← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 39

Sashe 2

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kad'an bazaka ce ya tab'ayin dariya bama idan ka kalli fuskar sa yayi wani kici kicin da fuskar nan sekace wanda aka aikowa da manzon ranar mutuwar sa, cikin tsare gida mahaifin sa ke kallon sa

"Yaya zakace bazaka ba? Ni kakeso naje kokuma so kakeyi ka mayar dani sa'anka sarai ka sani bana sauya hukuncina, baiwar Allah nan tayi shekaru masu yawa bataje gidansu ba, sabida haka kai da kuma Abu huraira kune zakuje ku kaita idan yaso ku dawo city ku jirata daga nan baya ta kammala adadin kwanakin data gaya muku zatayi seku koma ku d'akko ta tunda yake tafiyar akwai nisa daga nan DOGUWAR HANYA ce zakubi" Be isa ya k'arayin gaddama dan haka cikin girmamawa yace

"Kayi Hak'uri dad, dama ban fahimci manufar kaba ne se yanzu, yaushe zamu tafi to?" Kallon sa uban yae

"Kuje ranar Juma'a da safe" iyakar abinda General ya fad'a kenan ya mik'e cikin isa dajin mulki ya haura saman sa ransa ad'an b'ace, besan meyake sa Abu Sufyan yake da kafiya ba akan al'amura wataqil kuma halin sane daya gada yakeso ya masa fintinkau akan halin.

Abu sufyan yana mik'ewa hanyar waje ya nufa, sojoji se k'ame masa sukeyi kkallon su beyi ba yau ran maza ya b'aci, kurun shi dad baze saurari uzurin mutum ba seya wani kafe akan seyayi abu, yana da hidimomin gabansa yazece seyaje har wannan garin abin haushin ma acikin k'auye irin wannan tafiyar wahala ce zasuyi yasani tabbas dan kuwa akwai direbobi masu tulin yawa agidan, sesuje da ita mana amma dan wani neman rigima dad har yace ita zata fad'i adadin kwanakin datakeso su duk uzurinsu ya zamto na banza kenan? Haba dad sam baya adalci wasu lokutan wlhy, figar motar yae ya soma gudun fanfalaqi akan titin na birnin Tarayya ranshi a b'ace.

***********
Amma General kana ganin hakan ya dace kuwa, yaran nan dukan su sunada uzuri ni samma se nakeji ajikina tafiyar ba alkhairi bace ba sam" Harara ya wurga mata

"Se uzurin su yafi aiken dana musu? Sesuke had'e kai sunawa mutane shashan ci da girmansu da komai shekarunsu nawa yanzu? Haba Haj Adama, mesa newai ke har yanzu kike biyewa shirmen yaran nan da yawo suke so suje inane bazasu jeba dan Allah? Wlhy bazan janye maganar tafiyar nan tasu ba jibi jibi, dole ne sukai mun uwata har garin su su kuma jirata tayi adadin kwanakin datakeso tayi sannan su dawo da ita, mutunci d'aya zan musu shine su koma cikin gari su kama hotel su kwana kafin ta kammala sesu koma k'auyen su d'akkota su dawo" Nisawa tae

"Shikenan tunda haka kace, ina musu fatan Alheri Allah ya kaisu lapiya ya kuma dawo dasu lapia"

"Ameen" itace kurun kalmar da general ya furta ya mik'e yabar d'akin, yana fitowa motoci suka jeru burjik da sojoji se sare masa akeyi shi kuwa dama fara'a bawai damun sa tae ba ya wani sha mur bako alamun rahama a fuskar sa.

