← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can ɓangaren Umma ta ce"inye ɗan kuka me jawa uwa tasa zagi,yanzu kai Zubairu bakaji kunyar maganar ka ba?,matarka uwar ƴaƴanka kake so ka saka? saboda wata banza wacce ma ko ƙuda bata ajje mana ba? juyar yarinya wacce sai dai taci ta ƙwanta? akanta ne kake wannan haƙilon saboda an taɓani? ko an taɓa Bilkisu da Aisha ƙannenka"?.

ya ce"to Umma ni de indai akan wannan maganar ce gwara in kashe wayata,don ga Nana can ba lafiya yanzu ma ƙara mata jini za'ayi don babu jini jikinta ya ƙone".

  Ai kuwa sai cewa Umma tayi"uhm kaji ko? ai daman bazasu barta da jini ba,Allah kaji ko? ko Balaraba bata ɗauki mataki ba Allah ni sai na ɗauka don idan kai baka san mutuncin kanka da darajarkanka ba to mu munsani,ta inda ƙaninka ya fika kenan? Ahmad bai taɓa bijirewa magana ta,amman kai babu abinda ka sani sai ƙuntatawa waɗanda suke sonka,kake son waɗanda suke cinye muku kuruwa".

  bai kashe wayar ba har ta gama sababinta,don kanta tayi shiru shi kuwa ya fito don siyan jinin sai dai duk jinin da aka gwada babu irin na ta,haka ya haƙura ya koma gida kai tsaye ya ƙwanƙwasa ɓangaren ɗan uwansa.

kamar daga sama naji ana buga sashen mu,nima alokacin na kasa barci na tashi ina sallah ina kaiwa Allah kuka na,ga bakina daya kumbura sosai sai dana É—an gasa shi da ruwan zafi sannan ya koma normal amman ba kamar yadda yake da ba.

Shi kuwa sai barcinsa yake,na tashi ahankali naje bakin ƙofar tsoro ya ɗan ɗarsu araina na fara magana ahankali"waye anan".
Kamar daga sama na jiyo muryar Yaya Xubair,da sauri na buÉ—e masa ina ce wa"sannu Yaya Zubair,Allah de yasa lafiya"?.
Ya ce"to lafiyar de ba lafiya ba don Nana ce a asibiti kuma ayanzu haka tana buƙatar jini kuma an gwada na can yaƙi yi,shine na dawo muje da Ahmad ko zaiyi dai dai tunda jininsa O   ne.

da sauri na ce"subhanalillahi,ai ba muga ta zama ba muje har dani sai a gwada don nima O É—in ne dani banbancin nasa dana wa shi Nagetive ni kuma positive".
ya ce"a a baza ayi haka ba je ki faÉ—a masa tukunna ya taso".
Nasan zan iya janyowa kaina zagi don haka nace"ba komi muje kawai don yanzu tunda ya fara barcin nan ba tashi zaiyi ba".

   Bai ce komi ba ya wuce muka tafi,duk jikina amatuƙar sanyaye zuciyata cike da tausayin Nana Khadija,don tunda aka haifeta yarinyar har yau bata yi lafiya ba,batz cikakkun ƙwana biyar ba tare da ciwon ya tashi ba.kuma har da sakacin mahaifiyarta don haryanzu bata dena yi wa  yarinyar wanka da ruwan sanyi ba,sannan kuma maganinta ma sai taga dama take ba ta,abinci ma sau biyu yarinyar ke ci arana,don dama tuni ta yaye yarinyar wai ita ba tasan yawan takura,uban baya so amman ahaka ta yaye ta babu yadda zaiyi tunda abin a jikinta yake.

  Ashe Hajiya ta fito acikin wannan daren,tazo ta buɗe Balaraba sai kuka take ta faɗo kan Hajiya tana ce wa"ina ya kai min ƴata Hajiya"?.
Hajiya ta ce"yace min suna asibitin da ake kaita wai ba tada jini".
da sauri suka tafi asibitim Balaraba sai kuka take.
Muma alokacin muka shiga asibitin,Balaraba na gani na ta........Soon➡️✍🏽

ga link na facala game nema,bana son maza a grp da ƴan iska ehe😎😂.
https://chat.whatsapp.com/DFeZycAMeQZ09jYzYRWCX0

#YARIMA
#RABIATU
#AHMAD
#BALARABA
#ZUBAIR

MRS GREEN CE.

SHARE
COMMENTS.

TALLAH TALLAH TALLAH

MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.

Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾

HaÉ—in Dilka
HaÉ—in man gyaran gashi
HaÉ—in sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
HaÉ—in gyaran (Breast)
HaÉ—in maganin infection
HaÉ—in furen zogale
HaÉ—in tsumin tabaje
HaÉ—in Kaza
HaÉ—in tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata

          Bonus
Sirrin riÉ—i
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)

Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga
Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani 07068048901 SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.
[1/9, 08:44] Ummu maher ce: F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
        {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

             _BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
ki kasance me tsaftace jikinki da kuma gidanki,yin hakan zai sa ki ƙara samun muhalli awajen me gida.

