← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 39

Sashe 6

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***********
Hankalin su Dawud a tashe yake musamman shi Dawud dayakan tsinci abinda suke fad'a acikin wak'ar dasuke rerawa da harshen su me kamada yarbanci, dukda yake ya kula akwai banbanci sosai acikin yaren nasu, ko shakka baya yi wannan wani ikone na Allah amma yarbancinne dai, tunda har ya iya yin magana da ita,gashi kuma yakan gane abinda suke nufi, se turasu sukeyi sekace sun kamo bayi

"Abu sufyan wlhy zancen Sacrifice sukeyi fa, kanajin abinda suke cewa a wannan wak'ar dasuke inajin wani abun kaman yarbanci suke, mun shiga uku munzo garin matsafa" cikin tashin hankali Abu Huraira yace

"Dena gayamun mun shiga Uku Dawud, inshaa Allah bamu shiga komai ba se Alheri, sunada k'arfin tsafi munada k'arfin ikon Allah, kaci gaba da addu'a da karatun alqur'ani inshaa Allah zamu kub'uta" shikamma Abu sufyan ya dena gane komai, gaba ki d'aya ya gagara furta wata kalma banda gumi babu abinda yake had'awa haka aka tankad'a k'eyar su har zuwa wani babban fili me zubin yashi kawai ba itatuwa, a tsakiyar yashin aka ajiyesu aka d'auresu kowa baya fuskantar d'anuwansa dan a had'e aka d'auresu sedai bayansu dake gugar juna,a nan aka barsu har rana ta fito ta fad'i bako ruwa gashi an k'wace musu jankunkuna an ajiye angefensu har wannan lokacin kuwa wayar Dawud tana rero karatun alk'urani seda k'yar ya janyota a aljihunsa ya kashe sabida gudun k'arewar caji.

*********
Yamma lik'is mutanen garin suka firfito aka zo aka ajiye kujera koda a k'auyen dake dokar jeji ne kana gani zaka hango cewan harkan saraki ne, haka aka jere kujeru sassak'ar katako sunkai k'waya bakwai mutanen gari suka zo sukazo suka jeru bame wata sutura se kayan fata da kuma wasu ganye sun rufe iya farjinsu maza da mata, matayen kuwa zuwa k'irjinsu ma arufe yake da kayan fata, zuwa akayi aka zagayesu da wani abu kaman cage amma na kara, kaman k'ananun ramukan dake gun dama jira suke dankuwa acikinsu kurun ake kafe abun ana zagayewa har aka kammala

Wani wanda ko ba'a gaya musu ba sunsan sarkine da ahalainsa suka iso gun an d'akkosu acikin wani cage na itace shima k'arti sun d'akko ko wanne susu hud'u d'auke dashi Kowa sujuda yae harseda sarkin da ahalinsa suka zauna sannan suka mik'e tsaye dukansu, gasunan da tsofaffi da kowa, wani ne yafito da jawabinsa na cewan Er sarki Lawuri itace ta kamo mutanen da zasu ceci babanta da danginta batare data tsallaka ruwan ba anan aka d'auki tafi da sowa saurayinta sr murmushi yake yayinda ko kallonsa batayi ba sabida taji haushin yanda bezo ba, Cikin takunta na k'asaita ta k'arasa cikon hilin tare da rakiyar muqarabanta mata masu kula kula da ita. Kunce mata su akai duk aka mik'ar dasu tsaye, lokaci d'aya Abu Sufyan ya nemi zubewa k'asa sabida azabar kishirwa da kuma wuni a dunk'ule gu d'aya, da sauri Abu huraira ya rik'oshi

"Sannu Sufyan, menene?" Ya furta cikeda tashin hakali

"Ruwa nakeso Huraira, kuma k'afana baya iya d'aukana" jakarsu ya janyo da sauri ya zaro roban ruwa, wurin kowa yayi tsit ana kallon su har Lawuri ma, bud'ewa yae ya jonama mai robar a abaki, sosai yakeshan ruwan jiyake kaman ze iya had'iye kogi ma akan tsabar kishin dayakeji, hannu Lawuri ta saka ta karb'e roban ruwa ta tuttular da sauran a k'asa sannan ta wankawa Abu Huraira mari ta turw sufyan a k'asa

