← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

washe gari da wuri na shirya cikin uniform ɗina na wajen aiki,don ayanzu muna lokacin hutu ne babu boko,Ammi ta ce"Adawiyya idan kinje kice ogan naku ta bugomin waya aƙwai maganar dana ke so muyi,yanzu ba nida numba ɗinta ne".
na amsa mata lokacin dana ke saka ƙaton hijabina,wanda nake rufe doguwar rigar da take jikina ta aiki.

    ina fitowa kuwa mukayi kiciɓis da ya Ahmad,ya riƙe baki yana kallona ya ce"a auta aikin kenan aka tafi? gaskiya an kusa fa a dena aikin nan,don nifa inada kishi wallahi".
É—an murmushi nayi ina wasa da Æ´an yatsun hannuna,sai kuwa ya ce"to muje in rakaki inga wajen na ku".
muna tafiya muna hira har muka iso,ya riƙe baki yana cewa"la la la ashe wajen naku na manya ne?".
muka shiga ya gaida oganmu wacce ta kasance macece,sannan gata da kirki sosai duk da yare ce ita.
bayan ya tafi na faɗa mata saƙon Ammi,ta kuwa kira sukayi maganar da zasuyi sannan ta kashe,kai tsaye na fara wucewa don lokacin dana bawa amaryar da zan yiwa ƙwalliya ya yi.
tana zuwa kuwa nayi mata,sosai tayi kyau ai kuwa ƴan uwanta ma waɗanda ba anan za a yi musu ƙwalliya ba suka biya kuɗinsu me tsoka aka rangaɗa musu tasu,har da cewa in basu lambar waya ta sai na sanya musu ta Ammina.

ina gama musu oganmu ta kirani,ina zuwa ta ce"Adawiyya an fasa yin decoration ɗin nan a unguwar shanu,a unguwar malali za ayi saboda haka yanzu zaku tafi,kuma ke na sanya shugabarsu ke zaki tsara komi,don naga sauran girma suka fiki amman kin fisu brain(ƙwaƙwalwa)".
na murmusa ina ɗan sanya lipstick a leɓena na bita muka fito compound,muka shiga motar baki ɗayanmu mukayi gaba.

muna kan hanya Ammi ta kirani,ta ce"yauwa ko da mama uwargida zata kiraki ta tambayeki a ina za kuyi aiki,kada ki yarda ki É—aga wayar".
nace mata "to".
azyciyata ina ta mamakin abinda yasa Ammi ta kirani,ina cikin mamakin sai kuwa ga kiran mama uwar gida don daman kaf ƴan gidanmu suna da numbar wayar wajen aikinmu,kuma idan muka fita aiki nike riƙe da wayar wajen aikin a hannu na.
mamaki nake sosai,amman sai naƙi ɗagawa ta kira yafi sau goma amman ban ɗaga ba,da ta gaji sai ta turomin saƙo.
dariya nayi bayan na karanta saƙon sannan na ajje wayar ma baki ɗaya.

****muna cikin haÉ—a wajen decoration É—in sai ga kiran safiya,wato Æ´ar gidan mama safiya itace autarta.
ina ɗagawa ta ce"Adawiyya yanzu naji mama da mamansu Badi 'a suna waya,wai tunda kinƙi faɗa musu inda kuke walimar zasu biyo muku ta wata hanyar ke da Amminki".

    kasa ce mata komi nayi,jikina yayi sanyi ƙalau,ina mamakin hali irin na waɗannan miyagun mutanen waɗanda basa tsoron Allah,na rasa mi yasa suka tsanemu haka? hawaye suka fara ƙwaronyomin sai naji ana kirana na juya don ganin waye............soon➡️
07068606171
ga masu son joining ɗin grp faccala,zasu iya bin wannan link ɗin na ƙasa bana son maza a grp sannan bana son ƴan masu turo ba tsa.

https://chat.whatsapp.com/L6lrdpNeslXEN6TlUzv4BA

*MRS GREEN CE✅*
[1/9, 08:44] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
Æ´an uwa mu yawaita yin istigfari,Allah ya yafe mana baki É—aya.

