← Book details Facala Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 29

Sashe 1

Facala Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

[1/9, 08:44] Ummu maher ce: F𝘼C𝘼L𝘼 🌈*_
{{}}Ta fi kishiya🔥{{}}

_BY_
_*©UMMU M𝘼HER(MRS GREEN)*_💚

*_Wattpad✅_*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333

*_𝘼rewabooks✅_*
https://arewabooks.com/user/rabiattu0444

*_M𝘼RUBUCIY𝘼R_*

1-Uwar gidana
2-Auren dole
3-Ruhi É—aya
4-Farouk
5-Inayatullah
6-ƙaddarar Rayuwa ce
7-Akan aiki na
8-Jamila
9-Doctor Nawwara
10-Darasi
11-Silar fyaÉ—e
12-Basma
13-Abin cikin ƙwai
14-ÆŠinyar makaho
15-Inda ba ƙasa
16-Zulfah
17-Asanadin abayar sallah.
18-Facala🔥.

*Doka🧧*
Ban yarda wata/wani ya canjamin labarina ta kowacce siga ba,idan mutum ya aikata shi da Allah.

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم*

_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*➡️1 & 2*

............shiri ake sosai na tarar ɗan gata autan Momma,kai ka ce wani biki akeyi agidan ko wani sashe na gidan zaka ga suna cike da nishaɗi da kuma murnar dawowar Autan Momma,har anko akayi na murnar dawowarshi gwanin sha'awa maza suna sanye cikin cort fara sol da kuma wandonta baƙi,ya yinda aka yiwa gaban rigar ƙwalliya da flower me ratsin ja an rubuta love ajiki.
mata kuma suna sanye da dogayen riganu masu santsi maroon colour wanda duk suka yi gown dashi ƴammata sune masu wannan kalar,manyan mata kuma less ne me ruwan baƙi da Red,abin dai sai wanda ya gani gwanin sha'awa.
daga can gefe wata matashiyar budurwa na hango tana shirinta ahankali tamkar dai babu inda zasu je taro babban baƙo,tana cikin saka ɗankunnenta taji ana ce wa"Autar Momma fito mana,kinsan ba bro baya son jiya kuma jirginsu ya kusa sauka".
ÆŠan turo bakinta tayi kamar za tayi kuka ta ce"Allah ni don Momma tace in shirya Allah da bazan fito bama".
daga can me kiran nata ta ce"ato oya les go dai ku ki fara da dukan soja".
banza tayi mata ko ɗaura ɗan ƙwalin bata yi ba ta fito da achogen takalminta tana tafiya cikin nutsuwa.
kowa ya shiga mota aka tafi filin jirgi don tahowa da babban baƙo wato Canal Aliyu .A. Aliyu wanda aka fi sani da Triple A haka sunansa yake tun a primary har izuwa yanzu da yake a matakin Canal.
Sosai ƴammatan ke ɗokin ganin Canal,kowaccensu taci adonta na kece raini duk da ankon kala ɗaya ne amman kowacce da stile ɗin ɗinkinta mai ban sha'awa,don kowacce ba laifi tayi ba ƙarya gaskiya sai dai hasadun iza hasadan.
kowacce kuma sai bin ƴar uwarta take da harara har da ɗan tsuke fuska,alamun fa cewa kowaccensu ƴar jaraba ce jiran ƙiris take yi😂.
Ko a filin jirgin ma sai da aka ɗan raba hali,don kowaccensu tsayawa tayi jikin mota wai ita zai fara gani daya fito,Autar Momma sai kallansu take tana dariya,don tun ba yau ba tasan wanene Bro Aliyu mutum ne mai shegiyar kafiya da kuma ɗauke kai aduk abinda kasa wai don ka burgeshi sai ma gwaleka da zaiyi,don ba ma sai ya kalli fuskar taka bane zai san ka sanya wani abu? idan kuwa kaga yana hira har da ɗan murmushi,to fa kada ka tambaya ma ko dai da Momma ne ko kuma da yayansa ko kuma Abbah,wato mahaifinsu tuno da wannan yasa Autar mama ƙunshe dariyarta don tasan nan ba da daɗewa ba zasu ƙwashi kashinsu a hannu,don shi ko kallo ma bai so ballantana ma aje ga maganar so.
ƴammata fa anyi cas anyi acan acan,ana ta gyara glass da kuma tsayuwar zaman riga das a jikimsu,Momiga wato ƴar ƙanin mahaifin Canal ta kalli Autar Momma sannan ta ce"wai ke Salma me yasa kika raina mutane ne? saboda kinga munzo tarar ɗan uwanki shine kike mana wannan cin fuskar?to wallahi kiji da kanki,don ni wallahi ba raga miko zanyi ba kamarsu Fatima kina yimin zan disga ki".
Autar Momma tayi mata wani kallo,wanda ya sanya ƴaƴan hanjin cikin momiga juyawa,yarinyar aƙwaita da ƙwarjini da kuma tsare gida,kuma sam bata san raini saboda haka ma bata fiya shiga cikin muta ne ba.
bata ce mata ƙala ba amman wannan hararar ita ta wakilci maganar,tayi juyawarta ta sanya idonta sosai a filin jirgin don Allah ya sani tayi kewar ganin Bro ɗinta,shekara 12, fa ba wasa bane don tun tana ƴar shekara goma ya tafi gashi yanzu tana da shekara 22,shi kuma ayanzu yana da 29 years.

