Sashe 28
Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
kukan Ammi tsananta sosai, har tana fyace majina nima sai na ƙarawa kukan nawa bolum don ganin majinginata tana kuka wato mahaifiyata, bata taɓa bani wannan tarihin na ta ba sai yau, abu ɗaya take faɗamim kullum shi ne iyayenta sun rasu, amman bata taɓa faɗamin maƙasudin mutuwar tasu ba.
Tsoho ya gyara zamansa sannan ya ce" ku kasance masu haƙuri da duk abinda xai faru, don kuwa indai baka mutu ba to fa tabbas ba a gama yi maka jarrabawa ba, saboda haka aƙwai rubutun da zan dinga mata dai ki dinga zuwa kina amsa, sannan duk halin da kika tsinci kanki kada kiyi ƙasa a gwiwa kizo ki amsar mata, saboda ita ayar Allah tsari ce sosai daga dukkanin abin ƙi".
Sosai muke ta masa godiya, ya ɗakko wani ɗan mitsitsin allo ya rubuta ayoyin Allah sannan ya wankesu ya bani a wani ɗan ƙoƙo.
Na amsa na shanye tas, duk da ina cike da tsoro amman haka na daure nasha, sai kuwa ya fara tsokanata da ce wa" sai haƙuri fa ƴar lelen babarta, don ko da yaushe zaki dinga sha ne ko da kuwa bana wajen, don naga ina wajen ma kina kallon gyatumarki kina ya mutsa fuska".
murmushi na É—anyi, ba tare dana ce komi ba sai kuwa ya ce" ku shiga cikin gidan ku gaisa ko? daman wannan satin me bikin Isma'il".
a matuƙar firgice naga tana kallon tsoho, ina kallon yadda gabanta ke luguden faɗuwar gaba, shima ya fuskanci hakan amman da ya ke tsohon ya iya shariya bai ko kalle ta ba.
Muka shiga gidan duk jikinmu a matuƙar sanyaye daga ni har ita Ammin, a babban tsakar gidan muka haɗu da matan Tsoho da kuma matan ƴaƴansa wasu na daka wasu suna girki wasu kuma suna wanke wanke.
sosai suka ji daÉ—in zuwanmu musamman ma uwar gidan tsoho, wato Inna Sa'ada ta fara tsokanata da ce wa"oh yau sai ga jikata agidan nan, da aka rabani da ita don san ran gyatumarki".
Ni dai dariyar yaƙe kawai nake don har ga Allah kai na ya yi mugun kullewa akan wannan sarƙaƙiyar da suka jefa ni, wai an ɗaukeni a gidansu? to ni a yaushe ɗin na taɓa zama agidansu har ake iƙirarin anɗauke ni?.
Tambayar dana kasa amsawa kenan, don nima da kaina ban san me hakan ya ke nufi ba?.
bayan mun gama gaisawa ne ta ɗebo irinsu daddawa da kuka da sauran ƴan kayan miya ta bani, ina ta mata godiya sannan muka fito don tafiya gida, dai dai lokacin wani yazo wucewa ta kusa dani, ban san ya akayi jikinsa ya gogi nawa ba, sai kawai naga yana kallona nima na fara kallonsa Ammi tayi saurin jana nima na bita da sauri don wani irin abu naji ya tsargamin, tun daga ƙafafuwana ya zarce har zuwa ƙwaƙwalwata ya zarce zuwa abar tunƙahon ko wani ɗan adam wato zuciya.
***
Bayan ƙwana 2
komi ya kammala, don ayanzu haka ma ya Ahmad yazo ɗauka ta ne, ina jinsa Malam yana ce masa ya kula da shan maganinsa kada kuma ya yi wasa, ya ce" in sha Allah Malam ba zanyi wasa dashi ba Allah ubangiji ya ƙara girma da arziƙi". Mu duka muka amsa da amin.
Ban san ya akayi ba sai naga hawaye suna fitowa daga idanuwa na, alokacin da Ammi ta riƙoni tana ƙara jaddadamin duk hadisin da ta koyamin wanda tuni na iya ma har na haddace.
muka shiga ɗakin Umma, don yi mata sallama ta ce"Adawiyya duk wanda zai faɗi halinki baya gani ce, tunda ni ɗinnan ni na yaye ki a hannuna sannan rabi da ƙwatan zaman gidan nan da kika yi a ɗaki na ne, saboda haka nasanki nasan halinki ke yarinya ce me matuƙar biyayya da kuma sanin ya kamata, saboda haka ki kula sosai da zaman aure, saboda shi aure ibada ce wacce Allah subhanahu wata'ala ya sanyamu yin ta, sannan babu abinda ya tsana irin sakin aure shiyasa abinda ya faru atsakaninki da mijinki abin ya tsaya azuciyata, sai nake ganin kamar kina da sakaci ta hanyar addu'ah, sannan kuma ki kasance mace jajirtacciya wacce ke iya ɗauke duk irin ɗawainiyar dake gidanta, shi aure ɗam haƙuri ne kada kice idan namiji yayi miki wani abu kema zaki rama,yin hakan zai iya janyo miki hanyar shiga wuta wanda ke kika ɗauka ba zai ja miki komi ba, alhali shi kuma Allah yana fushi dake.
sannan lamarin facalarki yana buƙatar taƙa tsantsan, don a kullum a shirye take don taga ta cutar dake saboda haka ki kasance me kaffa kaffa aduk sanda kuka haɗu, sannan ki kasance cikin addu'ah da kuma yiwa mijinki biyayya sau da ƙafa, sai kiga komi ya zama tarihi".
sosai na fashe da kuka, tamkar dai yau ne ranar da zan bar gidan amatsayin amarya, ina rungume ƙirjin Ammi muka shiga ɗakin mama uwar gida, Sakina da Badi'a suna a falon mama, kowannensu yana abinda yasa agabansa, don kuwa Sakina tsaye take da wayarta a hannu tana ɗaukar kanta a vedio, kuma daga ganin tiktock zata ɗora, don nima da kaina na taɓa ganinta a tiktock ɗin, sai dai ban wani samu nutsuwar dama zan faɗawa wani ba, ita kuwa Badi'a zaune take tana chart amman vedio call ne.
