← Book details Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 39

Sashe 39

Doguwar Hanya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nak'udace ta tasowa zuhrah haik'an, babuji ba gani, a wannan lokacin kuwa Abu hurairah baya gidan kuma 'yar neman fitinar hanifer tana gun aiki, kiran duniya kam tayiwa Abu hurairah be d'aga wayar ba sabida baya kusa, haka ta juya akalar kiran wayarta zuwa gidansu inda tayi nasara mahaifiyarta tazo har gidan nata suka kwasheta zuwa asibiti, taci bak'ar wuya har sanda huraira yazo asibitin shida ahalinsa kanta samu ta haifi yaranta biyu duka maza kyawawan gaske masu tsananin kamanni da mahaifinsu tun suna yara kamanin suka bayyana, murna awurin Abu burairah ba'a magana baki har kunne, ba'a sallameta ba sabida wuyan datasha yasanya ma jininta yak'i ya sauka....... Tana kwance ita kad'ai a d'akin Abu hurairah ya shigo zama yae akujerar dake kusa da gadonta ya fuskanceta sosai yace

"Ina fatan miki samun lafiya me d'orewa zuhrah, sannu da fama Allah ya baki lafiyarki, nazone dama akan maganar mu ta kwanan baya, kin buk'aci rabuwa dani duk ranar da kika sauka lafiya, inaji mom taje da yara wurin wanka gida, so kema kuma munyi alk'awari dake akan duk ranar dakika sauka lafiya zan baki takardarki, toni nasan muhimmancin alk'awari, sabida haka ga wannan takardar seki nunawa iyayenki ki kuma gaya musu yanda mukayi tun farko.....nizan kula da yarana, wannan kuma kud'ine ki kula da lafiyarki zuwa sanda zaki fita ajego, nagode sosai da dauriyar ki har zuwa wannan lokacin, ina fatan zaki dakatar da faruk har zuwa lokacin daya dace kuma dukkanin wayar dakike dashi agidana na yafe miki seki neki Allah gafara sabida kinci zarafin aure" koda ya kammala maganganunshi bata fahimtar komai, cikeda firgici ta firta

"Kamun rai Abu hurairah karka rabani da yarana ina k'aunar na rayu dasu kaji" mik'ewa had'e da sanyawa fuskarsa murmushi yace

"Aikuma tun ran gini tunran zane zuhrah, yara ina tuni kikace zaki ijiyemun nine ubansu? Kinga bako semunja da tsayi ba, takardar nan ta gama raba mana gaddama akan wannan zancen, kiyi k'ok'arin sanar da iyayenki hukuncin dakika d'auka, yara kuma na d'auki abuna me reno zan d'auka" yana kaiwa nan ya juya, se faman k'walla masa kira take amma ko waiwaye beko waiwayo ba.

*Ina neman afuwarku, banida lafiya amma inshaa Allah zan daure zuwa sanda zamu kammala, zanyi a gurguje sabida yanayin lfiyata nagode da adu'arku*

Mom Nu'aiym.
[11/27, 9:48 PM] Maamah twins💕❤: 38****** kuka takeyi tamkar ranta ze fita, bazata iya fassara yanayin datake jiba a wannan lokacin, babu abinda takeso fiyeda ace yau gata ga yaranta, tasani tanaso tawa Faruk halacci amma ta dena waya dashi kwata kwata, ya kamata Abu hurairah yasan wannan ya barta da yaranta koda baze rayu da ita ba, kai ina bama ze yiyu ta koma gidansu ba mahaifinta ze hallakar da ita, wayarta ta zaro ta kira abu hurairah har ya k'araci ringing d'insa be d'aga wayar ba, ganin ta kirashi yakai so 10 be d'auka ba ya sanya ta juya akalar kiran wayar nata zuwa ga Ayusher, ringin biyu ta d'auka take sanar mata tana son ganin ta.
Babu abinda ta b'ye mata daya faru, take agun ta bata shawarwari masu kyau tare da nuna mata illar ha'intar aure be dace ba sam daganan suka yanke shawara akan ana sallamar ta su wuce gidan mom.

*********
*Agurguje plss*

Hakan dasuka yanke haka akayi, atake suka wuce gidan mom ana basu sallama inda murna suka tarar mom nayi hadda gud'a, soyayya me tsanani ke shigarta ta yaran duk yayin data kallesu seta tuna ranar haihuwar mahaifansu, bata tare da kowa se Baba Ladi, agida ta haihu amma taci bak'ar uk'uba sosai. Hurairah ma yayi mamakin ganinta gidan amma be isa yace komai ba haka ya zuba har ranar suna tana gidan amma babu mewa wani magana, su d'inma sunan da aka mayar musu kenan Hasan da usaini, aka laqabamusu Affan da haifan, an kashe dukiya kam ba laifi.