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️7 & 8
…………………sosai gabana ya faɗi,don ganin Balaraba don nasan wannan zuwan na su ba zai haifarmin daɗa me ido ba,sai ma na fara jin tsoro akan abinda na yarda na aikata don sam ban so na biyo Yaya Zubar ba,amman yafi ƙarfin wannan awaje na yana iya sadaukar da farin cikinsa sabodani,duk masifar matarsa idan yaga damar abu bata isa ta hanashi basai dai gani da hange shiyasa take kirana da mayya saboda wai na lashe mata kuruwar miji.

    Ban kula ba ashe tare suke da Hajiya sai da suka ƙaraso gab damu idanuwana ƙuri akansu,jikina har tsuma yake tun dama ni ina da tsoro sosai ga kuma muguwar shagwaɓar dana taso da ita awajen mahaifana duka biyu,don kaf gidanmu kowa yasan nice ta gaban goshin Abba shiyasa ma ake ce min ƴar lelen Abba ko kuma Rabin Abba.kamar daga sama naji Hajiya na ce wa"iko sai rabbani,idan baka mutu ba za kayi kallo? yanzu tsabar maita nan ɗin ma sai da kika biyo mu? yarinya ta koma kamar ƙashi duk ta dalilinki? kuruwarta kur de wallahi,duk maitarku sai da kuci kanku daga ke har uwar taki mayya masu cinye ƴaƴan mutane,shiyasa ma duk ƴaƴanta take cinye su aciki kece de da kika gado ta da maitar tsiya kika fito duniya saboda ki tayata lashe kurwar mutane".........
   
       Kafin ta kai aya Balaraba ta karɓe da cewa"kuma wallahi ƴata tafi ƙarfinki mayya,kawai idan kina tutiya kin cinye kuruwar mijina to ni wallahi nafi ƙarfinki,kuma waye ya gayyato kixo nan wajen? tun da de babu dangin iyaa ballantana name dattin hula me kalle ƴaƴan mutane akan titi tunda uwarki ta hanashi ya cike da ta huɗu,wai ku shuwa ko? to wallahi mu baki isa ki gama damu ba,banza me bin mazan mutane karuwa".
    kuka na fashe dashi kawai,zuciyata sai tafasa take tamkar xata fito waje tsabillar baƙin ciki,wai ni meye na yiwa waɗannan mutanen har haka ne? ni ba daɗin mijin nake ji ba? ballantana suce wai na gama dashi? inbanda baƙar wahalar dana ke sha uban me na tsinta agidansa? sai baƙin ciki da kuma nadamar aurensa marar misaltuwa,kullum sai nayi kuka sosai akan wannan hatsarin dana ke ciki gaba damisa baya zaki karasa inda zaka sanya ƙwaƙwalwarka kaji daɗi.
    Alokacin yaya zubair ya ƙaraso ya sameni sai kuka nake idanuwana sunyi jazur,ya ƙaraso yana kallonsu hajiya ya rasa me xai ce musu ya buɗe bakinsa zaiyi magana sai ya jiyo muryar hajiya tana ce wa"to sallamamme,wai ni anya kuwa ba Zulaiha da Rabi na haifawa Zubairu ba? sai rawar ƙafa kake ka ƙaraso kana huci don ka dakemu don an daku ƴar gwal ɗinka ko?, to bari kaji wallahi tallahi idan bakayi wasa ba kan wannan yarinyar sai na sassaɓa maka."
    caraɓ ta amshe da cewa"hajiya wai miyasa kike jin tsoronsa ne? ki fito ki faɗa masa mana,idan sonta yake ƙaninsa ya saka sai ya aure ta ko?, yanzu tsabad kai baƙin azzalumine shine kaje ka ɗakkota alhali ni ka kulleni aɗaki?, saboda kana sauri ku tafi hotel wajen yawon.........."
    A'i bata ƙarasa ba taji wani wahalallan mari,wanda mai shi yake jin tamkar zai tsaga kumatunta saboda ya huce daga azabar raɗaɗin da ta saka azuciyar wanda ta ƙuntatawa,ta jiyo zata sake magana ya ƙara mata wani ya fara nuna ta hannunsa yana kakkarwa,hajiya tayo kansa da zagi da masifa amman bai saurare taba,sai daya gama zazzaga mata masifarsa sannan ya fara faɗa mata wasu maganganu waɗanda suka sanyata sumewa na wucin gadi ya ce"Balaraba idan kin gama faɗamin maganganun da kike so daga yau kada ki koma min gida ki tafi gidanku sai na neme ki"?.

ba ita ba hatta ni sai dana razana,ita kuwa gigicewa tayu tana ihu tana cewa"Zubairu ni kake faɗawa haka saboda wata? wannan tsinanniyar yarinyar mayya?, to wallahi zaka san kayi da ƴa don wallahi sai dai ka aikomin da takarda don wallahi ba zan cigaba da zama da kai kana wulaƙantani akan wata ba".
Chapter 5 · 0% Book details