" kai waye dazaka mana k'aud'i, ka isa kaciyar dashine?" Dafe kuncin sa yae cikin mamaki ya bita da ido beyi aune ba yaji dirar k'asa a idan sa

"Ni wannan abun ze kalla ido cikin ido? Kai d'an iskan inane dazaka kalleni ido cikin ido? Tabbas inaga kaine zamu yankawa Raminus a wannan shekarar" murza idanshi ya hauyi ga k'asar ya shiga masa sosai haka ya dinga murzawa ya rasa inama ze sanya rayuwar sa, Abu sufyan ne ya rik'oshi ya soma hure masa idan sa, haka yae ta masa kowa yae tsit daga k'arshe ya janyo roba daga jakars ya bashi ya wanke masa fuakarsa da idansa seda yaga ya samu nutsuwa sannan ya rik'e hannunshi yaja yayan shi bayan shi ya had'e hannayensa gu d'aya alamar rok'o kan cewar suyi hak'uri, wata mahaukaciyar dariya ta kwashe da ita sannan ta sanya hannu ta d'auki robar ruwan daya ajiye takai bakinta ta k'wankwada, wani iri taji daban kaman an sanyawa ruwan rake lumshe idanta tae ta shanye duka sannan ta kalli Dawud, tace dashi cikin yaren data fahimci yana ganewa

"Ruwan meye wannan?" D'agowa yae ya kalleta amma be bari sun had'a idoba yace

"Ruwan shane" atak'aice. Murmushi tae masa

"Amma ba irin namu bane, ina ku kuka samo?" shid'inma kafirar k'ishi yakeji seda ya hadi'yi bushashen yawunsa sannan yace

"Dashi mukazo daga garinmu, ku taimaka kubarmu mu koma gida, badasan ranmu mukazo nan ba, hanya ce ta b'ace mana" Hannun ta takai taja gashin gemunsa seda yae k'ara sannan tace

"Wannan zan saka a soma askewa, kaf garin nan babu wanda yakeda daman ajiye wannan se Sarki k'uru naka yayi yawa" Bece komai ba se jakar shima daya janyo ya zari robar rowan da itace ta k'arshe ya kwankwad'a sosai yakusa shanyewa ma kanya ajiye, warcewa tae ta k'ara shanyewa kamar wata mahaukaciyar zakanya. Matsawa tae kusada Abu Huraira ya k'ura mata ido, Dawud dayaga kowa baya iya kallonta sosai ya fahimci ba'a kallonta seya sanya hannu ya rufe masa ido, hannun nasa Abu Huraira ya bige ya sake sanya idanshi a nata, matsawa sosai tae kusa dashi tace da macen dake gefenta

"Wannan nakeso abayar wannan shekarar, banason yanda yake kallona, na tsaneshi sosai, da inada hali bazasu sako musu zakiba, shi zan tura" murmushi tae mata

"Lawuri aike ta dabance, koma wani zakin ya zab'a semu mayar wannan" Murmushi tae daya mugun k'arawa fuskar ta kyau ta tab'e baki had'e da d'age kirarta d'aya

"Muje" tafad'a bayan ta juya tana takun k'asaita babu ko takalmi a k'afarta kafatanin garin ma bame takalmi harshi kanshi sarkin, harsun juya ta kuma waigowa ta kalli jakar su dake wurin tacewa d'aya

"D'akkomun abinda ke jakar cen nacikin irin wancen seki bar musu abunsu agun" dubawa tae bame fari seme baqi haka ta d'akko coke d'in d'aya tabar jakar anan, bayan sun gama maganganun dasuke suka ruf'e qofar cake d'in bayan da suka sako musu wani qaton zaki wanda ya sanya Abu sufyan sakin fitsari a wando ya koma bayan tawayen shi, se ihu mutanen garin keyi ganin yanda suka rud'e anata zabgawa zakin kirari, lokaci d'aya ya soma rura yana zagayen su, yayinda su kuma suka had'e gu d'aya suna adu'a had'e da kukan zuci haukace suke dukkansu.