Har wannan lokacin Zuhrah bata bud'e takardan sakinta ba, washe garin suna tana zaune a d'akin da aka bata sega Abu hurairah ya shigo fuskar nn babu yabo babu fallasa ya kalleta sosai yace

"Ina kyautata zaton dakin bud'e takardar dana baki dabakiyi rashin hanklin zuwa gidan mu ba" batace masa komai ba sedai kam k'irjinta yayi mugun dokawa, kallon sa tae cikeda tsoro tunawan datae da takardar amma ta kasa furta wata kalma k'wak'wara

"Ki tabbatar yau kinduba takardar" ya fad'a sannan ya juya abunshi, kuka wiwi ta saka, kan daga bisani ta mik'e tsaye cikin rashin kuzari ta janyo handbag d'inta takardar ta d'akko amma har akafi k'arfin awa ta gagara bud'ewq, sea tayita faman du'a'i kafin ta bud'e takardar cikeda kasala, ga abinda akace

**** "Zuhrahty na sani nine na sab'a miki, nine kuma na janyo kika shiga halin tozarci da wulak'anci, kikaga rayuwa mara d'ad'i iri iri, amma ina nrman alfatmar yafiya, dan Allah ki yafemun, na tuba ina k'aunarki matata, banida kamarki uwar 'ya'ya na, ina me k'ara baki hak'uri akan abinda na miki abaya dakuma wanda nake sharin miki yanzu, kamar yanda mukai alk'awari akan idan kika sauka lafiya zan sauwaqe miki kije gidanku, to hakan bame yiyuwa bane ba, bazan iyaba, ina zan rayu babu farin cikina? Ina zan rayu babu rabin raina, ina zan rayu babu ruhina zuhra? Kece komai na ina k'aunar ki fiyeda tunani, ina miki sonso fisabilillah my zuhrah, kiyi hakuri zan baiwa d'an uwanki hak'uri akan matata inason abata ya janye yaje ya nemi wata kurin. Daga k'arshe ki sani wannan kalmar mara dad'i babu ita tsakanina dake har gaban abada, bazan lamunce taba, bana buka tarta bana sonta kuma har abada, bakuma zata tabbatar har abada, ina jiran amsrki ko nai miki fushi ki taimaki marayan nan dan Allah kinji?"...

Ta k'arashe karanta wasik'ar tana me daka tsalle da ihun murna, wanda yae daidai da shigowar Ayusher inda atake ta rungumeta, bata b'ata lokaci wurin sanar mata abinda wasik'ar ta kuns ba suka dinga murna da yaron cikin Ayusher amma haka take daka tsalle.

*****
*Bayan sati shida*
Aure dai a d'aura tsakanin Lawuri (Naja'atu) dakuma Oga shamsu, ansha budiri se murn suke dukkansu sabida sun fahimci juna sosai, mahaifiyar Lawuri tazo sedai mahaifinta yana jinya be samu zuwa ba, murmna kam bama sena fad'a ba awurin su....

Hanifer ganin ba sarki se Allah ya sanya ta hak'ura ta gbatar da tsohon saurayinta me suna khamis, inda aka shirya musu aure nanda 6month lokaci daya dana cyama da dawood.

Mom ta tuba da halayen sonkai tayita istigfari, ta yarda *Doguwar hanya* Alhkhairi ce arayuwar su, babu abinda yafi ace yau naka yay8 sanadin yad'uwar addinin Allah da guminsa, dan haka take godewa Allah da wahalar dasuka sha bata tashi a banza ba suke k'aunar junansu kuma sukai sanadiyar shiriyar wasu mutane masu d'inbin yawa.

Barbo tanata zuba soyayya da malam inda har ake shirin musu aure inshaa Allah.

*Tammat bi hamdillah. Bamso na tsaya anan ba, ban shirya dakatar da labarina anan ba, amma dalilai da dama sun tilstani aikata hakan, banida lafiya banida k'arfin dazan muku typing kowace rana, Allah shine ya d'auramun da wannan nake fatan zaku fahimceni, zakuma ku gane inda na dosa, a yanda dai na fahimta nake kuma zato, duk wani me hankali ya gan inda alk'alamina ya dosa.

Bazan manta kuna Masoyana dasuka siya littafin nan, Allah ya baibaiyeku da zuri'arku da d'inbin alkhairi ya sanya albarka a rayuwarku ya shiryar daku da yaranku da dukkanin zuri'a.

Bissalam.

Mom Nu'aiym

www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.

We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors

We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.

AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.

Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.
Chapter 39 · 0% Book details