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️21& 22
…………………ina juyawa mamaki ya kusa kashe ni saboda ganin Ammina,da sauri naje na rungumeta ina kuka me tsuma zuciya.
na ce"Ammi wai mi yasa su Mama basa jin tsoron Allah?yanzu safiya ta kirani take shaidamin wai mamansu ta ce idan mun tsallake wannan ba lallai ne mu tsallake wani ba".

Ammi ta shafa kai na sannan ta ce"Adawiyya yadda muka tsallake wannan shima wancan ɗin zamu tsallake,hankalina ne ya kasa ƙwanciya har sai dana je wajen oganku ta ƙwatantamin nan nazo".
Tausayin Ammi ya kamani sosai,me yasa tun daga kan haihuwata har zuwa yanzu ya zame mata mabuɗin wahala? tun kafin ta haifeni ma tasha faɗawa wahalhalu kala kala,amman haihuwata sai ya ƙara wutar tsana tsakaninta da mama uwar gida da kuma Mama safiya,tun haihuwata har zuwa yanzu bazan taɓa tuno rana ɗaya da sukaji tausayina ba,ko amsa gaisuwata basa yi ni sai nake ganin ta wani ɓarin kamar gwara mama uwar gida akan mama safiya,sam ta tsaneni ni da Ammi na wai har cewa take ita da Ammi kishiyarta ce da ta daɗe da korarta,duk iya asirinta na sadaka yallah to ita ta dame ta ta shanye.

muna gama decoration ɗin mukayo hanyar gida ni da Ammi,muna zuwa gida muka tarar da wata masifar wacce tafi ta ɗazu yawa,don mama uwar gida ce xaune tana zuga baba,wai dama kusan ƙwana biyu haka Ammi take yi tana fita ba tare da sanin Abba ba,ina jiyo karaɗin miryarta tana ce wa"yo barewa za tayi gudu ne ɗanta yayi rarrafe? kaga tare ma suka tafi yawon,yo da haka ne ma fa zata koya mata yawon,daga haka sai kaji abu yayi girma ya girmi ne tarin tunani da kuma dattaku irinka,kai da ake ganinka malami ana ganin girmanka da ƙimarka duk sai ta zube saboda mummunan tsiron daya fito daga bara gurbi".
Duk bahaushe yasan abinda take faɗa,wato ni ce ma mummunan tsiron kenan? lallai tana son ta kaini maƙura wataran in kasa sarrafa jikina da harshena in faɗa mata maganar da har ta mutu ba zata taɓa mantawa dani ba.
Ammi ta kasa yin shiru har sai da ta ce"haba mama Uwar gida,me yasa kike haka ne? ai idan baki kare ni ba bai kamata kuma ki nemi tona asiri na ba,nasan ban kyauta ba dana fita ba tare da saninsa ba,amman ko menene ku kuka janyosa ke da mama safiya".

a'i da sauri ta ce"ke zulaiha uban me mukayi miki ni da mama safiyar? wani sharri kuma zaku ƙullamin? to duk sharrinki da tsanar da kike mana baki isa ki haɗa mana sharri ba,ƴar baƙin haure kawai".
Don kar a tona mata asiri sai ta shige É—aki,Umma dake tsaye tana kallon ikon Allah ta ce"Zulaiha kinsan mlm baya son fita ba tare da an sanar dashi va,ki kiyaye ko don nan gaba".
tana faɗar hakan ta shige ɗakinta,shi kuwa Abba tuni ya shige ɗakinsa bai ƙara cewa komi,kamar yadda na faɗa muku a baya shi Abbana mutum ne mara son hayaniya,musamman akan matansa kowaccensu baya faɗa ta faɗa duk rashin kunyar mama uwar gida,saboda shi bai taso yaga ana haka agidansu ba,sannan ga iliminsa wanda shima ya ratsashi sosai.

