← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 29

Sashe 29

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 6 min read

da saurin gaske na kallesa har ganina yana sarƙewa, matar daba a ɓangarenta nake ba taka yimin laɓe gamida shukamin muggun tuggu awajen mijina da sirikata, shi ne kuma yanzu zan koma sashenta? lallai an kaiwa kura nama kenan?.
Tuni hawaye suka jiƙa fuskata, ya riƙo hannuna sannan ya ce" yi haƙuri munyi magana da ya zubair, akan ɗakunansu biyu zasu bamu sannan nan bada jimawa ba za a ƙarasa gyara naki ɓangaren, don komi naki sun ƙone kayan ɗaki dana kicin, kinga to kenan yana ɗan buƙatar lokaci, sannan kuma kada ki damu dan zaki zauna da Balaraba, na daɗe da sanin kina jin tsoronta, alhali kuma ita kullum so take ta kyautata miki, motata kuma da kike tambaya dukansu sun ƙone da maƙudan kuɗaɗen mutane aciki, wanda ahalin yanzu nake kan ganin na biyasi kuɗinsu, amman bazan iya biyansu ni kaɗai ba, ya zubair da Baba sun bani miliyan ɗaya tunda kuɗin miliyan biyar ne".

da mugun kallo na bisa, gamida hawayen tausayinsa duk aɗan ƙanƙanin lokacin nan komi ya faru? ƙonewar motocinsa biyu da kuma maƙudan kuɗaɗen mutane? da kuma ƙonewar sashena?.

sai na fara girgiza kai ina ce wa" tabbas wannan abin da aƙwai lauje cikin naɗi ya Ahmad, ta yaya za'ace komi namu ne suka ƙone banda na su Balaraba"?.
ya Ahmad ya ce"Adawiyya bana son ki ƙara wannan maganar, idan har ban godewa Balaraba ba ai ba zan zage taba, tunda ita ce tayi sanadiyyar zuwa ta kira mutane aka kashe wutar, da ɓangaren namu ma toka zai koma".

yana faɗar hakan yaja hannuna zuwa ɓangaren dana kirasa da kura handame me kallonki.
tana zaune afalonta tana waya, tana ganinmu ta yi saurin ɓoye wayar ya yinda cikinta ya fito sosai haihuwa ko yau ko gobe, Nana tana ta wasanta a ƙasan tiles, babu ruwanta da yarinyar wacce akace a dinga kula da ita saboda ciwonta.
murmushin fuska take mana, gamida yi mana lale marhabin sannan ta shiga gaba wajen nuna mana ɗakin da suka bamu ɗin, wanda daman ɗakuna shida ne a ɓangarensu muma haka.

kasa tsaida hawayena nayi, saboda ganin wai ɗakin da aka bamu ɗin katifa ce a yashe a ƙasa, sai filo ɗaya sai banɗakin dake manne jikin ɗakin, sai kuma ɗayan ɗakin wanda ba komi acikinsa sai tvn bango ko risibar kallon babu.

kuka na fashe dashi gamida faÉ—awa kan katifar dake É—akin.

Balaraba ta ƙunshe dariyarta gami da wuce wa cikin sanɗa sanɗa, har da turo mana ƙofa tsabar burinta ya cika akanmu.
ranar ƙwana nayi ina kuka, tun Ahmad yana rarrashina har ya dawo sanyamin ido saboda al'amarin ya fara basa haushi, in barsa yaji da abinda ya ke damunsa mana?.

