← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidanmu ɗaya da Facala ta,rana ɗaya muka tare da ita don ranar da aka kawoni a matsayin amarya ranar itama ta tare agidan amatsayin amarya,don rana ɗaya akayi aurenmu sai dai muna da banbanci me girman gaske,ta fannin hali da kuma nasaba dama komai.abu na farko daya sa Facalata ke ƙuntatamin shine mijina yafi sona,don kuwa ta tabbatar da hakanne a ɗan zaman da mukayi,alokacin ina amarya hatta aiki tare mukeyi ni da Ahmad,haka zai goyani muyi ta nishaɗi kasancewar ni anyi min aure da ƙananan shekarun da basu wuce 16, ba ayanzu kuma ina da shakera 17 a duniya don dai Allah bai bani haihuwa bane,amman cikina na farko zubewa yayi tun daga nan kuma ban sake samun cikin bama.
Balaraba ta haihu wato Facalata,ayanzu haka ma tana da wani cikin gwarnai tayi don Æ´atta bata fi wata biyu ba ta samu wani cikin kuma ayanzu haka gab take da haihuwa ko yau ko gobe.
Balaraba ba ƙarama bace kamar ni,don ita ayanzu tana da shekara kusan 29 ko 30 ma don mijin nata ma da kaɗan ya girme mata.
Abu na biyu daya sanya Balaraba ƙara tsanata shine kyau da ilimi,don ina da kyau sosai sai dai ni ba fara bace,ina da gashi mai kyau da kuma cika amman gashina irin me cika kai ne kuma yana da tsayi,gashi Allah subhanahu wata ala yayi min ƙira me masifar kyau,komai na jikina tamkar an tsaramin shi ne,ba ni da wani tsayi can amman baza a kira ni da gajeriya ba,kuma sannan ni ba me ƙiba mace amman ina da irin ƙirar nan da ake cewa koka kola,komai dai zan zan sannan ina da ilimin addini dana boko don kafin ayi min aure ina da haddar qur'ani cif cif akaina,sannan kuma na yi candy kafin ayimin aure,mahaifina yana masifar son yaga yaransa sun haɗa ilimi duka,don ni kaɗai ce ma ban jona da jami'a ba amman duk sauran yayyina sai sunyi degree suke aure,ni kaɗai ce awajen mahaifiyata kasancewar tunda ta haifeni bata ƙara haihuwa ba,matan Baba na uku ne ita ce kuma amaryarsu,mahaifiyata asalinta shuwa arab ce kyakkyawar gaske mai cika tamkar ni dai ƴarta ɗaya tilo.
fara ce sol ba kamar ni dana yo fatar mahaifina ba,don shi baƙine asalin hausa fulani kuma har kamanni ma wasu na mahaifina ne na ɗakko.

zumbur na miƙe ganin an turo ƙofar ɗakina,da sauri na juyo ina kallonsa shima ni yake kalla hannuna sarƙe a ƙirjina ina sanye da wata kyakkyawar rigar barci,wacce ta ƙwanta luf luf a lallausar fatar jikina,rabin cinyoyina duk awaje wai don duk a burge miji,sai dai kash ko kallona baya yi ballantana ma in sanya ran za'a yaba min,gashin kaina kuwa na tufkesa a tsakiyar kai na wanda yayi cukus yayi gwanin sha'awa kamar black america.
kallona yake sosai tamkar dai yadda ya sabayi idan yana kallona ako da yaushe.
Share hawayena nayi,don ni dai na rasa wannan masifar wallahi,muna son juna ni da Ahmad ba kaɗan ba soyayya irinta Layla majnun amman kuma yanzu duk abin ya canja lokaci ɗaya,ako da yaushe Ahmad cikin kallona yake yana masifar son kasancewa dani ayadda na fuskanta,amman kuma daya zo gare ni sai ya kasa sai dai ya koma gefe,abin yana matuƙar damuba gashi ina jin kunya na kasa faɗawa kowa,kai hatta da Innah ta mahaifiyata na kasa faɗawa,gani nake tamkar tona sirrin mijina nayi ayadda kowa yake ganin muna zaune lafiya da Ahmad,to inason aci gaba da kallonmu a haka ɗin.
Ahmad ya ƙaraso inda nake ya ce"wai me ya hanaki barci ne"?.
Tambayar tazo min a bazata,da mamaki na kallesa ina kallon agogon dake ɗaure a jikin bangon ɗakin,na ce"rashin dawowarka ne ya hanani barci habibi,kalli agogo fa ka gani ƙarfe nawa"?.
Kallon agogon kuwa yayi sannan ya ce"ƙarfe 11:30 menene"?.

Maganarsa ce ta harzuƙani na tashi cikin bala'in da ban san ina dashi ba na ce"haka ma zaka ce menene ko? kana can wajen ƴan iskan matan da kake bi shine zaka ce hak..............."

Wani irin bugu ya kaiwa ɗan ƙaramin bakina,nan da nan ya fashe har da jini na sanya hannuna ina dubawa naga jini,na firgice na fita daga hayyacina don Ahmad bai taɓa dukana ba duk da ba yau muka sabayi ba,matuƙar ya fita ya kai dare ban san lokacin da na taƙarƙare na sanya ihu iyakacin ƙarfina ba......................➡️soon🤪.

