin kunyar taki zai yi tasiri akai na? to bari kiji ni a halin yanzu daga ni har ahalina munfi ƙarfinki kuma Allah ya fiki, sannan ni bazan taɓa toma miki asiri ba, idan har halinki ne zaki ce zaki sake ko? to bari kiji ga fili ga mai doki saura sukuwa, sannan ni da ƴata ƙadangaren kan tulu ne, me taɓamu sai ya shirya ke har me kika taka aduniya? kuɗi ko matsayi? babu ɗaya acikin biyun nan sannan kuma maganar da kike na cewa zaku haukatamin ƴa gaki ga ta, idan har ke kin isa kina jin kanki ƙaramar ƴar iska to ki sani ni ɗin dai dai nake da ke, ga tanan gabanki ki cinye ta tsaf kada ki bar ko da romanta".
ta faÉ—i hakan tana nuna ta da manuniyarta.

kunya ta ishi Mama ta kasa ko da ɗago kai, sai dai tsabar jin haushin furucin Ammi sai girgiza ƙafarta take tana ɗan ciccije leɓenta alamar an kai ta bango, sanin idan tayi magana zata tonawa kanta asiri sai tayi shiru tamkar malam yaci shirwa.

hasina, maryam, badi'a, duk suna zaune komi ya faru sai harararmu suke ni da Ammi Hasina ita ce cikakkiyar mara kunya, wacce bata baro Mama a komi ba cikin rashin kunya ta ce" to ai mugun abu kema kina yi, tunda kim juyawa Abbiey hankalinsa baya ganin duk matansa da mutunci sai ke, Allah zai saka musu muguwa azzalu........."
bata ƙarasa maganar ba Ammi ta sharara mata wani gigitaccen mari, sannan ta nuna ta da manuniyarta ta ce" duk ranar da kika ƙara yimin rashin kunya, sai kin gwammace baki zo duniya ba,banza jahila wacce bata san mutuncin manya ba".
Tuni dukkansu suka liƙe bakinsu, ɗan ƙunƙunin da suke sai suka rufe bakinsu tsaf, ba tare da ko kallon banza sun yi wa Ammi ba, Hasina kuwa kuka ta fashe dashi, da yake mai taurin zuciya ce ta ce"mama kina kallon duk abinda take yi? amman saboda kina jin tsoronta kin kasa magana"?.

tuni Ammi ta ƙara janyo hannuwa na zuwa ɗakinta, ta jehomin mayafi na ta bani umarnin da in biyo ta,ni kuwa sakin bakina kawai nayi don nasan Ammi aƙwaita da masifar zuciya, matuƙar haƙurinta ya kai bango bata saurarar kowa, shi da kansa Abiey uxuri ya ke mata don yafi kowa sanin wacece Zulaiha.
kiran Abiey tayi awaya, kiran farko ya ɗaga tayi masa dabarun mu na mata, akan tana son taje dani kasuwa don siyo kauan kitchen saboda nawa wasu sun zama tsoffi, ya yarda ɗin kuwa muka tafi tunda muka hau mota babu wanda ya yi magana, har mukaje inda zamuje ɗin babban gida ne mai kusan kusurwa uku sannan yanayin gine ne na ƙasa, amman tsarin gidan ko a fuska yayi min sosai yasha daɓen farar ƙasa, wanda aka yisa a wanacan ƙarnin ko da ba a faɗamin ba nasan ba gine na yanzu ba.
Riƙo hannuwa na Ammi tayi muka shiga cikin gidan, kai tsaye ba tare da ɗar ko wani tsoro ba kamar dai ni yadda nake a tsorace, duk da nasan Ammin ba siyar dani za tayi ba, amman duk da haka a tsorace nake don kunsan mutum baya iya canja halittarsa, ni kuma aƙwai ni da tsoro da kuma rauni sosai.
muna shiga Ammi ta nufa babban sashen daya fi kowanne girma ta nufa tana riƙe da hannuwana har muka ƙaraso.
wani waje ne wanda aka ƙawatashi da lambu, sannan ga ciyawa awajen gwanin sha'awa, sallama Ammi tayi a ƙofar ɗakin, kusan sau biyu sannan aka amsa mata da ta shigo.
muna shiga naji gabana ya faÉ—i sosai da ganin mutumin dana gani É—in.................