kallo ya koma kansa,don yadda ya fara sakkowa cikin kayan sojojinsa masu matuƙar kyau,sun zauna masa sosai tamkar don shi dama akayi kayan.

wai! wai!! wai!!

wannan guy ɗin yayi wa maza zarra,dogo ne samɓel farin bafulatani me ji da yarintarsa yadda kasan jini zai fito haka yake ballantana kuma daba a nan yake ba a ƙasar waje,sosai skin ɗinsa ya samu hutu har wani ɗaukar ido yake tamkar wata mace,ƴammata fa sai da suka kusa durƙushewa awajen saboda kyaun da yayi musu,gashi jikinsa a murtuke alamu dake nuna cewa ya samu hutu sosai.
nan fa aka fara rige rigen zuwan tarbarsa,sai dai kunya ce ta hana ƴammatan ƙarasawa saboda iyayensu maxa da suke wajen,cikin ladabi ya gaishesu suna yi mai sannu da zuwa.ya amsa yana murmushi yana leƙe ko zai ga Mommansa ko Papa ɗinsa,sai dai duk bai gansu ba tsabar miskilancinsa bai sa ya tambaya bama,baza kuma kayi tunanin ya damu ba ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya wuce abinsa.
masu busa fa suka fara suna yi mai kirari,Galadima É—an sarki ya sauka Allah ya bar mana kai sarki mai jiran gado.

cikin takunsa mai matuƙar tsayawa arai yazo ya wuce ta gaban ƴammatan nan,tamkar su janyosa haka suke ji amman babu damar ko magana suyi masa,saboda haka suka ɗinke bakunansu suna mai take masa baya.

Ƙamshin turarensa ma kawai abin burgewa ne,yadda kasan turaren dayafi kowani turare ƙamshi,dukkansu suka buɗe hancinsu suna shaƙar wannan daddaɗan ƙamshin mai mantar da mutum daga damuwa.

kana shiga gidan BABBAR MASARAUTA,zaka samu kowanni babban ƙusa da kuma bayi da dogarai ta ko'ina,saman benen gidan na hango Sarki gagara badau yasha ƙwalliya cikin kayansa masu matuƙar tafiya da mutum,ado ta ko'ina sai walƙiya yake yana ɗaukar ido kuma ko ba a faɗa maka ba kasan cewa shine mahaifin Canal Aliyu Galadima.

Fara'ar dattijon ta ƙaru,kasan cewar Aliyu shine ɗansa namiji tilo daya malakka,yana masifar sonsa so mai matuƙar tsayawa azuciya,kowa kuma ya tabbatar da hakan Aliyu ɗan lele ne tako in,sai dai zuciyoyin wasu agidan Sarautan suna mai cike da shan alwashi da kuma ɗaukar fansa akan Aliyun,tun wasu shekaru da suka shuɗe wanda aka so halaka Aliyun Allah ya kare shi.
duk miskilancin Aliyu da sauri sauri ya ƙarasa wajen mahaifin na sa,ya yinda ya buɗe masa hannunsa ya ƙarasa da sauri ya rungume mahaifinsa,yana ɗan zubar da ƙwalla shi kaɗai yasan yadda yayi kewar mahaifansa musamman ma mahaifinsa wanda yake masifar so,don ya taso ne da ɗinbin soyayyar mahaifinsa aransa.
sosai mutane suka tsaya suna kallonsu,gwanin ban sha'awa wasu suna murna waÉ—ansu kuma zuciyoyinsu kamar zasu fashe saboda tashin hankali,don dawowar wannan yaron masarauta dai dai yake da rugujewar rayuwarsu,don sun daÉ—e suna shuka tsiyarsu ba tare da anyi musu wani shinge ba,amman sun tabbatar zuwan wannan yaron komai ma sai ya canja.

Magajin gida ya kalli waziri ya ce"lallai aƙwai babban yaƙi a wannan masarautar,don wannan yaron me ido a tsakarka ba barinmu zaiyi ba,yanzu ma haka na tabbatar ba tsakani da Allah ya dawo ba,amman ko yana so ko baya so bai isa ya mulki ƙasar nan ba".

*** *** ***

RABIATU

..................wasu zafafan hawaye na share,na kalli agogo ƙarshe 1:30 dai dai takaici da baƙin ciki suka hanani ko da rintsawa,shekararmu ɗaya da Ahmad da aure amman zan iya ce muku rabona dashi kusan wata biyar kenan,ni ɗin dai ni ce matarsa ta halal amman nayi imani da cewar aƙwai wacce Ahmad yake raba mana ƙwana da ita,sam Ahmad ya juya min baya ƙwata ƙwata baya ganin mutuncina ko kaɗan,nayi tunani akan abinda nayi masa yasa yake wulaƙantani amman na kasa tuno da wani lefi dai dai da ƙwayar zarra,abu ɗaya na sani shima idan shi ɗinne kenan wato matsalar FACALA, wacce nake wa iƙirari da ce war tafi kishiya,don kuwa ni tawa facalar ta banbanta da kowacce irin facala,kai hatta da uwar mijina sai da ta shiga tsakaninmu,mace mai mutunci da mutunta mutane amman sai da ta shiga tsakaninmu dako gaisheta nayi,bata amsawa ko kallon inda nake ma bata yi.
Chapter 1 · 0% Book details