************
"Dude kana ina?" Ya tambaya bayan tawayen nasa ya d'aga wayar sa

"Ina Green tea" tsaki yae ya juya akalar motarsa zuwa cen batare dayace masa komai, cikin mintunan dabasu wuce sha biyar ba se gashi a wurin, k'arisawa yae ya baiwa Abu huraira hannu shida wani abokin shi suka gaisa yace

"Kai Musty shine zaka gudo ka barni da Dad kaga wani had'a rai da yae yanata mun masifa sekace wani abu" Murmushi yae dayake shi dama be cika shariya irin na Abu Sufyan ba shi bama shida yawan surutu

"Bansan mezan ce masa bane ba, kuma kaima nace karkace masa haka ka hak'ura da bikin kawai tunda ba dole, amma ka kafe aika jaraba, halin dad ka manta kaima kasani wlhy baze tab'a bari mu tsaya biki mubar aikensaba kona waye" Tsaki Abu sufyan yae

"Amma bro aikasan ana iya d'age lokacin tafiyar nan, dama Allah ya taimakemu zamu samu wannan program na mata wanda za'ayi thursday night kaga Bashir bazeji zafinmu sosai ba" Kishin gid'a yae ajikin kujerar dayake kai cikin takaici

"Allah ya mana jagora, ni gabaki d'aya tafiyar se idan na tunata k'irjina yake bugawa wlhy, Doguwar hanya ce zamu bi fa" murmushi yae

"Nan zuwa garin aiba nisa karka wasu 'yan damu inshaa Allah zamuje lapia mu dawo lapia, kuma zamuji dad'in tafiyar nan" murmushi kurun yae yana tunanin tafiyar, dole yaje Shops nasu yaga tafiyar al'amuran yau tunda yake gobe thursday tafiya kuma friday ne, ranshi a jagule ya mik'e

"Abu Huraira zanje Building materials shop, sekaje tile making company ka had'a abubuwan nan, sauran kuma Cyama taje, tunda yake tana gari" jinjina masa kai Abu huraira yae yayinda ya mik'e ya musu sallama shida Friend d'inshi Dawud ya wuce.

***********

Hanifa kam tayi kici kicin da fuskarnan se rigima take masa akan tafiyar nan

"Amma yaa abu huraira da gasken wai tafiya zakayi, tayaya kakeso naci bikin nan baka nan" murmushi ya sake mata

"Hanny kiyi hak'uri banida wani zab'in daya wuce nabi umarnin dad,indai baso kike ya fasamun kai da gun ba toki dena wannan rigimar" Turo baki tae

"To naji amma karku wuce 2days plss" murmushi ya sakar mata

"Inshaa Allah my hanny karki damu kinji" Langwab'ar da kanta tae

"Ban maka alqawarin cewan baran damu ba, amma zan kwatanta" Murmushin dake fuskarsa ya fad'ad'a

"To my hanny barinzo in wuce yanxu dai, kinga gobe da sassafe zamu cira kuma ga gajiyan biki yau, Abu sufyan yanata kirana a waya ma" Fuskar ta sam ba dad'i tace

"Ina maka fatan Alheri Yaa Huraira kace ina gayar da yaa sufyan, zan muku waya so 20 akowace rana amma zancen motar fa?" Murmushi yae

"Tana waje ai, habu ya kawo tuni, yanzu zanje na daukeshi kese ki shigo da ita, and plss karki mun wasa da motana, kar kuma na dawo na tarar tayi datti ko wani scratch ajikinta" murmushi yanzu kam tae

"Yaa Abu kacika rigima indai akan motane, inshaa Allah ma biki kurun zanje dashi sena dawo na ajiye" murmushi yae

"Nizan wuce muje gate seki karb'a ko?" Haka ta tako shiyaja motarsa har xuwa gate suka rabu zuciyoyin su ba dad'i, itadai haka nan hankalinta be kwanta da tafiyar nan ba ajikinta setage ka tamkar akwai wani abu daze faru da yayyunta abinda bazata iya d'auka ba kenan har abada, jikinta amace ta k'arisa cikin gidan, kallonta Baba saude tae

"Hanifer na yada fuska haka ne? Naga duk kinyi wata kalar tausayi" kwanciya tae ta kwantar da kanta asaman cinyar Baba

"Baba hakanan hankalina ne kwanta da tafiyar su yaa Abu ba, ni tunda nake banji tafiyan dabe kwantamun ba kaman wannan" murmushi irin na manya Baba saude tae, dukkuwa da yake cewan itama tafiyan ba wani yi mata yae ba sam, jitakeyi tamkar tawa General magana akan a fasa tafiyar da yaran a bata kud'in mota aitasan hanya inyaso seta tafi abunta, batayi tsufan daza'ace bazata iya tafiya da kanta ba amma Tarasa meke damu General yacika kafiyan tsiya yanzu koda cewa tae zata mai magana ma baji zeyiba ranta ne kurun ze b'aci

