← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malamin ya juyo da sauri ya ce"caɓɓijan,aƙwai matsala fa Balaraba idan baki tashi tsaye ba".
Sosai ta waro ido ta ce"na shiga uku malam,wacce irin matsala kuma?".
Bushewa yayi da dariya sannan ya ce"ai ina faÉ—a miki idan baki yi abinda muka sanya ki ba zaki iya shiga cikin mummunan tashin hankali,saboda haka ku bada kai bori ya hau kawai".
shiru tayi tana tunani sannan ta ce"amma boka babu wanda yasan fa da wannan matsalar,ina tunanin kada Zubairu ya gane komi don wallahi inasonsa ba zan iya rabuwa dashi ba,asan dai yadda za ayi kawai komi ya zama tarihi".
dariya yake ta ƙeta sannan ya ce"Balaraba ina jiye miki faɗawa halaka mafi muni arayuwa,sabida haka ki yarda kawai da abinda zan faɗa miki" .

wani irin kallon banza tayi masa,a fakaice tana ɗan toshe hancinta ta saba mu'amala da manya manyan malamai waɗanda suka amsa sunansu,don kuwa ko ƙamshin turarensu ma na musamman ne,amman shi wannan sai ɗan karen wari tamkar ma baya wanka,amman ahaka yake son ta kasance dashi saboda biyan buƙatarta? anya kuwa za ta iya? ita dai ta sani arayuwarta macece me masifar son turare duk da itama ba tsaftar ce da   ita ba amman kuma tana son turare,kuma mijinta ma mutum ne me masifar son turare,abinda ma ta lura dashi shi ne duk ƴaƴan hajiyar suna da son ƙamshi,shiyasa itama zama da maɗaukin kanwa yasa take son ƙamshin.

maganarsa ce ta dawo da ita daga hayyacinta,don irin gardawan nanne masu masifar ƙatuwar murya,ba don aikinsa yana da kyau ba da tuni tabar masa wannan shegiyar tabarmar tasa me cike da dauɗa da wari.

   "nasan kina tunanin wannan warin dana ke yi ko? to kada kiyi mamaki don kuwa sai inyi wata biyar banyi wanka ba,shiyasa aikinku yake ci sosai son haka mukayi alƙawari da aljanun birnin maƙasudi,kinga kuwa ai bana karya musu alƙawari ba,amma kada ki damu idan za muyi sai inyi abinda ba zakiji warin ba".…

kallon ƙasan ido tayi masa sannan ta ce"kai gaskiyar magana inason cikar burina,amman kaɗan shafa turare mana".
kallon ƙasa shima yayi mata sannan ya ce"uwa riyonki yarinya,ni zaki yiwa wayo ki karyamin sihiri ko kina so ko bakiso dole sai nayi abinda nake so saboda nima ai ina miki abinda kike so".
ba yadda za tayi don tun ba yau ba tasan halinsa,kuma matar da ta  yi mata hanyarsa ta faɗa mata dattijon aƙwai maita,idan kuma ya sanar miki muddin bakiyi ta daɗi ba,to tabbas za ki haɗu da masifu kala kala da ke da kanki zaki kawo kanki wajensa.
gudun kada ta samu matsala yasa ta bada kai bori ya hau.