Wurin Abu huraira yae gadan gadan, shi kuwa yae maza yana k'araso jikinshi ya kwanta k'asa ya dakarwa zakin ciki ya hankad'ashi bayan shi seda ya mulmula, tasowa zakin yae ya karkad'e jikinsa ya k'arayi kansa, nan ya soma adu'a dakiran sunan Allah ya k'ara kaimasa naushi ajikin wuya inda ya kuma zubewa, koda zakin ya d'ago sega idanshi yakoma ja kaman jini jikinsa ya koma kalar baki qirin, atake suka fahimci zakin na tsafine

"Ku d'auki ayar Allah Dawood wlhy ba zakin asali bane ba" haka suka had'a baki suna rero ayatul kursiyu da duk wata adu'a da karatun alk'ur ani me girma dayazo bakin su, hakan ce ta sanya zakin ya gagara dogon motsi ya zube agun yana zabga rura, daganan ya soma shure shure, itaciya d'aya Abu huraira ya zaro daga cikin wanda aka kafe akai cage dashi yace

"Allahu Akhbar!!" Ya dab'a mai aciki take agun zakin ya mace beko shura ba, mik'ewa tsaye sarki yae ya kallu k'uruwa yace

"Bala'i ya samemu ance me tarwatsa garin nan shine me kashe zaki, wannan akashesa da ruwan jikin zakin shine kad'ai maganin sa" Itad'inma rikicewa tae tace

"Hakane, daya tarwatsa garinmu gwara mu kashe sa, tunda susu ukune akashe makashin Lamme" haka suka d'auki kuka gaba d'aya garin ana wak'a aka kwashesu suda gawar zagin akai cikin gari dasu, a hanya sukejin labarin za'a jiqa Lamme (zakin suke kira haka), seya kwana ajik'e se'a baiwa wanda ya kashe zakin ruwan yasha shima ya mutu idan ba haka ba, garin ze kama da wuta danme tarwatsa gari ya karkashe su ne yazo idan be mutuba su zasu mutu...... Dawuda dakejin wannan yaren ya sanar dasu me ake cewa suka hau adu'a, yanzun ma a cage d'aya aka ajiyesu akaje domin aje a jik'a gawar lamme akashe Abu huraira.

*Littafina na kud'ine idan kinsan baki biyaba karki karanta dan Allah, idan har kinaso ki siya akan farashin 200 kacal ki nemi wannan lambar 07084161619*

*********
Da sassafe sauya agogon hannunsu sukai da sufyan da zobe harma da rigarsu dayake dama ba kala d'aya bace ba, suka shirya idan an kawo yayi bismillah so 21 shi yasha sun kula tsafine kawai Allah ne kawai ze kub'utar dasu.........

Lawuri duk yanda taso tayi bacci abun ya gagareta, abinda taji suna karantawa da k'arfi shine yake mata amsa kuwa acikin kunnuwanta, ko shakka babu so takeyi ta k'ara sauraren wannan abun, bazata iya bacci basam so take ta rik'aji sunayi koda mutum d'aya ne yana mata, mesa takeson ta saurari wannan abun? Mesa ma takeson yanda wannan yake kallonta? So take taje ita yama k'ura mata idanshi, kodan sabida ba'a saba kallonta bane ba takejin hakan? Tana tsananin son taga idanshi a nata, Kalmar sa ta karshe itace tafi kowacce yi mata yawo sabida yawon datake mata harta haddace "Allahu Akhbar!!", matsafane ko shakka batayi wannan ruwan datasha sun mata wani stafin ne aciki amma bari tabi daren nan taje gunsu ya mata wannan karatun dayake koma su duka su mata.
Chapter 6 · 0% Book details