"Hanifer a sanya alkhairi acikin zuciya, a k'ullawa zuciya salama, adu'a itace abun buk'atar su yanzu, Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya kurun zakice kinji" murmushi tae

"To Baba, ni ki sosamun kaina yana mun k'aik'ayi" sosa mata kan tahauyi batayi magana ba, tana tunanin yanda yafiyar nan ta yara zasu kasance, kosu sunce basason tafiyar, mahaifiyarsu ma haka mesa General ze kafe ne? Tana musu fatan alheri aduk inda suke"

**********
Dukkaninsu suna durk'ushe agaban mahaifiyar su sunyi shiru suna sauraraenta amma shiru batace dasu komai ba, yanayin shigarsu ya karb'esu sosai shadda ce brown me duhu da hula brown amma light sunsha d'inkin zamani d'an cakwai yayi cas ajikinsu, komai nasu iri d'aya ne banda abu d'aya shine agogon hannunsu wannan nashi fatar kalar baqi ce wuluk yayin da d'ayan ke sanye da kalar fari k'al, wanda wannan shine kad'ai abinda zesanya ka banbanta su sabida tsananin kamanin dasukeyi, ko iyayensu idan ba ta wurin idanunsu ba basa banbance su se abu d'aya na halayya koda yake dukkaninsu basuda yawan magana bare kace ka gane su sedai kurun d'ayan yanada hak'uri sosai yayinda d'ayan sam bashida hak'uri komai k'ank'antar laifi abin masifa ne a gunshi, amma yafi wancen sauk'in kai sabida baya rik'ewa mintuna k'alilan sun wadace shi ya manta da abu komai b'acin ran daya sakashi

"Kyautar Allah inaso aduk inda kuke kuji tsoron Allah, ku sani dukkkanin abinda kuke aikatawa Allah yana ji yana kuma ganinku, bakuda abinda shaku shamakance Lillahi daga ganin ku a komai dakukeyi, karkuga kaman kunyi nisa da gidan kuce zaku aikata abinda bashi bane halayyar ku ta asali, karkuyi abu koku bari danni kuyi dan Allah ku kuma bari dominshi, shikad'ai yasan ladan daze baku, kuna k'ok'ari sosai kuma ina matuk'ar jin dad'i ina kuma yabawa sosai akan hakan, sedai ku k'ara, kuma ku rik'e adu'a ku yawaita yin adu'a, musamman idan zaku fita da kuma duk wani abun k'i daya tinkaro ku kubishi da ambaton Lillahi inshaa Allahu zakuga haske komai yawan duhun daya taso muku, kuci gaba dason juna tafiya ce ta sati d'aya nake ga, dukda koni a raina banson tafiyar amma babu yanda zamuyi, awurin Allah sati ai kaman yau ne zakuga kun dawo, fatan kuje ku kuma dawo lafiya" A tare suka had'a bakinsu wurin cewa

"Mungode sosai Mom, Allah ya saka da alkhairi, kuma inshaa Allahu zamu kiyaye" Dafa kan Abu hurairah tayi ta masa adu'a sannan ta sake ta dafa kan Abu sufyan ta masa sannan sukai mata sallama suka fita" A waje suka tadda general ya murtuke fuskar nan tamkar be tab'a dariya ba, k'arisawa Abu sufyan yae kusa dashi yace

"Dad yanzu zamu tafi" kallonshi yae kanya kai kallonshi zuwaga zoben hannunshi sabida yanaso ya gano ko waye, shi kanshi idan bada zoben nan ba to baya tab'a banbantasu, shisa tun suna yara suna k'ara girma yana sanyawa ana musu zobuna masu sunayensu d'aya me d'igon bak'i d'aya kuma me d'igon fari, agogon hannunsu kuwa sune dan kansu suke sakawa sabida abokanan su da sauran mutane

"Abu sufyan?, kun fito kenan ina Baba ladin?" Sadda kanshi yae a k'asa

"Tanawa mom sallama ne, yanzunnan zata fito" Jinjina kanshi yae
Chapter 2 · 0% Book details