Balaraba dake laɓe tana jin lallashin da Ahmad ke yimin ta tuntsire da dariya, gamida shigewa ɗakinta tana turo ƙofar ɗakin ta zauna abakin gadonta tana waro idonta waje ta ce"wo sai ni Balaraba duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, Adawiyya kike ko wa ma? uhm ai tunda kika ce zaki sanyani agaba idan na tashi ɗana miki tarko sai kinyi danasanin shigowa cikin rayuwata, sai na sanyaki kuka fiye da wanda kika yi yanzu, ba kince ke sai kin zauna da Ahmad ba? shima ya nace duk halin da ya ke ciki sai kin dawo masa? to zakuyi zamane ayanzu a ƙarƙashin ikona,wanda abinci ma sai ya gagareku duk sai nayi maganinku".
sai ta tuntsire da wata irin dariyar basawa sannan ta ce"saura plan B É—ina akanku, shi kuma daga gobe zai fara HHHHHHHHHHH".
ta dinga dariya ita kaɗai aɗakinta, sannan ta dannawa wata lamba kira, daga can ɓangaren aka ɗaga ta ce" yauwa kada dai ka bani matsala,idan kuma aka samu matsala komi zai iya faruwa da rayuwarka".
ta kashe wayar gamida wurgata kan gadonta, lokacin da taji shigowa motar Zubair gidan, sai ta ƙirƙiri tashi don ɗakko mana abinci wanda ada can bata yi ba, wai don duk ace mata tana kyautata mana.

ranar kasa rintsawa nayi, kukana yana ƙara tunzura zuciyar Ahmad, ya juyo ya ce" haba Rabiatu wannan wacce irin rayuwa ce, kinsan kuwa kukanki ya hanani barci, sannan kema kin hana kanki? don Allah ba don ni ba ki yi haƙuri kiyi shiru".

ganin naƙi yin shiru sai ya fita daga ɗakin, zuwa ɗakin kusa dani ya zauna kan shimfiɗaɗɗan kafet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin , yana jiyo kukana ya yinda yake jin babu daɗi abisa abinda yayi min, duk da ya yi iya yinsa.

wayarsa ce ta fara ruri, ya ɗaga duk da bai duba lambar ba gashi kuma cikin dare ne, muryar daya sani wacce ba zata taɓa ɓacewa ganinsa ba yaji, aka sheƙe da dariya sannan aka ce" haba Ahmad, ya zaka gujeni? duk irin nisan gudun da zaka yimin baka isa ka gujemin ba, tamkar taswirar inda kake ake zana min, saboda haka ka ƙwana da sanin asirinka ya kusa tonuwa wai an binno na binne".
sai aka kashe wayar, katse wayar sai yayi dai dai tsayawar ko wata jijiya ta jikinsa, yaji tamkar dama zai mutu ya huta da masifar dake tunkaro rayuwarsa, ranar yadda yaga dare haka yaga rana.

***
safiya na yi na tashi na ganni aƙasan tiles, ga uban sauran da suke kuka a ɗakin tamkar ba safiya ba, na kasa tsaida hawayena na fashe da kukan tausayin kai na, dana mijina shikkenan hankalin Balaraba ya ƙwanta ta cucemu.

banɗakin dake jikin ɗakin na shiga nayi wanka, da yake aƙwai sabulu sannan duk shayar gidanmu ta ruwan zafi ce, ina gama wanka na ɗauro alwala nazo na fara sallah ina kaiwa Allah kuka na.

ga kai na da yake masifar ciwo tamkar zai fashe, na É—akko cikin sabbin kayan da Malam ya É—unkomin, na sanya gamida saka babban hijabi.

na fito falom gabana yana faÉ—uwa, ya Ahmad da ya zubair suna falon suna hira.
ban san ya akayi ba sai naga sun koma min bibbiyu.

tun daga nan ban ƙara sanin me akeyi ba, sai lokacin dana farka likita na gani akai na, sai ya zubair da ya Ahmad suka dinga yimin sannu.

likitan ya ce"congratulations mrs Ahmad, kina da juna biyu har na tsawon wata uku".

A'i ban san lokacin dana hantsilo daga kan gadon ba, saboda tsabar gigicewa da rashin makama, to a ina na samo cikin? wanda rabona da mijin ma wata 8 kenan?.

tuni idanuwan Ahmad suka firfito gamida yin wani irin ja.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

*SAI KU BIYONI A LITTAFI NA BIYU, DANA UKU WANDA ZA KUJI KOMI BA TARE DA ÆŠAGA HANKALI BA*

500 ne kacal ki karanta cikin ƙwanciyar hankali, zaki tura kuɗinki ta wannan banking.
2212328303
ZENITH BANK
RABIATU BASHIR.

Sannan kiyimin magana ta no É—ina.
07068606171.
BYEEEEEEEEEE🥰

Alla ya jiƙan iyayenmu👏🏻🥹
Chapter 29 · 0% Book details