***              ***             ***
ranar da aka sallameni kuwa gida nayi,don Ammina ta kasa ta tsare tace babu inda zanje,sabida haka ma yasa ban wani damu sosai ba don tun inason Ahmad yanzu naji ya fice min araina baki É—aya.
Umma ce tazo dubani amatan Babana,amma Umma uwargida ce wa tayi babu inda za taje,kuma ko kunyar Ammi bata jiba tace ita fa baza ta zo ba.
Umma ta kalle ni ta ce"yanzu Adawiyya haka Ahmad É—in ya ce miki"?.
É—aga kai na nayi cike da kunyarta,don ma nafi buÉ—e mata cikina akan Ammina duk na faÉ—a komi,alokacin Ammi ta fita waje siyo min ayaba dana ce ina so.
Umma ta ce"Adawiyya har ga Allah yanzu bana son zamanki da Ahmad,sannan ni ayanzu ma na fara zargin aƙwai wata maƙarƙashiya,zaman gidan auren ne ba a son kiyi sannan ni a ƴan ƙwanakin nan ina mafarkai da dama akanki don Allah kada ki koma don ni dai sam zuciyata taƙi jinin gidan da kike ciki".
   kama hannunta nayi ina kuka na ce"Umma ya zanyi ne wai? duk sanda na kawowa su Ammi ƙararsa kafin ma in ƙarasa sai suce wai inyi shiru,damuwa tana yimin yawa Umma wallahi na tsani Ahmad yanzu,saboda shi bai san damuwar kowa ba sai tashi,sannan uwa uba mahaifiyarsa da facala ta Allah sun tsaneni Umma,da za a basu damar harbeni da tuni sunyi yadda suke so dani,Umma yaya xanyi yanzu don nasan halin Abba zai iya cemin in koma daga baya".
Rungumeni tayi a ƙirjinta,hawayena yana ɗiga a kafaɗarta tana rarrashina har Ammi ta dawo.

tare suka shigo da Abbas,ya ƙuramin ido tamkar tsohon maye ni kuwa haushinsa ma ya sanya ni juyawa kawai ba tare dana ce komi ba,wasu hawaye masu xafi suna sakkomin alokacin dana tuno da rayuwa ta tabaya wanda magogi ba zai taɓa goge mummunan tabon dana adana azuciyata ba,wanda kuma ya fito fili bai kai wanda na adana ba...........soon➡️

a tayani share masoya🥰

#ZUBAIR
#ALIYU
#RABIATU
#BALARABA
#AHMAD.

MRS GREEN CE.

MATA da yawa na fuskantar matsaloli, wanda mafi yawa daga ciki su ne su suka haifar da matsalar da kan su, tamkar dai sun ɗauki wuƙa sun daɓawa cikinsu, garin neman gyaran gira sai aka rasa ido. Hausawa na cewa'lafiya uwar jiki.'Saboda babu abin da ya kai lafiya daɗi, haka yasa na zurfafa tunani na ta hanyar kawo ma 'yan uwana mata wannan littafi mai suna *SIRRIN MOWA* kacokam littafin zai koyawa makaranta ingantattun hanyoyin gyaran ciki da wajen jiki, ta hanya ingantacciya wacce ba zata saɓa ma ƙa'idar lafiya ba, duba ga ƙurɓe-ƙurɓe da haɗiye haɗiye tare da cushe-cushen magungunan mata barkatai da mata ke yi, ba tare da tantance wanɗanda suka saɓa ma ƙa'ida, 'yar uwa wannan littafin zai koya miki yadda za ki haɗa komai da kanki, ki yi ƙoƙari ki mallaki na ki.

Abubuwan da ke cikin littafin kaloli dabam dabam na👇🏾

HaÉ—in Dilka
HaÉ—in man gyaran gashi
HaÉ—in sabulun gyaran jiki
Haɗin ƙugu(hips)
HaÉ—in gyaran (Breast)
HaÉ—in maganin infection
HaÉ—in furen zogale
HaÉ—in tsumin tabaje
HaÉ—in Kaza
HaÉ—in tantabara
Haɗin ƙamshin jiki
Haɗin ƙamshin baki
Ingantattun maganin mata

          Bonus
Sirrin riÉ—i
Sirrin magarya
Sirri magaruwa
Sirrinmu(Addu'oi)

Za ku iya biyan kuɗin littafin akan farashinsa mai sauƙi #1,500 kacal amma ga garaɓasa ga
Mutum 30 da suka fara biya na farko, zasu biya 1000 kacal, ku yi hanzari ku yi payment akan lokaci don neman ƙarin bayani 07068048901 SIRRIN MOWA NA MANYAN MATA NE, MATAN SO BA MUNA MATA BA.
[1/9, 08:44] Ummu maher ce: _*🌈F𝘼CC𝘼L𝘼 🌈*_
        {{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

             _BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*Sirrinmu➡️*
ƴan uwa mu yawaita yin sallah akan lokaci don gudun saɓawa ubangiji.