ni da Ammi muka shige ɗaki muma,duk hankalinmu ba a ƙwance ba don indai Abbana yayi shiru to tabbas shirun nasa ka iya zuwa ya dawo,don kuwa ɗauke musu wuta yake baki ɗaya ya fita daga sabgarki,yanzunma hakan ce ta kasance don kuwa ɗaukewa Ammi wuta yayi baki ɗaya,sai da ƙer suka shirya don abinda na lura dashi Ammi ta riga da ta kanainaye Abbana,ko yayi fushi da ita baya iya yin nisa kuma tsantsar kulawa ce kawai ba wai asiri ba,don ko da Ammi ta haifeni ba zakace ita ce ta haifi ƴar budurwa me shekara 13 ba,sai ka ɗauka wata ƴar budurwa ce sabida tsantsar gyara da sanin ƙimarta na ƴa mace,shiyasa baya gajiya da ita sam tasan takan gyara jiki ta ko ina don har gyaran jiki tana yiwa amare,musamman ma awajen aikinta na ƴan hisba tana samun costumer sosai,don mata da yawa kan kawo mata koke koke akan mazajensu na wulaƙantasu a shimfiɗa,sai kiga nan da nan ta baki shawararwari sannan ta haɗa miki haɗin ƴar gata,wanda nima da kaina nasan wasu daga ciki.

an sanya rana ta da yaya Ahmad,amman shekara guda aka sanya Hajiya kamar za tayi hauka don cewa tayi babu wanda ya isa ya É—aurawa É—anta aure da É—iyar mayu shuwa arab.

abu yayi tsamari sosai,don a yanzu haka ko gaisuwata ma Hajiya bata amsawa,ban damu da hakan ba don dama ko acan baya ba kullum ne take amsa sallamar tawa ba.

Yaya Zubair yana son Baby ƙawata sosai,amman ko da Hajiya tasan da hakan cewa tayi indai ya aure ta babu shi babu ita,don dama ita a yaranta tafison Ahmad,don duk abinda yace tayi shi take yi,saboda haka shiyasa ta sanya masa ido akan aure na don ba zata iya magana ba kamar ma tsoronsa take.

rana É—aya Yaya Zubair ya juyawa Baby baya,duk da dama ta É—an girme min amman al'adar gidansu ma da wuri suke aurar da Æ´aÆ´ansu tunda fulanin usul ne su.

Hajiyarsa tace indai matar aure ce zata nemo masa wacce take so,haka kuwa akayi don tuni ta nemo masa ƴar ƙawarta ashe dama ta daɗe tana sonsa me suna Balaraba,Hjy ta sani sarai kaf ƴan gidansu Balaraba ba suda tarbiyya ko kaɗan,yara ne masu bala'in jin kai da kuma yawon tsiya,ina ga gidan biki ko paty ga bin bokayen tsiya,don mahaifiyarsu ta koya musu duk halinta,ita da kanta idan ta fita tun safe sai dare take dawowa tana can tana yawon ta zubar,sannan uwa uba mahaifinsu bai isa yayi ko da tari ba don yana masifar tsoron matarsa,duk abinda tayi me kyau ne ko mara kyau ne haka yake haƙuri yaja bakinsa yayi shiru,don idan safiya tayi duk ƴammatan gidan da samarin gida ficewa suke daga su har uwar,shine yake zama agidan yana ɗan yi musu aikatau tun daga kan wanke wanke da shara,wankinsu duk shine ke yi idan kika shigp gidan kika ga aikin da yake yi sai kin zubar masa da hawaye tsabar takaici,kuma ahaka Hajiya ta rufe idonta tace dole sai Zubairu ya auri Balaraba,idan baiyi haka ba zata cire ta cikin ƴaƴanta,babu yadda ya iya da ita don Zubairu mutum ne me matuƙar biyayya ga iyayensa,don dole ta sanya shi sintiri hanyar gidansu Balaraba,amman duk sanda zaije sai ya yi azkar saboda wani turare da yake sanyawa sam bata sanshi,yaya Zubair likita ƙwararre na mata yana kallon Balaraba yasan ta gama yawon ta zubar ɗinta tun da kuwa gashinan har da tsarabar ciki.
Chapter 15 · 0% Book details