Umma ta ce"ku dukkanku baku iya gaisuwa bane?".
Cike da tsiwa Sakina ta ce" haba Umma vedio fa nake yi, yanzu gashi nan kin ɓata min".
Umma ta ce" ikon Allah, daman ke kullum rashin kunyarki ƙara fitowa take, sannan wannan wayar ban sanku da ita ba daga ke har Badia ɗin".
Badia dake vedio call sai yanzu ta juyo, ba tare da tayi magana ba sai kallon banza da take mana na ƙasan ido,sakinah ta ce" eh baki sanni da ita ba gaskiya, iphone 12 ce saurayina ne ya kawo min ita".
Ammi dai bata ce komi ba, saboda ita ahalin yanzu ko kallon inda suke ma bata yi don bata san rashin kunya, Umma kuwa da taga za ta iya dasu gata ga su nan wai É—an koli a caca.
Mama na fitowa ta ce"lafiya ku kuma kuka cikamin falo? sai kace masu neman gafara?".
Ammi ta ce" lafiyar ce ta kawo haka, Adawiyya ce tazo don kuyi sallama yau zata koma É—akinta".
Sai kuwa mama ta zaro idanuwanta duka waje, gami da sake kallona sosai ta ce" uhm jeka ka dawo ba".
Ta faÉ—i hakan tana harararmu.
Umma ta ce" ko dai jeka ka zauna ba, in sha Allah ta koma kenan sai dai idan mutuwa ce zata rabasu ko shi Ahmad É—in ya birneta ko ita ta birneshi".
tana faɗar hakan muka fice, ina jin maman na ce wa"oho dai wannan gidan sai ta ƙara dawowa saboda mugun hali irin na uwarki".
Mu dau babu wanda ya kulata, muka wuce amman ni dai azuciyata takaicin halin mama ne ya cikamin zuciya, ita kullum tamkar yarinya ƴar yaye, kullum baka hankali sai dai rashin hankali da kuma hassada, bata kunyar faɗar duk abinda yazo bakinta matuƙar hassada ta rufe mata ido.
har bakin titi su Ammi suka rakamu sannan suka dawo.
Kallon ya Ahmad na yi cike da tambayoyi a bakina, shi kuwa kallon shauƙi yake mini tare da ƙara yimin kallon kina nan araina.
zaƙuwa nayi da tambayar dana ke son yi masa na ce" ya Ahmad ina motar taka yau kuma"?.
É—an basar da maganar yayi ta hanyar ce wa" tana nan tana gida ban dai taho da ita bane, na yi sha'awar shiga adaidaita sahu ne".
Duk da ban yarda da amsar daya bani ba sai nima na basar da maganar, amman ƙasan zuciyata na tambayata akan anya kuwa da gaske yake min? tun da mukayi aure bai taɓa yarda ya hau motar haya ba, tunda yana da motocinsa har guda biyu shima ya zubair yana da tasa guda biyu, sannan guda ɗayan ta ya zubair ya ajje mana ni da Balaraba duk inda zamuje ake kaimu, nima da kaina bana shiga motar haya to amman yau sai gashi yazomin da maganar da ba zan yarda da ita ba.
sosai gabana ya faɗi, ganin ƙofar sashe na a kulle ga kuma wani sashe na ɓangare na a ƙone sosai na waro ido ma ce" ya Ahmad me kuma ya samu ɓangare na? me yasa baka gayamin ba"?.
Duk alokaci É—aya na rattabo masa waÉ—annan tambayoyin?.
a ɗan kunya ce ya ce" ƙwarai ban gaya miki bane dama, lokacin da kika tafi gida washe gari ɓangarenki ya ƙone".
da sauri na kallesa na ce" ya ƙone fa kace? to me kuma ya ƙona sa ɗin?".
cike da basarwa ya ce"eh to ni dai bana ce ba, don sanda na fita na kashe komi na kayan wuta, sai da ya Zubair ya kirani awaya ya ke shaidamin abinda ya faru amman Balaraba tayi gaggawar kiran maƙota da ƙer aka kashe".
Sosai na waro ido, don nama manta da wata me suna Balaraba, sai yanzu ne dana tuno da ita hankalina ya yi matuƙar tashi saboda nasan halin Balaraba za ta iya komai don taga ta kassara rayuwata.
na jiyo idanuwana na zubar da hawaye na ce" ya Ahmad me yasa ka dage sai na dawo alhalin kasan ga yadda ɓangarena ya ke?".
ya É—an ware hannuwansa alamar shima bai sani ba?.
Takaici ya isheni har na kasa ɓoyewa cikin fushin na ce" to yanzu a ina kake son na zauna"?.
tambayar ma bata damesa ba ya ce"sashen Balaraba mana".