#MRS GREEN CE.

a dage da comments,da yimin share ni kuma in ta sambaɗo muku typing🥰

https://chat.whatsapp.com/DFeZycAMeQZ09jYzYRWCX0

ga link ɗina ga masu son shiga grp na facala,bana son talla da turo batsa duk wanda ya turo yasin ko gidanmu ɗaya sai na cire ka ehe🤪💃.

https://chat.whatsapp.com/B8xJCI0gOCiAvl71TTWjFS

https://chat.whatsapp.com/B8xJCI0gOCiAvl71TTWjFS

MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.

Abubuwan da ke ciki;
HaÉ—in Dilka
HaÉ—in man gyaran gashi
HaÉ—in sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
HaÉ—in gyaran (Breast)
HaÉ—in maganin infection
HaÉ—in furen zogale
HaÉ—in tsumin tabaje
HaÉ—in Kaza
HaÉ—in tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata

Bonus
Sirrin riÉ—i
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)

Za ku iya biyan kuɗin littafin akan fara shi sauƙi #1,500 kacal
Mutum 20 da suka fara biya na farko, zasu biya 1200, ku yi hanzari ku shigo sannan ku yi payment akan lokaci.
[1/9, 08:44] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
        {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

             _BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da yiwa Æ´aÆ´anmu zane kamar,kalangu,tattu da sauransu.domin canza halittar ubangiji.

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.
yana gyara breast sosai,masu son su ciko suyi gwanin sha'awa sai su garzaya su nemu na su.
idan kin shirya gyara ki kirawo MAMAN KHAIRYS SABAYAS🗣️🗣️🗣️🗣️.
08067329607.
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

➡️3 & 4

…………Jin ihu yasa Zubair ya kalli Balaraba ya ce"kamar fa ihun Rabiatu nake ji"?.
wani irin ya mutsa fuska tayi sannan ta ce"eh menene? ai ba abune wanda aka farashi yau ba,balle a daina sa yau ɗin yarinya sai shegiyar fitina,ke kullum faɗa da miji? ni wallahi banga amfanin auren mace irin Rabi ba? Ahmad baiyi dacen mace ba wallahi Allah dai ya bashi mace tagari,ni da zai ƙara aure ma ai da ya burgeni wallahi,ko ya samu farin ciki tunda ita ƴar masifar ba zata barshi ya huta ba".
Zubair ya kalli Balaraba ya ce"haba Balaraba,wai mi yasa kika tsani yarinyar nan ne? ai naga kema macece ko? ya zakiji idan akace mijinki me irin halin Ahmad ne? mijin da ba zai tashi dawowa gidansa ba sai tsakiyar dare? wallahi ni na rasa inda Ahmad ya É—akko wannan halin".
Balaraba ta ce"au ɗakko ma halin yayi kenen? kaima halinne da kai? ga masifar son ƴammata a cikinka kamar kaine ka yankewa mamajo cibiya,kuma a haka nake haƙuri da kai ban ɗagawa kaina hankali ba,itama sanyawa kanta tayi saboda haka duk wanda ya ɗakko masifa bakinsa a'i,shiyasa Hajiyarku ta ce"yadda uwarta ke juya Babanta haka itama takeson juya mata ɗa,to shi kuma da yake ɗan halak ne sai yaƙi hakan,to shine fa abin duk ya damesu daga ita har uwarta mai taken shuwa".

Zubair bai ce mata ƙala ba ya tashi ya fita,Balaraba ta tashi da sauri tasha gabansa tana ce wa"Abban Khadija ina zaka je ne"?.
bai ce mata komi ba ya wuce ta,abin nan ya tsaya mata arai ta dai daure ta bishi don ganin inda yake son zuwa É—in.
a hankali take binsa,ya É—anyi murmushi don yasan Balaraba ke binsa kuma a koda yaushe haka É—in take idan tana son yin gulma.

***              ***        ***

....Ganin bakina har yana zubar da jini yasa na juyo cikin kuka na ce"Ahmad babu abinda zance a wannan lokacin,Allah yana sama yana kallo kuma shi kaɗai ne zaiyi min sakayyar duk wani abu da kake min,kai a ganinka ɓatamin ɗin da kake Allah zai barka? in sha Allah wataran sai kayi kuka akan abinda kake min na cutarwa".
wani bugun zai ƙara kaiwa bakina na gauce,na ɗanyi wata ƴar dariya wacce ake cewa tafi kuka ciwo na ce"Ahmad kenan,zaluncin bai ishe ka ba kenan"?.
a harzuƙe ya ce"wallahi kika ƙara kirana da azzalumi sai na canja miki kamanni,banza mara kunya wacce ba a bata tarbiyya agidansu ba".
Wani malolon baƙin ciki ne ya haɗu da ɓacin rai suka haifarmin da kyarmar jiki,na juyo da sauri ina hawaye na ce"Ahmad yau iyaye na kake zagi son ranka? ni ce ƴar marasa tarbiyya? ni kake jifa da irin waɗannan kalaman"?.
a matuƙar harzuƙe ya ce"da suna da tarbiyyar ne? tunda har suka kasa baki tarbiyyar da ta dace,baki san yadda zaki yiwa mijinki magana ba? kullu yaumin ke sai fitina da rigima? da kuma zargi? to ki sani ba zamanki nake ba kece kike zamana,saboda haka ki kula da duk abinda zai dinga fitowa daga wannan banzan bakin na ki".

durƙushewa nayi awajen na saki wani irin gigitacciyar ƙara,tunani kawai nake anya kuwa wannan Ahmad ne? mijina wanda ke tattalin farin ciki na? wanda baya son inyi kuka? amman yau shine yake zagina da ƙuntatamin? awasu lokutan abin ɗaure min kai yake,sai na dinga tunanin anya kuwa shine ko waninsa?.
Chapter 2 · 0% Book details