*_SABAYA KAYAN MATA🥰_*
ko kunsan sabaya na gyara jiki🗣️ta ciko miki da ni',imarki a matsayinki na ƴa mace🗣️in har kika rasa ni'ima to tabbas kin zama saura🗣️🗣️na ce ba? kin haihu kinƙi ki koma dai dai? to wallahi ga sabaya zata gyaraki ciki da waje,ta matseki ta dawo miki da martabarki,ita sabaya bata cutarwa ko kaɗan sabida ƴaƴan itatuwa ce herberls.tana ciko da mama yayi kyau sosai.
08067329607.

➡️17& 18
*…………………LABARINA*
sauri nake sosai har ina haɗawa da ɗan gudu gudu,murmushi ne ɗauke akan kyakkyawar fuskata me ɗauke da dara daran idanuwa masu kama dana turawa,daman ni tun ina ƙarama mutane da yawa ke tsokanata da ƴar bature,ba fara bace ni baƙace amman kuma ni kyakkyawa ce rawn face ce dani gashina har gaban goshi,saje kuwa har wanu nannaɗewa yake a ƙwance tamkar baƙar ba indiya.

ina da dimple me matuƙar tafiya da dukkanin ruhi da sanyaya zuciya,ni ɗaya tilo mahaifiyata ta haifa bayan ni kuma bata kuma ba har nake da shekara 13.

    tun a ƙofar gidanmu na tabbatar da cewa yaya Ahmad ya dawo,nayi murmushi dimple ɗina ya lotsa ya bada wani irin sirrin kyau da tsantsar ƙuruciya, har xan shiga gida sai ga Baby ta taho da sauri tana murmushi itama,aminiyata ce tare muka taso da ita anan bayan gidanmu take,tana murmushin ta ce"yau ya Ahmad ya dawo"..
iyayi ne dani sosai,don haka cikin yauƙi da yanga ba ce"to an riga ki".
Murmushin ta sakeyi ta ce"to mu shiga a kunce tsaraba dani".
na ce"no ba zai yiwu ba,ni kaɗai nake so Ya Ahmad ya fara gani,saboda haka ki saita hanyar gidanku ato ba zaki ƙwacemin shi ba".

     dariya take har tana riƙe ciki sannan ta ce"oho wallahi ni de sai na shiga".
ture ta na fara yi wai bazata shiga ba,amman sai da ta ture ni ta shige gidan na sanya kukan ƙuruciya ina ce wa"wallahi na dena kulaki banza fara kamar farin fenti".
haka tayi shigewarta gidan tana yimin dariya.

na shiga gidan ina kuka,mama uwar gida ce a babban tsakar gidan namu tana ganin na shigo ta ce"to shagwaɓaɓɓiya,uwar mi akayi miki da zaki shigo kina yiwa mutane taɓara"?.
tsayawa nayi na ce"mama wai Baby ce tace sai ta rigani ganin yaya Ahmad,ni kuma ina tsoron kada yace ya dena sona ita yake so tunda ita fara ce".
wani mugun ranƙwashi ta gasa min a kaina tana riƙe haɓa ta ce" ke kiji min shegiyar yarinya? wacce tasha ruwan karuwanci a maman uwarta idan banda haka ya za'ayi ace kamar ki shekara 13 har kinsan wata soyayya? kai gaskiya Zulaiha bata ji daɗin rayuwarta ba,ƙwaƙwar son namiji ashe ba ita kaɗai keda shi ba,ƴarta ma ta gaje ta ashe? ko da yake sanin hali yafi sanin asali zakiyi fin haka ma,don dama itama ance ba ƴar halas ba ce,kema ba don agabanmu akayi cikin ba ai sai muce can aka samo ki acab yawon sadaka yalla,wanda aka gada tun kakanni da uhm uhm".
Chapter 12 · 0% Book details