*** *** ***
sosai yayi kyaunsa cikin farar shadda ƙal, kasancewar yau jumma'atu babbar rana ne, sai wani haske yake yana haɗawa da walwali tamkar wata acikin zarah.
Dai dai lokacin shamaki ya shigo ɗakin, ya kallesa cikin ɗan son shaƙiyanci sannan ya ce"bro irin wannan kyau haka? tamkar ango? ko da yake ai angon ne ma".
Yana saka agogo a tsintsiyar hannunsa bai ko ɗago ya kallesa ba, don shi ayanzu mutum tsoro yake basa, ba kuma ya son ya shiga jikin ko wani mahaluƙi a cutar dashi kamar yadda aka yi masa acan baya.Shamaki bai wani damu ba ya cigaba da tsokanarsa har suka fito sallah masallacin dake cikin babbar masarauta, shamaki ya ɗaga wayarsa yana ce wa"to mama gani nan zuwa".
Yana katse wayar ya kallesa cikin girmamawa ya ce"ranka ya daÉ—e mama ce take son ganina, gashi kuma mun fito sallah ko in ce mata bari muyi sallah?".
Galadima kenan aƙwai sauƙim kai sai dai idan baka zauna dashi ba, zaka iya sanyasa a maza masu matuƙar girman kai da izza, haɗi da faɗa sai dai sam ba hakan yake ba kamar dai abinda ya faru yanzu, bai kalli shamaki ba ya ce"yanzun idan nace maka kace mata sai zamu tafi masallaci sai ka faɗi hakan? uwa tafi gaban komi shamaki, muna iya ajje komi don mu yi mata biyayya indai har ba zai saɓa da ƙa'idar musulunci ba, masallacin bamuyi latti ba don kuwa ƙarfe sha ɗaya ne yanzun, to kaga muna da damar maki wajen yiwa iyayenmu biyayya, saboda haka ka fifita iyayenka sama da son ranka, sai kaga rayuwarka na cigaba duk da awani halin kana haɗuwa ne da nau ikan ƙaddarori da jarabta ta rayuwa". ya ƙarasa faɗar maganar yana ɗan haki, don bai saba magana a jajjere haka ba.
Sosai maganarsa ta tsaya masa, kuma sai yaji ya ƙara girmama Galadima sosai ashe haka halinsa ya ke? sai ka zauna dashi kake sanin hakan, amman da duk a wani matsayi suke kallonsa na me girman kai da izza da kuma son wulaƙanta mutum, ashe duk wanda kaga ya wulaƙanta wulaƙantacce ne kenan?.
Har suka isa ɓangarensu bai daina satar kallon Yarima ba, wanda ya ƙara masa wani ƙwarjini da kuma girma a zuciyar Shamaki, sai ya ke ganinsa tamkar shi ne sarkin Babbar masarauta.

falon ba kowa, saboda haka shamaki ya ce"ranka ya daÉ—e ina ganin kamar fa tana ciki, bari in shiga amman ka zauna kafin ta fito".
Galadima ya zauna ɗin kuwa, yana jan kyakkyawar tasbaharsa wacce ba komi yake faɗa ba sai HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL, ƙarfin wannan tasbihin ba kaɗan bane ƴan uwa mu kasance masu faɗar sa akowani yanayi akowacce rana, saboda ka bar kotun duniya ne ka kaiwa Allah kacokan buƙatar ka, sannan ko wanine ya cuce ka wallahi sai Allah ya saka maka, don ita ce fassarar Allah ya isa da waɗansu suke ganin don anyi musu Allah ya isa ai ba komi bane.

Kusan sakin babban farantin da ta ciko da kaya tai, har sai da ta ɗan saita kanta mamaki take me ya kawo Galadima sashensu? wanda ita dai da wayonta bata taɓa ganin ko da me kama dashi ne ba, sai gashi yau Allah ya kawo sa har hawayen godiya sai da ta yi wa Allah, sannan a ganinta wannan ita ce dama guda ɗaya daya kamata ta isar da saƙonta na soyayya awajen Galadima.
Kai guy ɗinnan kana da farin jin fa🥳ko zaka ɗan san min nima in yi wa Maher ɗina🧐😂😏, ko da yake ban san me gwaggwala ta jiƙa ta baka ba?🥹
Chapter 25 · 0% Book details